Credible Time
Credible Times
Your trusted source for fast, reliable, and up-to-date news from around the world. Stay informed. Stay connected.
We bring you breaking stories, politics, entertainment, sports, lifestyle, and trending updates with accuracy and credibility.
Jam'iyyar PDP ta tsaida Professor Isa Ali Pantami a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Gombe a zabe mai zuwa.
Gwamnatin Tinubu ta soke ciyo bashin dala miliyan 717.7 na Bankin Duniya kan gyaran lantarki
Sojoji sun kashe gomman ƴanbindiga a jihar Neja
Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Naiman Hana Goodluck Jonathan Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a 2027
Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin hutun babbar Sallah
ADC a Adamawa ta amince da Atiku Abubakar a matsayi dan takarar shugaban kasa
Sanata Shehu Buba daga jihar Bauchi ya fice daga APC, ya koma PRP
FRSC ta buƙaci matafiya su kauce wa hanyar Abuja-Kaduna saboda cunkoso
Farashin mai a defo zai iya sauka a Nijeriya sakamakon shirin buɗe mashigar Hormuz – Rahoto
25/05/2026
‘Yanbindiga sun kona fadar Sarki tare da sace mata da yara a jihar Kwara
Wasu ‘yanbindiga sun kai hari da tsakar dare a garin Yashikira da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara, inda s**a kai farmaki ofishin ‘yansanda da kuma fadar Sarkin Yashikira tare da kona wani bangare na fadar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 2:00 na dare ranar Litinin, inda s**a rika harbe-harbe wanda ya jefa mazauna yankin cikin firgici tare da sa mutane guduwa zuwa dazuka domin tsira.
An bayyana cewa maharan sun sace kimanin mutum 10, ciki har da wasu mata da yara, yayin da Sarkin Yashikira ya tsallake rijiya da baya ba tare da ya samu rauni ba.
Shugaban karamar hukumar Baruten, Issa Jubril, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa sarkin na cikin koshin lafiya duk da cewa an sace wasu daga cikin mutanen da ke cikin fadar.
Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da harin, yana mai cewa kwamishinan ‘yan sanda ya umarci fara wani samame na musamman tare da hadin gwiwar sojoji, masu gadin dazuka da kungiyoyin sa-kai domin ceto wadanda aka sace da kuma kamo maharan.
Rundunar ta ce an kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke fama da barazanar hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
‘Yan Bindiga Sun Kashe Masu Ibada 3, Sun Sace 15 A Wani Coci A Kwara
Click here to claim your Sponsored Listing.