Manara RADIO
Radio channel that sheds light to listeners in Africa,Middle East and across the globe, predominantly "HAUSA" on Islamic tenets and civilization
LABARUN DUNIYA
SHUGABA TINUBU YA GANA DA SHUGABAN RABIDA SHEIKH AL-ISSA
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban majalisar musulunci ta duniya RABIDA Sheikh Abdulkarim Al-Issa a fadar A*o Rock.
Ganawar dai ta zo ne bayan gudanar da taron majalisar ta Rabida da hadin guiwar kungiyar Izala.
Dukkan bangarorin biyu sun yaba juna yadda su ke bukatar a bunkasa fahimtar juna a tsakanin al’ummar kasa.
Baya ga shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, akwai wasu gwamnoni da ministoci da su ka raka tawagar Sheikh Al-Issa zuwa fadar ta A*o.
Najeriya dai mai bin tsarin mulki na kowa ya yi addininsa ba tsangwama, na da mabiya addinai da tsarin rayuwa daban-daban da dama.
Duk wanda zai kawo shawarar yadda za a dinke dukkan barakar zama tare, na zama abun maraba a Najeriya.
MUSULMI DA MABIYA ADDININ KIRISTA SUN SANYA HANNU KAN YARJEJENIYAR SALAMA
Musulmi da mabiya addinin kirista sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman salama tare a lamuran yau da kullum.
Wannan na cikin babban sashen taro na duniya tsakanin RABIDA da kungiyar a Abuja wanda ya samu halartar manyan malamai daga wasu kasashen duniya daga ciki da wajen Afurka har zuwa Turai.
Jagororin musulmi da wakilan kungiyar kiristocin Najeriya CAN sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya ya tabbatar da zaman lafiya.
Ba batun mabiya addinai su zauna a addini daya, amma tsarin na son kusantar juna da fahimtar tanadin addinin juna da girmama hakan.
Jagororin sun kawo hujjoji daga Alkur’ani da kuma Baibul inda hakan ke nuna kusaci tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista.
Shawarwarin da a ka yanke za su zama abubuwan da a ka mikawa gwamnati don karfafasu da hakan zai kawo maslaha kan al’adu da lke kawo zaman doya da manja tsakanin musulmi da kirista.
An wallafa kundin da zai zama abun misali da amfani don kawo karshen duk wata arangama ko kiyayya tsakanin bangarorin biyu.
Traon ya nuna ba alheri ba ne musulmi ya tsangwami kirista ko kirista ya tsangwami musulmi, alhali a na zaune a kasa daya.
ZA A GUDANAR DA ZABEN GWAMNAN OSUN A RANAR ASABAR MAI ZUWA
Hukumar zaben Najeriya INEC za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Osun ranar Asabar din nan mai zuwa.
A na kwana 3 gabanin zaben, hukumar zabn ta shigar da sunan dan takarar jami’iyyar SDP Fransis Olugbenga cikin jerin masu takara da hakan ya maida yawan ‘yan takarar 15.
Hakika alamu na nuna magoya bayan tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola na son yin duk mai yiwuwa wajen kawo karshen gwamnatin Ademola Adelele.
Hakika shi ma wannan zabe na Osun zai zama raba-gardama ga yadda a ke hangen babban zaben 2027 zai gudana.
Samun nasarar gudanar da karbabben zabe a Osun zai nuna yadda musamman ‘yan takarar adawa za su shiga zaben 2027 da kwain guiwa.
Tun kwanaki hukumar zaben INEC ta gudanar da taro da duk masu ruwa da tsaki na zaben.
GWAMNAN JIHAR KEBBI YA RABA MOTOCIN SAFA 7 GA MANYAN MAKARANTUN JIHAR
Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idris Kauran Gwandu ya raba motocin safa 7 ga manyan makarantun jihar.
An yi bukin mika motocin ne a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Gwamnan ya ce ya dau matakin ne don bunkasa yanayin koyarwa a manyan makarantun jihar ta hanyar saukaka bukatun sufuri.
"A matsayina na malami na ga ya dace na tuna bangarena na kuma inganta shi.
Tun farko kwamishinan ma'aikatar ilimi mai zurfi Alhaji Isah Abubakar Tunga ya jinjinawa gwamnan don raba motocin sashen da ya dace.
Yayin da ya ke godewa gwamnan don daukar matakan bunkasa sashen ilimi, kwamishinan ya yi alwashin amfani da motocin ga abun da a ka says su na ilimin manyan makarantun jihar.
A sanarwa daga Sakataren labaru na gwamnan, Ahmed Idris, Kolejjn ilimi na Adamu Augie a Argungu, Kolejin jinya da ungozoma ta Kauran Gwandu a Ambursa, Kolejin kimiyyar lafiya da fasaha ta Jega, Jami’ar kimiyya da fasaha ta Abdullahi Gwandu a Aliero, Kolejin ilimi mai zurfi ta shari’a da ke Yauri, Kolejin ilimin lafiya ta Birnin Kebbi sai makarantar kimiyya ta jihar Kebbi da ke Dakingari
TRUMP YA CE AMURKA KE RIKE DA IKON HORMUZ
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa ke rike da ikon kula da muhimmiyar mashigar ruwan Maliya na Hormuz.
A nan Trump ya ce Amurka za ta rike mashigar kuma Iran ba ta da wani mataki da za ta dauka.
Trump ya kara da cewa sojojin ruwan Amurka ke kula da mashigar Hormuz a halin yanzu.
Iran a na ta bangaren ta ce sam ba haka ba ne, ita ke rike da akasarin mashigar kuma ikon mashigar na hannunta.
Muhawara dai kan ikon mashigar Hormuz ba sabon abu ba ne musamman a bangaren Amueka.
A na fatan samun maslahar da za ta kawo zaman lafiya mai dorewa tsakanin Iran da Amurka kuma hakan ya dogaro a wani fannin da sulhu kan Hormuz.
An dai samu tsagaitawar hare-hare kan Iran da ramuwar gayyar Iran kan cibiyoyin sojan Amurka da ke gabar ta tsakiya.
12/08/2026
Cikin daren jiya Talata, Sheikh Abbas Jega Mataimakin Shugaban Kungiyar Izala Na Kasa Na biyu ya kawo wa Sheikh Abdullahi Bala Lau ziyara, domin kara tattaunawa akan nasararon da Kungiyar mu ta Izala ke karasamu.
Manara radio
27 Safar 1447H
11/08/2026
Muslim World League da JIBWIS Nigeria Sun Buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa kan Tsaron Ƙasa a Abuja
Ƙungiyar Muslim World League, tare da haɗin gwiwar JIBWIS Nigeria, ta buɗe babban Taron Ƙasa da Ƙasa kan Tsaron Ƙasa domin Dorewar Ci gaban Tattalin Arziki da Zamantakewa a Abuja.
Ana gudanar da taron ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Sheikh Dr. Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa, Babban Sakataren Muslim World League, inda manyan shugabanni, malamai, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki s**a hallara domin tattauna ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Daga cikin manyan baki akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnonin Borno, Sokoto, Kaduna da Jigawa, tare da Mataimakan Gwamnonin Yobe da Katsina.
Taron ya kuma samu halartar ministocin, ciki har da Ministan Yaɗa Labarai Alh. Mohammed Idris, Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Daga cikin malamai da manyan baki da s**a halarci taron akwai Hon. Ali Isah Jesy; Sheikh Dalhat Abubakar Hakimi, wanda ya wakilci Sheikh Sanni Yahaya Jingir; Sheikh Karibullah Nasiru Kabara; Dr. Khalid Aliyu, Babban Sakatare na Jama’atu Nasril Islam (JNI); da Dr. Ahmed Mahmoud Gumi, tare da sauran manyan malamai da shugabannin addini.
Haka kuma, sarakunan gargajiya da s**a halarci taron sun haɗa da masu martaba Sarkin Zazzau, Sarkin Bida, Sarkin Hadejia da Sarkin Maradun.
An mayar da hankali kan ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, da hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da tsaron ƙasa a matsayin ginshiƙan ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Manara radio
10/08/2026
Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa Ya Iso Najeriya Domin Babban Taron Ƙasa da Ƙasa Kan Tsaron Ƙasa da Dorewar Ci gaban Al’umma.
Mai Girma Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa, Babban Sakatare na Ƙungiyar Muslim World League, (RABIDA) ya iso Najeriya domin halartar Taron Ƙasa da Ƙasa kan Tsaron Ƙasa domin Dorewar Ci gaban Tattalin Arziki da Zamantakewa (International Conference for National Security for Sustainable Socio-Economic Development), wanda Ƙungiyar Muslim World League (RABIDA) tare da JIBWIS Nigeria s**a shirya.
Za a gudanar da babban taron gobe Talata, 11 ga Agusta 2026, a Abuja, inda za a tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi ƙalubalen tsaron Najeriya, da kuma muhimmancin samar da zaman lafiya da tsaro domin samun ɗorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
An tarbi Mai Girma Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda tawagar Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, Shugaban JIBWIS Nigeria, tare da sauran manyan baki s**a tarbe shi.
Ana sa ran taron zai haɗa manyan malamai, wakilan gwamnati, masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro, masana da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, tare da bunƙasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ɗorewa a Najeriya.
Manara radio
Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar da haɗin gwuiwar kungiyar Haɗa kan Musulmai ta duniya (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY, na gayyatar Al'ummar musulmi zuwa gagarumin taron ƙarawa juna ilimi mai taken 'BAMBANCE BAMBANCE TARE DA ZAMAN LAFIYAR JAMA’A”
Taron wanda 'HAƊIN GUIWA NE TSAKANIN KUNGIYAR HAƊA KAN MUSULULMAI TA DUNIYA, MAI CIBIYA A ƘASAR SAUDIYYA (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY DA ƘUNGIYAR WA'AZIN MUSULUNCI TA KASAR NAJERIYA, JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA IKAMATIS SUNNAH.
-Za a buɗe taron conference ranar talata 11/August/2026 da misalin karfe tara na safe (9:00am) a kuma gama ranar laraba 12/August/2026 da rana 2:30pm.
-Za'a gabatar da Wa'azin kasa a harabar Masallacin JIBWIS dake helkwatar kungiyar a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja, daga yammacin laraba har zuwa daren alhamis.
-Safiyar alhamis 14/August/2026 kuma sai jama'a su koma garuruwansu.
Babban bako na Musamman, Shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Ahmad Bola Tunibu.
Uban Taro: Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad
Sauran manyan Baki sun haɗa da:
Gwamnoni Ministoci, Yan majalisu na tarayya da na jahohi, Iyaye Maluma, Sarakuna, yan kasuwa da sauran yan uwa musulmi dake fadin Naijeriya da sauran ƙasashen ketare.
Ana sa ran halartar manyan bakin Malamai daga manyan ƙasashen duniya insha Allah.
Sanarwa daga Sakataren JIBWIS' na ƙasa Sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe, ta ofishin kwamitin Labaru na babban taron.
LABARUN DUNIYA
SHUGABA TINUBU YA AMINCE DA KARAWA JAMI’AN SOJA ALBASHI MAI TSOKA
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da karawa jami’an soja albashi da kaso mai tsoka inda jami’an soja 250,000 za su amfana.
Wannan dai don karawa jami’an kwarin guiwa su cigaba da gudanar da ayyukan tsaron lafiya da dukiya jama’a musamman wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Karin ya tada yawan kudin albashi ga jami’an soja daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.
Tsarin albashi ya nuna matsayin soja daga na gaba da Kanar zuwa Janar-Janar za su samu Karin kashi 30% yayin da masu matsayin Kanar zuwa kasa za su samu karin kashi 50 %. Akwai kuma na kasa gaba daya da za su samu karin kashi 80%.
Wannan karin dai zai fara aiki daga 1 ga watan gobe na Satumba 2026.
Tuni wannan karin ya jawo farin ciki a tsakanin sojoji da masu sharhi kan lamuran tsaro da sauran ma’aikata.
KOTUN MA’AIKATA TA YANKE HUKUNCIN DAWO DA ‘YAN SANDA 475 BAKIN AIKI BAYAN RITAYAR DOLE
Kotun ma’aikata ta ba da umurnin dawo da jami’an ‘yan sansa 475 bakin aikinsu bayan ritayar dole da a ka yi mu su.
Hukumar kula da ‘yan sanda ta salami mutanen ta hanyar ritayar dole inda su ka nuna ba su yi wani laifi ba don haka kotu ta duba kadunsu ta umurci dawo da su bakin aiki.
Babban sufeton ‘yan sanda Tunji Disu ya ba da umurnin a sake ba wa jami’an da a ka dawo da su horon gogewa kan aiki don ba da gudunmawar da ta dace.
Masu sharhi kan tsaro na nuna illar sallamar jami’an tsaro da ke aiki da makamai don ta kan iya yiwuwa su iya shiga miyagun ayyuka ko tallafawa ‘yan ta’adda da horon sarrafa makamai.
HUKUMAR EFFC TA BAYYANA DALILAN RUFE MA’AJIYAR KUDIN BANKI NA JIHAR OSUN
Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta bayyana dalilan rufe asusun banki na gwamnatin jihar Osun.
Karin bayanin na EFCC ya biyo bayan yadda a ka yi caa da sharhi kan dalilin rufe asusun gwamnatin Osun a na ‘yan kwanaki kalilan gabanin zaben gwamna a jihar ta kudu maso yamma.
Kakakin EFCC Dele Oyewole ya ce hukumar na sane da cewa a na gab da zabe a jihar Osun, amma hakan ba zai hana ta daukar matakin kare dukiyar al’umma ba.
Oyewole ya kara da cewa EFCC ta lura a na ta dibar kudi daga asusun a na tura su zuwa wasu ma’ajiyun kudi na wasu kamfanoni.
Matakin a cewar EFCC don hana jidon dukiyar al’ummar Osun ne kuma tun wajajen watan Maris a ka fara gudanar da bincike har ma a ka binciki babban akantan jihar ta Osun.
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya nuna damuwa cewa EFCC ta kai farmaki kan asusun gwamnatin jihar kuma ba tare da samun hurumin yin hakan daga kotu ba.
IRAN TA YI ALWASHIN MAIDA MARTANI KAN MURADUN AMURKA A GABAR TA TSAKIYA MATUKAR AMURKA TA KAI FARMAKI
Iran ta yi gargadin daukar matakan ramuwa kan muradun Amurka a gabar ta tsakiya matukar Amurka ta kai hare-hare kan sassan makamashi na Iran.
Wannan ya fito a bayanan sirri da a ka samu inda a ka ruwaito ministan wajen Iran Abbas Araqchi na yin gargadin martani kan kasashe kawayen Amurka.
Araqchi ya yi magana ta waya da takwarorinsa na Saudiyya, Turkiyya, Katar da kuma ministan tsaro na Pakistan.
A nan Iran ta bukaci kawayen na Amurka su hana Amurka kai wani hari ta hanyar amfani da kawancen da su ke yi da kasar ta yammacin duniya.
Iran dai har yanzu na jan ragamar mashigar ruwan Hormuz mai muhimmanci ga sufurin danyen man fetur, don hakan ya zama kandagarki ga Amurka da kawayenta wajen yi wa Iran din hawan kawara.
Tun 28 ga watan Febrairu Amurka da Isra’ila su ka faro hare-hare kan Iran har da sanadiyyar kisan gilla ga shugaban addini na kasar Ayatollah Ali Khamnae amma hakan bai kifar da gwamnatin Iran ba.
06/08/2026
Allah yanunamana
SANARWA !!!
Daraktan Agaji na Kasa JIBWIS Nig. Engr. Mustapha Imam Sitti na sanar daku "INTERNATIONAL CONFERENCE" da za a gabatar hadin gwiwa da RABIDA ta Duniya da kuma JIBWIS NIGERIA daga Litinin/Alhamis, 10 - 13/8/2026 a garin ABUJA.
Ga yadda tsarin Taron yake :
1. Za a bude Taron Conference ranar Talata, 11/8/2026 a kuma gama ranar Laraba 12/8/2026 da rana 2:30 pm.
2. Wa'azin Kasa kuma a Eagle Square daga yammacin Laraba har zuwa daren Alhamis.
3. Safiyar Alhamis kuma sai Jama'a su koma garuruwansu.
Ana bukatar dukkan 'Yan Agaji su shigo Abuja tun ranar Litinin 10/8/2026 da wuri.
(Dep. Nat. Pub. Sec.)
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Utako District
Abuja