TEDxZaria
TEDxZaria is making history as the first TEDx event in Hausa - a language spoken by over 150 million people across Africa.
Me ya sa za ka tallafa wa TEDxZaria?
Saboda kana tallafa wa isar da hikimomi masu amfani, ƙarfafa matasa, da taimakawa wajen samar da tasiri mai ɗorewa a cikin al'umma.
Ku kasance cikin masu gina tasiri mai ɗorewa tare da mu.
Domin ƙarin bayani ku ziyarci: www.tedxzaria.org.ng
10/06/2026
Muna kira ga mutane da ƙungiyoyi da ke sha’awar zama abokan haɗin gwiwa (partners) ko masu tallafi (sponsors) na TEDxZaria 2026!
Wannan dama ce gare ku ku zama wani ɓangare na taro mai matukar mahimmanci da tasiri, wanda ke haifar da sabbin ra’ayoyi tare da kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’ummar mu.
Mu haɗa kai mu gina abu mai girma tare!
Don ƙarin bayani, ku ziyarci:
www.tedxzaria.org.ng
ko ku turo mana da saƙo kai tsaye!
---------------------------------------
We are calling on individuals and organizations who are interested in becoming Partners and Sponsors for TEDxZaria 2026!
This is your opportunity to be part of an inspiring event that sparks ideas and drives meaningful change in our community.
Let's build something great together!
For more information, visit www.tedxzaria.org.ng or send us a DM.
Waiwaye Adon Tafiya!
Abubakar Abdulhakeem ya yi mana ɗan tsokaci game da ƙwarewar da ya samu yayin gudanar da aikin taron TEDxZaria na bara 2025
Waye mutum guda da ayyukan sa/ta ke zaburar da kai kullum? Yi masa tag ka faɗi dalili.
06/06/2026
Menene abu ɗaya da kake sa ran samu daga TEDx Zaria da ya sa ya cancanci kuɗin tikiti?
Me ya sa TEDxZaria yake gudana da harshen Hausa? Kuma me ya sa yake da muhimmanci ga al'ummar mu?
A wannan bidiyo, Mal. Khadijah Suleiman ta yi bayani a taƙaice, kan dalilan da s**a sa TEDxZaria ya zaɓi Hausa a matsayin harshen taron, tasirin da yake samarwa, da kuma muhimmancin ci gaba da samun goyon bayan al'umma.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan tafiya don yaɗa tunani masu kawo canji.
03/06/2026
Me Ya Sa Za Ka Tallafa wa TEDxZaria?
Tallafa wa TEDxZaria ba wai kawai saka logo ko tallata suna ba ne. Dama ce ta kasancewa cikin masu gina al'umma ta hanyar ilimi, tunani, da aiki mai kyau.
Ta hanyar ɗaukar nauyi ko haɗin gwiwa da TEDxZaria, za ku samu damar:
✅ Nuna kamfani, masana'anta ko ƙungiyar ku ga ɗalibai, ƙwararrun masana, manya da ƙananan ƴan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire, da sauran masu ruwa da tsaki.
✅ Nuna goyon bayan ku ga ilimi, aiyukan ƙirƙire-ƙirƙire, ci gaban matasa, da kyakkyawan tasiri ga al'umma.
✅ Gina alaƙa mai ƙarfi tsakanin kamfani, masana'anta ko ƙungiyar ku da al'umma.
✅ Haɗuwa da mutane masu basira da hangen nesa da masu kawo sauyi a fannoni daban-daban.
✅ Kasancewa cikin tafiyar da ke taimakawa wajen yaɗa ra'ayoyi da labarai masu amfani da kuma ƙarfafa matasa su ɗauki matakin inganta rayuwar su.
A TEDxZaria, mun yi imani cewa manyan sauye-sauye suna farawa ne daga ra'ayi ko tunani guda ɗaya, amma tasirin su ba shi da iyaka. Kuma suna yiwuwa ne kaɗai idan mutane da ƙungiyoyi s**a ba da goyon baya.
Domin ɗaukar nauyi ko haɗin gwiwa (sponsorship ko partnership), ku tuntuɓe mu ta shafin yanargizon mu ko ku turo mana da saƙo ta nan kai tsaye.
27/05/2026
🌙 Barka da Sallah!
Eid Mubarak from TEDxZaria ✨🌙
Muna yi ma dukkanin musulmin faɗin duniya Barka da Sallah, Allah Ya karɓi ibadun mu, ya sa ayyukan mu su kasance masu amfani da tasiri mai kyau a cikin al’umma. 🤍
Waiwaye Adon Tafiya!
Yahaya Bala Yahayaya yi mana ɗan tsokaci game da ƙwarewar da ya samu yayin gudanar da aikin taron TEDxZaria na bara 2025
Waiwaye Adon Tafiya!
Nasiruddeen Shehu ya yi mana ɗan tsokaci game da ƙwarewar da ya samu yayin gudanar da aikin taron TEDxZaria na bara 2025
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the organization
Telephone
Website
Address
Opening Hours
| Monday | 16:00 - 20:00 |
| Tuesday | 16:00 - 20:00 |
| Wednesday | 16:00 - 20:00 |
| Thursday | 04:00 - 20:00 |
| Friday | 16:00 - 20:00 |
| Saturday | 16:00 - 20:00 |