Smartdata4u
We offer instant recharge of Airtime, Databundle, CableTV (DStv, GOtv & Startimes), Electricity Bill Payment and more
29/07/2026
SALLAR DARE 💚
Umar bn Khattab (RA):
Ya kasance yana tashi cikin dare yana karanta Qur’ani, yana kuka har ya sa sauran jama’a su tashi.
Aliyu bn Abi Talib (RA):
Ya ce: “Sallar dare tana haskaka fuska, tana haskaka kabari, tana kawo rahamar Allah, kuma tana hana laifi.”
Imam Hasan Al-Basri:
“Ba su da wata ni’ima wacce s**a fi jin daɗinta kamar sallar dare.
Wani malami ya ce:
“Idan zuciyar mutum ta daskare har baya iya tashi ya yi salla da dare to wannan alamar kasawar ruhinsa ce.”
Ibn Mas'ud (RA) ya ce:
"Bawa ba ya barin sallar dare sai zunubansa sun rinjaye shi har s**a ɗaure zuciyarsa."
Allah ya Bamu ikhlasi a dukkan Ayyukan Mu Na Alkhairi 💚
08/07/2026
SALLAR DARE 💚
Ya ɗan'uwa, kada ka bari gajiya ko barci su hana ka tashi domin sallar dare. Akwai lokacin da Allah yake saukowa zuwa saman duniya a ƙarshen dare, yana cewa:
"Wane ne yake roƙona in amsa masa? Wane ne yake neman gafarata in gafarta masa?"
Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim
Dan uwana Ka tuna:
Rak'a biyu da ikhlasi sun fi yawan aiki ba tare da niyya ta me kyau ba.
Ka yi addu'a da istigfari, domin lokacin amsar addu'a ne.
Ko da raka'a biyu ne ka fara bayan Ka Kammala sekayi wutri, kada ka daina. Dorewa a kan ɗan aiki ya fi yawan aiki da ake yankewa.
Allahumma a'inna 'ala dhikrika wa shukrika wa husni 'ibadatik.
Allah Ya ba ka ikon tashi sallar dare, Ya karɓi ibadarka, Ya biya maka buƙatunka na alheri a duniya da lahira. Amin.
18/04/2026
CIN ZARAFIN ADDINI DA TAUYE HAKKI NA DOKAR QASA!
Yanzu naga Labarin
Wata Daliba Musulma tazo zata shiga gurin da zasu rubuta jarabawa ta JAMB sai wata jami'ar tsaro na Civil Defence ta hanata shiga, ta koreta saboda hijabin ta
Amma ga wasu Dalibai sun zo tsirara an barsu sun shiga ba tare da wata tsangwama ba😢
Wannan cin zarafi da tauye hakkin addini da wulakanci ya faru ne a makarantar Peter Harvard School dake Kubwa a garin Abuja
Dokar Kasar Nigeria ya bawa kowa damar yin addininsa yadda ya ga dama ba tare da cutarwa, saka hijabi a gurin mace Musulma addini ne ba wai ganin dama ba
Abinda wannan jami'ar tsaro tayi fito na fito da dokar Kasa ne, wanda ya kamata a gudanar da kwakkwaran bincike domin ta fuskanci hukunci, domin zai iya haddasa fitina da tashin h@nkali
Kuma wannan yana kara bayyana mana cewa Musulmin Nigeria an gama cinye mu da yaki, ku yi tunanin in ba Musulma bace tazo zata shiga sai akace dole sai ta saka Hijabi? me kuke tunanin zai faru?
Yawan mu ya zama kamar bai da wani amfani, irin wannan wulakanci da cin fuska ya kamata ace ya jima da zama tsohon yayi🗣
Allah Yasa Mudace 🙌
I'm in the top 0% of Musti manzo fans. I earned 859 points on their weekly engagement list last week.
16/04/2026
DUNIYA TAZO KARSHE KAMAR YADDA MANZON ALLAH ANNABI (SAW) YA FADA😢
YACE! Idan Karshen Duniya yazo Zakaga Alamu Kamar haka:”
1.Masu Kudi Zasu Zama Marasa Godiyar Allah.
2.Ana gasar Gina Manyan Gidaje.
3.Baiwa Zata Zama Sarauniya.
4.Zina Zata Zama Abin Kwalliya Ga Al'ummah.
5.Za'a Yawaita Zubar Da Jinin Salihan Bayi.
6.Azzaluman Mutane Zasu Zama Shuwagabanni.
7.Lokaci Zai Zama Gajere,(Da Zarar Gari Ya Waye Sai Kaga Dare Yayi).
8.Zakaga Dan uwa Yana Gudun Dan Uwansa.
9.Addinin Musulunci Zai Kasu Kashi-Kashi.
10.Malaman Addini Zasu Zamo Masu Son Duniya Da Abinda Ke Cikinta.
📌Innalillahi Wa innah Ilaihi Raju'un..
Tabbass Wadannan
Alamomin Sun Bayyana Dikkansu📍
🤔 Ni Yanzu Tinanina Yaushe ne ma Zan Mutu Yau Ko Gobe...?
Kashe Ni Za'ayi, Ko Rashin Lafiya Zanyi, Ko Hatsarin Mota Zanyi, Ko Zan Fada Cikin Rami In Mutu?, Ko Gobara Ce Sanadina, Ko Kuma Haka Kawai Zan Mutu..
Allahu A'alam.
Allah Kasa Muyi Kyakkyawan Karshe Allah Kasa Mu Mutu Da Kalmar Shahada Amin summa Amin
Idan Na Taba Zaluntar Ka/Ki Ina Neman Gafarar Ka/Ki Kafin In Koma Ga Allah Domin Naji Allah Yace Baya Yafe Laifin Dake Tsakanin Bawa Da Bawa.
Dan' Uwa Tunatarwa
Ankawo Facebook ka iya,
Ankawo WhatsApp ka iya,
Ankawo Instagram ka iya,
Ankawo Twitter Ka kware,
ko wane irin Chatting Ka iya.
Shin Ka kware wajen karanta Alqur'ani da sanin Tajwidin sa?
Kuma duk yarigasu jimawa a duniyar nan.
Dan uwa hakika akwai babbar asara idan baka iya karanta Qur'ani ba ko daidai da hizif 1 ne.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce- Azumi da Qur'ani suna ceto
ranar Alqiyama ga ma'abotansu.
Yan Uwa mu kasance ma'abota Qur'ani ba iya ma'abota social media ba.,,
TUNA TARWA CE.
~Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
15/04/2026
SALLAR DARE
Gajeren bayani game da ita,
Ma'anarta:
Sallah ce da ake yi bayan sallar Isha da tsakar dare zuwa asuba, domin neman kusanci da Allah.
Yadda ake yi:. Ana yinta raka’a 2-2 har adadin da zaka iya. . Za ka iya yin 2, 4, 6, 8 ko fiye da hakan.. Anfi so ayi ta d karatu me dan tsaho Amma hakn ba dole bane.
. Ana kammalawa da Sallar Wutiri (raka’a 1, ko 3, ko 5...).
Lokacinta:. Daga bayan Isha har zuwa farkon asuba.. Lokaci mafi falala: shine Ƙarshen dare wato rabin dare na ƙarshe (misali daga 2:30am zuwa asuba).
Ga Falalarta kuma:
1. TaNa kusan ta ka da Allah.
2. Addu’a a cikin dare bata Faduwa.
3. Farfado da ruhin Imani.
4. Tana share zunubi.
5. Yana saka mutum cikin bayin Allah na musamman.
“Wa'ibadur Rahman allazina yamshuna... suna kwana suna roƙon Ubangijinsu.” (Suratul Furqan: 63-64)
Abu mai sauqi:
Idan ba zaka iya tsayuwa sosai ba, ka yi ko 2 raka’a da raka'a 1 na Wutri da niyya me kyau sannan kayaiwata ambaton Allah da istigfari
Addu’a kafin ko bayan sallar dare yana da matuƙar tasiri.
Karka Bar Sallar dare Sabida Bacci Akwai dogon Zamaa a qabari Yafi Ka tashi ka nemi gafarta wajen mai Rahama
Allah yaye Mana Damuwoyin Mu
Ya Bamu iko💚
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Dairah