Alfallatee

Alfallatee

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Alfallatee, Digital creator, .

11/11/2025
11/11/2025

Episode 3

11/11/2025

Episode 2

11/11/2025

Wike Vs Soldiers
Episode 1

Photos from Alfallatee's post 06/11/2025

ALLAH YA ISA! BANDITS SUN CUTAR DA AL’UMMAR FULANI

Allah ya Isa! Wannan kalma ce kawai zamu iya furtawa tsakaninmu da waɗannan yan bandits din da s**a cutar da al’ummarmu ta Fulani fiye da yadda kalmomi zasu iya bayyanawa.

Sun raba da yawa daga cikinmu da dukiyoyinsu, s**a mai dasu talakawa bayan sun taɓa zama masu arziki da daraja.

Sun raba da yawa daga cikinmu da gidajensu da ƙasarsu, s**a tilasta musu yin hijira zuwa makobtan kasashe ko wasu jihohi cikin ƙasƙanci, tsoro da wahala.

Sun bata mana suna gaba ɗaya a idon jama’a, har ta kai ga cewa a wasu wurare, da zarar ka ambaci kalmar “Fulani”, mutane na iya shiga cikin tsoro, su gudu ko su ɓoye, alhali ba kowane ɗan Fulani ne mai laifi ko dan ta'adda ba.

Yanzu al’ummar Fulani sun zama abin tsangwama da wariya a ko’ina; sun zama abin gudu da kyama, k**ar ba ‘yan Adam ba. Wannan abu yana da matuƙar ciwo da takaici, domin ya lalata mutuncin kabilar da aka sani da gaskiya, mutunci, da halin kirki tun fil azal.

Wannan babban zalunci ne da ya haifar da ciwon rai da zubar da mutunci ga al’umma mai tarihi da ɗabi’a irin ta Fulani.

Mutanenmu da aka sani da gaskiya, amana, tausayi da karamci, yanzu an mai dasu k**ar basu da daraja, saboda wasu ‘yan ta’adda da s**a ɓata masu suna.

Ina kira ga Gwamnatin Tarayya, ta Jihohi, da Sarakunanmu na gargajiya dasu tsaya tsayin daka wajen ganin an dawo da mutuncin Fulani, an ware masu gaskiya daga ‘yan ta’adda, kuma a taimaka wa waɗanda s**a rasa komai sanadiyyar wannan masifa.

Haka kuma muna kira da Gwamnati ta ɗauki mataki mai ƙarfi da ya dace akan waɗannan bandits din, domin a kawo ƙarshen zalunci da barna da suke yi wa al’umma.

Muna kuma roƙon kungiyoyin agaji, religious bodies, da masu hannu da shuni, dasu kai taimako ga waɗanda aka zalunta, koda da kayan sawa ne, kayan abinci, da kulawa, domin su san cewa an damu dasu, an san halinda suke ciki.

A matsayinmu na yan Adam, muma muna da haƙƙi na rayuwa cikin aminci da mutunci k**ar kowa. Kada mu bar wasu ‘yan tsiraru su bata mana suna, su kuma hallaka mana al’umma.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Madaukakin sarki ya kawo mana zaman lafiya, Ya tsarkake sunanmu daga abin da bamu da hannu a ciki, Ya kuma dawo mana da mutuncinmu da martabar da muka rasa.

Allah ya kare Fulani, ya kare al’ummar Najeriya baki ɗaya daga fitina, zalunci da tsanantawa.

✍️ Muhammad Khalid Hussaini
(De General)
06/11/2025

29/10/2025

ALKHAIRI ALLAH YA KAIWA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR NEJA

Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, Farmer Muhammad Umar Bago, ya kai ziyara zuwa wata Ruga ta Fulani a cikin Jaharsa, k**ar yadda za ku gani a bidiyo na farko, inda ya gaisa da al’ummar Fulani, ya duba dabbobinsu, sannan yayi alƙawarin tallafa musu da katifu da magungunan dabbobi.

Kamar yadda za ku gani a bidiyo na biyu, Mai Girma Gwamna ya cika wannan alƙawarin, ga katifun nan an kawo musu yadda ya faɗa.

Gaskiya wannan abin ya kara mun natsuwa da gamsuwa a zuciyata, domin soyayyata ga Gwamnanmu tana ƙara ƙaruwa a kullum.

Mutanen da wasu Gwamnoni ke ƙin zuwa wajensu ko guje musu, ko su kafa wata commitee ko gungiya su Shiga daji suta kashesu da dabbobinsu, amma shi Gwamna Bago ya fito fili ya nuna cewa yana ƙaunarsu, yana kallon su a matsayin ’yan Najeriya k**ar kowa, wannan abun Godiya ne ga Gwamna.

Al’ummar Fulani suna cikin ƙalubale a wannan lokaci, kasancewar wasu ’yan ta’adda sun bata musu suna har kalmar Fulani ta zama abin tsoro a bakin wasu da yawa a Qasar nan kuma bawai laifinsu bane saboda yanayi ne da s**a tsinci kansu ne, harma wasu na ganin babu wani Bafulatani na Kwarai suna musu jam'i gaba daya. Amma mun san gaskiya tana nan, kuma muna fatan Allah Ya dawo da martabar Fulani da zaman lafiya a Jiharmu da ƙasa baki ɗaya.

Allah Ya taimaki Mai Girma Gwamna, Yasa a gama lafiya, Ya bada nasara a dukkan al’amura.

✍️: Muhammad Khalid Hussaini
(De General)
29/10/2025

Photos from Alfallatee's post 27/10/2025

MUNA ƘARA KIRA DA CEWA A TAIMAKI FULANIN ƘARAMAR HUKUMAR EDATI, JIHAR NIGER

Cikin tsananin damuwa da tausayawa, muna sake yin kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Neja, da ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu da su gaggauta taimakon Fulani na yankin Edati da s**a shiga cikin mawuyacin hali sak**akon tashin hankali da ya faru a tsakanin Fulani da Nufawa a ranar Alhamis, 23/10/2025.

Kamar yadda muka bayyana a baya, lamarin ya samo asali ne daga wani ƙaramin rikici da ya ɓarke tsakanin wani saurayi ɗan Fulani da wani ɗan banga banufe a gona. A cikin tsautsayi da rikicin ya haifar, sai ɗan Fulani ya jikkata ɗan bangan, wanda daga bisani ya rasu a Asibiti. Hukuma ta k**a wannan ɗan Fulanin, kuma ya amsa laifinsa.

Sai dai bayan rasuwar ɗan bangan, mutanen yankin s**a ɗauki doka a hannunsu, s**a kai farmaki kan rugagen Fulani dake yankin. Sun kashe iyayen yaron dama wasu Fulanin, sun raunata wasu da yawa, sannan s**a ƙone gidaje fiye da 500, tare da lalata dukiya da dabbobi.

A halin yanzu, waɗannan bayin Allah sun rasa komai. Gidajensu sun ƙone, kayan amfanin yau da kullum sun salwanta. Wasu suna kwana a daji akan tsaunuka, saidai su shimfiɗa ganye su kwanta ko tabarma babu, abinci kuwa idan aka kawo har wawaso akeyi tsakanin Yara qanana da Mata, Rayuwarsu ta koma cikin tsananin wahala da yunwa.

Mun samu rahoton kai tsaye daga ɗaya daga cikin wakilan mu na Bago Ruga-Ruga Media Team watau Rabiu Abubakar Alfullerty, wanda yaje yankin. Ya tabbatar mana da cewa halin da waɗannan mutanen suke ciki ba abin misaltuwa bane suna cikin yanayin da kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.

Muna roƙon gwamnati da ƙungiyoyin agaji da duk Wanda Allah ya bashi iko da a taimaka akai gaggawar taimako a basu abinci, tufafi, ruwan sha, magunguna, da wurin zama. Qungiyoyin Fulani anan ne yak**ata ariqa ganinku anan ne yak**ata aji muryoyinku.

Wannan ba lokaci bane na la’antar juna ko nuna banbancin qabila ko wani abu ba, wannan lokaci ne na nuna tausayi da taimakon dan adam.

Wasu na cewa, “Fulani ne, babu komai,” suna ɗora musu laifi saboda wasu ‘yan ta’adda Fulanin ne. Amma dole mu sani ba duk Fulani ne ‘yan ta’adda ba. A gaskiya, Fulanin kirki sune s**a fi fuskantar zalunci da talauci saboda ayyukan ‘yan ta’adda.

Yan ta’addan suna kai farmaki ne domin su kwace shanu, kuma Fulani sune masu shanu. Saboda haka, sune s**afi kowa fuskantar asara da wahala daga sharrin Yan ta'adda. Da dama daga cikinsu suna da daruruwan shanu ada, amma yanzu sun koma marasa galihu da ke jiran taimakon alheri daga al’umma.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya kawowa wadannan bayinsa da s**a tsinci kansu cikin wannan halin mafita, Allah ya kawo mana zaman lafiya da adalci a ƙasarmu, Ya ɗaure zukatanmu da soyayya da fahimta, Ya karemu daga fitina da tashin hankali.

✍️ Muhammad Khalid Hussaini
(DE GENERAL)
28/10/2025

Photos from Alfallatee's post 23/10/2025

SAKON JAJANTAWA GA AL’UMMAR JIHAR NIGER

Cikin sallamawa ga hukuncin Allah Madaukakin Sarki, muke mika sakon ta’aziyya da jaje ga:

Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, H.E. Farmer Umar Mohammed Bago;
Mai Martaba Sarkin Bida, Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar (Etsu Nupe);
Sarkin Fulanin Masarautar Nupe, Dikko Bida;
Da kuma dukkannin al’ummar Jihar Neja, musamman mutanen Zone A, bisa mummunan hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a kauyen Essa na Karamar Hukumar Katcha, wanda ya yi sanadin rasa rayuka masu yawa tare da jikkata wasu da dama.

Haka kuma, muna sake bayyana matuƙar bakin cikinmu da alhini game da rikicin ban tausayi da ya faru tsakanin makiyaya Fulani da al’ummar Nufawa a yankunan Gonagi da Jigi na Karamar Hukumar Edati a Jihar Neja.

Wannan mummunan lamari ya janyo rasan rayuka fiye da mutum biyar (5) Wanda s**a jikkata fiye da mutum ashirin (20), hadeda ƙonewa da rushewar gidaje sama da hamsin (50), tare da asarar dukiyoyi, dabbobi, da kayan rayuwa na al’ummomi da dama. Har yanzu, akwai wasu da ba a san inda suke ba — ko suna raye ko kuma sun rasu — abin da ya rage sai addu’a da tawakkali ga Allah Madaukakin Sarki.

Bazan iya saka wasu daga cikin hotunan anan ba saboda dokan Facebook inba haka ba da na saka maku kunga irin ta'adi da aka samu a wannan rikicin muna fatan Allah ya takaitashi.

Muna mika godiya ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Bida, Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar (Etsu Nupe) bisa irin matakin gaggawa da na uba da ya ɗauka, wanda ya taimaka wajen kwantar da tarzoma da hana ƙarin asarar rayuka.

Haka kuma, muna yaba da ƙoƙarin CSP Bima Enagi, D.P.O na Enagi, tare da Hakiman Gonagi da Jigi, bisa jajircewa da hangen nesa wajen daidaita lamarin tun daga farko.

Sai dai, muna roƙon Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Muhammad Umar Bago, da ya ɗauki matakai masu zuwa:

1. A aika da kayan tallafi da taimakon jinƙai ga waɗanda abin ya shafa, musamman iyalan da s**a rasa matsugunnansu.
2. A umarci jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci ga waɗanda s**a mutu ko s**a jikkata.
3. A gargadi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu, domin irin waɗannan matakai na iya lalata zaman lafiya da haɗin kai da ake ƙoƙarin gina wa.
4. A ƙarfafa jami’an ’yan sanda da DSS wajen inganta tsaro da gudanar da bincike mai zurfi domin hana maimaita irin wannan mummunan lamari.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya jikansu waɗanda s**a rasa rayukansu, Ya ba waɗanda s**a jikkata lafiya cikin gaggawa, kuma Ya tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna, da haɗin kai tsakanin dukkan al’ummomin Jihar Neja.

✍️ Khalid De General
📅 23/10/2025

20/10/2025

Allah yasa mugama da wannan duniyan lafiya

Culinary Team

Attire