Labarun Kafar Labaru

Labarun Kafar Labaru

Share

Kasance da wannan kafa domin samun sahihan labaru ko yaushe

05/08/2026

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya ƙaddamar da aikin faɗaɗa titin cikin garin Mashi mai tsawon kilomita uku kan kuɗi Naira biliyan 5.4.

An ƙaddamar da aikin ne a ranar Talata a garin Mashi da ke ƙaramar hukumar Mashi, inda gwamnan ya bayyana cewa aikin na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa da sauƙaƙa zirga-zirga musamman a yankunan karkara.

Radda ya ce tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bai wa bunƙasa ababen more rayuwa muhimmanci domin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Ya ce ana zaɓen ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa ne bisa irin gudunmawar da za su bayar wajen bunƙasa tattalin arziki da walwalar jama'a, yana mai tabbatar da cewa dukkan ƙananan hukumomin jihar za su amfana da ayyukan ci gaba.

Gwamnan ya yaba wa kamfanin Mothercat Nigeria Limited da kuma Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta jihar ƙarƙashin jagorancin kwamishinanta, Sani Magaji, bisa jajircewarsu wajen gudanar da aikin.

Ya bayyana cewa idan aka kammala titin mai layi biyu, zai inganta harkokin kasuwanci, rage haɗurran ababen hawa tare da sauya fasalin garin Mashi.

Radda ya kuma buƙaci kamfanin da ke aikin da ya tabbatar da ingantaccen aiki cikin wa'adin da aka ba shi, tare da kira ga mazauna yankin da su ba da haɗin kai wajen kare kadarorin gwamnati.

A nasa jawabin, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Mashi/Dutsi, Salisu Yusuf-Majigiri, ya yabawa gwamnan bisa aiwatar da aikin.

Ya ce bayan gwamnatin jihar ta gina titin Shargalle zuwa Dutsi, yanzu kuma al'ummar Mashi sun samu aikin titin kilomita uku daga Government Technical College, Mashi zuwa Government Pilot Day Secondary School, Mashi.

A madadin al'ummar Mashi da Dutsi, Majigiri ya miƙa wa Gwamna Radda doki a matsayin kyauta da nuna godiya.

Sarakunan gargajiya da jami'an gwamnati da ɗimbin mazauna ƙaramar hukumar Mashi ne s**a halarci bikin ƙaddamar da aikin.

05/08/2026

Yan Arewa bazasu zabi Peter Obi ba, domin kuwa bai tuntubemu ba kafin ya fito takara. Haka zalika bai sanya wata jiha a Arewa cikin kwamitin yakin neman zabensa ba -Inji Amb. Abdul Garba Dambature shugabam kungiyar matasan Arewa ta Arewa Youths Assembly for Good Leadership.

05/08/2026

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce zaɓen tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ba zai ƙara wa jam'iyyar ƙarfin lashe zaɓe ba.

Wike ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da manema labarai ta wata-wata a Abuja ranar Talata.

A cewarsa, zaɓen Amaechi na iya amfani wajen tallafa wa yaƙin neman zaɓe ta fuskar kuɗi, amma ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Rivers ɗin ba shi da irin tasirin siyasar da zai iya jawo wa jam'iyyar ƙuri'u masu yawa a zaɓe.

Sai dai Wike bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari ba, kuma Amaechi ko jam'iyyar ADC ba su fitar da martani kan kalaman nasa ba.

05/08/2026

Labaran safe na ranar Laraba 05-08-2026, tare da Hauwa'u Sani.

Photos from Labarun Kafar Labaru's post 05/08/2026

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansur Hassan, ne ya sanar da hakan yau a shafin sa na Facebook.

Ya ce sun kuma samu bindugogi guda goma (10) da sauran manyan kayan laifi da s**a k**a.

04/08/2026

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da cibiyar ba da tallafi da agaji da masu cutat shan inna (sikila)

Wakiliyarmu Hauwa'u Sani ta aiko mana da rahoto.

04/08/2026

An bukaci majalissar dattawa ta janye kudirin neman tallafin kasashen waje.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama da s**a hadar da Amnesty International, CISLAC da SERAP da ma karin wadansu kungiyoyi akalla guda 80 na duniya sun bukaci majalissar dattawan Najeriya da ta janye kudirin neman tallafin kasashen waje.

Kudirin da Sanata Ibrahim Hassan DanKwambo ya gabatar ya nemi majalissar mai lamba 1032 da ta kirkiri kwamitin da zai dinga kula da kuma tantance tallafin da Najeriya ke samu daga kasashen waje.

Sai dai tarin kumgiyoyin sun bukaci majalissar da tayi fatali da wannan bukata, ta kuma maida hankali wajen gabatar da kudirorin da zasu kawo ci gaban kasa da kuma habakar tattalin arziki.

04/08/2026

Fassarar takaitattun labaran rana tare da Hauwa'u Sani..

04/08/2026

Hukumar Tara Haraji ta Kasa (NRS) ta fitar da sabbin ka'idojin yadda za a rika karbar haraji kan kadarori ta hanyar kudaden zamani (virtual assets), inda ta fayyace sharuddan rajista, bayar da rahotanni, adana bayanai da kuma yadda za a tantance darajar irin wadannan kadarori.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, hukumar ta ce ka'idojin sun shafi masu biyan haraji, kamfanonin da ke gudanar da harkokin kadarorin zamani (VASPs), masu gudanar da kasuwannin saye da sayarwa kai tsaye tsakanin mutane (P2P), kwararrun masu ba da haraji da kuma duk wani mutum ko hukuma da ke gudanar da harkokin kadarorin zamani.

Hukumar ta bayyana cewa sabbin ka'idojin na da nufin inganta bin dokokin haraji, kara tabbatar da gaskiya da kuma daidaita tsarin harajin kadarorin zamani a Najeriya.

04/08/2026

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo, ba s**a ba, kan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron bunkasa tattalin arziki da zuba jari a Jihar Delta da aka gudanar a Asaba, babban birnin jihar.

Ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta sak**akon sauye-sauyen, matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka suna da nufin gina tattalin arzikin Najeriya mai dorewa, tare da jaddada cewa sak**akon gyare-gyaren zai kara bayyana a nan gaba.

Telephone