Hausa24

Hausa24

Share

Hausa24 jarida ce dazata rika kawo muku labrai na kasa Najeriya dawasu sassan duniya

Photos from Hausa24's post 16/01/2023

MAHAWARA: Idan Aka Ce Mutane Biyun Nan Ne 'Yan Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023; Wa Za Ka Zaba?

13/01/2023

Mawakin Kasar Koriya, Pop Brand Ya Gabatar Da Umrarsa Ta Farko Bayan Ya Karbi Musulunci, Inda Kuma Ya Sauya Sunansa Zuwa Daud Kim

13/01/2023

Mijin Balaraba Ganduje Ya Zarge Ta Da Yi Ma Awon Gaba Da Wasu Muhimman Takardun Kadarori Da Ababen Nawa

Mijin 'yar gidan Gwamnan Kano, Asiya Balaraba Ganduje, wato Inuwa Uba, yace Balaraba ta bude masa gida ta yi awon gaba da wasu muhimman takardun kadarorinsa da suke Abuja da Kano, tare da wasu manyan motoci guda uku da mabudai, saboda haka yana bukatar a dawo masa da kadarorinsa kafin ya amince da sakin ta.

Inuwa ya bayyana haka ne ta bakin lauyansa a gaban kotun shari'ar musulunci dake filin Hockey a Kano, karkashin jagorancin mai Shari'a Khadi Abdullahi Halliru, a cigaba da zaman shari'ar da akeyi tsakaninsa da matarsa, wacce ta bukaci kotun ta raba aurensu, bayan shekaru goma sha shida a matsayin ma'aurata, kamar yadda jaridar Daily Nigerian rawaito.

To sai dai bangaren Balaraba, ta bakin lauyanta, Barista Ibrahim Nasarawa, ya musanta zargin awon gaba da kadarorinsa Inuwa, bayan amincewar biyan N50,000 a matsayin sadakin mijin, amma lauyan Inuwa yace basu yarda ba, a basu lokaci domin bayyana adadin kudin da za'a biya su.

Alkali ya bawa lauyan Inuwa mintuna 30 domin ya bayyana adadin kudin da suke bukata, wanda har lokacin ya cika bai samu damar bayyanawa ba, saboda haka aka dage zaman shari'ar har zuwa ranar 19 ga watan da muke ciki na Janairu.

13/01/2023

ZABEN 2023: Atiku ya shiga matsalar bayan Jiga-jigan Kwamitin Yakin Neman zaben sa sun kaurace masa.

Ku shiga wannan alama domin karanta cikakken labarin 👉https://bit.ly/3XlmgoY

13/01/2023

CBN Na Magana...

Tsohuwar N200 da N500 da N1,000 na iya ci gaba da amfani har zuwa ranar 31 ga Janairu, 2023.

13/01/2023

DARA TA CI GIDA: Bakura Buduma Kenan, Jagoran Boko Haram Wanda Yanzu Haka Suke Kare Jini, Biri Jini Da 'Yan Kungiyar ISWAP Kan Rashin Fahimta

Photos from Hausa24's post 13/01/2023

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa Da Ya'yansu Biyu A Daren Jiya

Matar mai suna Bilkisu M Sani da mijinta da ya’yansu su biyu, sun mutu ne a gobarar da ta tashi cikin daren jiya a garin Zaria.

Photos from Hausa24's post 12/01/2023

🇺🇸 Bayan wata mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan California a Amurka, ana ta yunkurin shara tare da gyara barnar da ta yi a ranar Laraba, yayin da aka samu saukin saukar ruwan sama a yankuna da dama.

Photos from Hausa24's post 12/01/2023

Wannan hoton wani abinci ne da ake sarrafawa a wani bangare na Najeriya.

Shin za ku iya fada mana sunansa?
A wane gari kuma ake yin sa?

12/01/2023

Na Kusan Daina Waƙa, Domin Ina Son Na Zama Ɗaya Daga Cikin Waɗanda S**a Fi Shahara Wajen Karatun Kur'ani, Cewar Shahararren Mawaƙi, Ali Jita

Photos from Hausa24's post 12/01/2023

Naira Miliyan 60 Na Kashewa Ummita, Cewar Dan Chanan Da Ya Kashe Ta

A yau Laraba ne dai ɗan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun haɗu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa ɗan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta riƙa karɓar kuɗaɗe a wajen sa, ya ƙara da cewa " haka na riƙa bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na ɓata mata rai. Ma kashe mata kimanin Naira miliyan 60,"

Ya ƙara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, bar hakan ya ɓata masa rai ya koma Abuja da zama.

"Amma duk da haka ta riƙa kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine soyayyar ta mu ta dawo,"

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kuɗi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta deba kula shi.

"Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni," in ji shi

Alƙalin kotun, Sanusi Ado Ma'aji, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya ɗage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

Daga Daily Nigerian

Photos from Hausa24's post 12/01/2023

NEMAN TAIMAKO 😭😭😭

Don Allah don darajar Manzo Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mu taimaka mu ceto rayuwar wannan yaron yana fama da matsanancin ciwo kuma marayane bashi uba mahaifiyarsa bata da kudin da za'a masa aiki suna asibitin dake Gombe anason a masa aiki kimanin kudi dubu 100 shine suke niman taimako ga al'umma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama duk wanda ya taimakawa wani shima Allah zai taimaka masa duniya da lahira koda da sharing zuwa group mu taimaka.

1519664419
Fa'iza, Abdullahi
Access Bank

Allah ya bada ikon taimakawa. Ameen

Don Allah ku taimaka

Want your business to be the top-listed Media Company in Utako?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Area3
Utako
HAUSA24