Thabit Muhammad Ala
The mission of this channel is to convey the message of Islam to all the people around the globe.
23/04/2026
Wanann 1k Kuwaiti Dinar daidai take da naira miliyan 4 da dubu ɗari 3 😂😂
13/04/2026
Ma sha Allah. Muna taya Sheikh Bashir Aliyu Umar murna da samun promotion na matsayin Professor a Department na Islamic Studies, Bayero University, Kano (BUK).
Muna addu'a Allah ya sa albarka a wannan matsayi da ya samu. Allah ubangiji ya sa al'ummar Musulmai su ci gaba da amfana da ilimi da muqamin Sheikh Professor Bashir Aliyu Umar,. Ameen.
Duk wanda ya zagi manzon Allah tsakaninmu dashi kisa ne kawai....
Wannan itace aƙidarmu harmu koma ga Allah.
Idan Allah ya yika a Najeriya so yake ya jarrabeka..
03/04/2026
•'Yan uwa don Allah ku ƙara saka malamin Sunnah Sheikh Abdulrazak Yahya Haifan a Addu'a har yanzu yana jin jiki.
Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne Ameen.
Asalin Jos Garin Musulmi ne,
Saurara kaji yadda akayi....
02/04/2026
SAKAMAKON CIN NAMAN MUTANE
Al Imam Junaidul Baghdadi (rah) yace:
"Watarana ina tsaye a masallaci tare da jama'a masu yawa muna jiran isowar wata sallar janazah da za'a kawo, chan sai na hangi wani Almajiri, Faqiri, sufi (irin masu gudun duniyar nan).
Da ka kalleshi zaka ga alamar yawan ibadah atare dashi... Yana barar abincin da zai ci awajen mutane.
Sai na fa'da (acikin raina) "Yanzu wannan mai zai hana yaje yayi wani aikin da zai rika ciyar da kansa, ai da yafi masa".
Bayan na juya zuwa gidana, alhali ina da wasu ayyukan ibadah irin na yau da kullum da nake son yi, amma hakan bai yiwu ba. Kuma barci ya gagareni.
Chan cikin dare da barci ya daukeni sai nayi mafarki. Naga wannan mutumin ya zama gawa, an kwantar dashi agabana akan tebur, aka ce mun "GASHI NAN CI NAMANSA, TUNDA KAYI GULMARSA.. IN BA HAKA BA KUMA, TO KAJE KA NEMESHI YA YAFE MAKA".
Sai na farka a firgice, na tafi cikin Masallacin nan ina ta dubawa ko zan samu wannan mutumin. Nayi ta nemansa sai bayan kwana uku sannan na hadu dashi.
Yana kallona sai yace mun "Yanzu kai Junaidu, kamar kai, ka rika cin naman mutane!?."
Daga jin haka ban san lokacin da na suma ba.. Da na farfado na ganshi yana tare dani. Sai yace mun ''Shin zaka Qara?". Nace masa ''A'a". Sai yace "To Allah shi gafarta mana baki daya".
Shikenan sai ya tafi, tun daga ranar ban sake ganinsa ba...
(Shaikh Abdurrahman Ibnul Jawzee ne ya kawo wannan Qissar acikin littafinsa Uyunul Hikayaat).
BAYANI
********
Wannan labarin yana karantar damu abubuwa da yawa. Daga cikinsu akwai :
1. Muhimmancin kiyaye harshenka dake cikin bakinka, da kuma harshen zuciyarka daga cin naman mutane. Har ma da harshenka dake bisa yatsunka da kake yin rubutu dasu da alkalami ko rubutu a internet.
2. Allah yana da Salihan bayinsa wadanda ya boyesu acikin siffofi daban daban. Don haka kar ka raina mutum don ka ganshi acikin yagaggun tufafi, ko don bashi da komai.
3. Laifin da wani yayi aka kyaleshi, wani kuma idan yayi sai an nuna masa kuskurensa.
4. Ka rika amsa laifinka da neman yafewar kusakurenka komai kankantarsa.
Allah yasa mu dace. Ameeen.
Allah yasa daliban Zauren Fiqhu da dukkan sauran jama'a zamu dubi wannan madubi da kyau domin amfanar rayuwarmu. Ameeen.
31/03/2026
2023
KWANKWASO / ABBA
GANDUJE / GAWUNA
2027
KWANKWASO / GAWUNA
GANDUJE / ABBA
DARASI:- A RAYUWA BABU MAƘIYI NA DINDINDIN, BABU MASOYI NA DINDINDIN,
MAƘIYINKA A YAU ZAI IYA ZAMA MASOYINKA GOBE,
MASOYINKA A YAU ZAI IYA ZAMA MAƘIYINKA GOBE.
MUBI DUNIYA A HANKALI...
AZZALUMAN KASAR NAN SUNE DAI A APC, SUNE DAI AZZALUMAN DA S**A KOMA APC. SUNE DAI AZZALUMAN DA SUKETA TURURUWAR KOMAWA ADC. 😭😭
30/03/2026
Jan Hankali ga ’yan Najeriya,
Suna tunanin mu jahilai ne kuma masu sauƙin ruɗewa. Suna ƙoƙarin tada rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci domin su ruguza Najeriya su kuma sace albarkatunmu.
Idan s**a ga wani yana yada rarrabuwar kai, tashin hankali ko ta’addanci, sai su ɗauke shi ƙarƙashin kulawarsu su kuma ba shi kuɗi. Amurka ma tana tallafa wa masu tsattsauran ra’ayi daga ɓangarorin Musulmi da Kiristoci domin cimma manufofinta na sabon mulkin mallaka.
A wasu lokuta ma suna ɗaukar nauyin kai hari ga Kiristoci, sannan su ɗora laifi a kan Musulmi, alhali kuwa mai imani na gaskiya ba zai aikata irin wannan ba. Haka ma a ɓangaren Kiristoci, babu Kirista mai hankali da zai goyi bayan ta’addanci.
Wasu ’yan Najeriya marasa ɗa’a suna buɗe shafukan sada zumunta suna nuna kansu a matsayin Musulmi ko Kirista, suna zargin ɗayan ɓangaren tare da yada ƙarya da farfaganda.
A zahiri, wani ɗan Arewa yana s**ar kisan gilla da ake yi wa ’yan Arewa a Kudancin Najeriya da kuma hare-haren ƙungiyoyin Berom a Jos, ba wai yana kira ga rikicin addini ba. Abin takaici ne yadda wasu mutane, musamman waɗanda Fulani ’yan bindiga s**a cutar, ko wasu da ke ɓoye kansu da sunan Fulani, suke ɗora laifi a kan dukkan Arewa.
Addininmu yana koyar da kare rayuka ta hanyar Maqasid, kuma ba ya umartar mu mu bari a hallaka mu saboda wasu sun cutar da wasu.
Idan hukumomi s**a kasa dakatar da ta’addanci da kuma yaɗa ƙazafi a kan Musulunci da Musulmi, ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya ba. Dole ne DSS ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
Duk wani Musulmi ko Kirista da ya ga wani abu mara kyau ya kamata ya kai rahoto ga hukumomin da s**a dace, ba ni ko mutanena ba. Bisa doka, su ne ke da alhakin tsaron jama’a.
Idan laifi ya ci gaba ba tare da hukunci ba, mutane za su iya ɗaukar doka a hannunsu, wanda hakan haɗari ne kuma ba zai kawo zaman lafiya ba.
Ni ɗan Najeriya ne, Musulmi kuma mai kishin ƙasa.
ina son zaman lafiya ga al’ummata. Dimokuraɗiyya tana nufin wakilci, kuma dole ne in yi magana idan an tauye haƙƙin mutanena.
Ya kamata ku ma ku yi haka ga naku.
Dole ne mu rika kai rahoton duk wani laifi ba tare da son zuciya ba. Don haɗin kan ƙasa, dole mu ajiye bambance-bambancenmu mu yi aiki tare.
Alex, wani ɗan Amurka, ya yi amfani da ayoyin Alƙur’ani ba tare da ilimi ba domin tayar da hankali da ruɗar Kiristoci a Jos su ɗauki mataki a kan Musulmai marasa laifi.
Ya yi ƙoƙarin jan hankalinsu su ɗauki doka a hannunsu.
Muna jajanta wa Kiristoci marasa laifi da aka kashe ta hannun ’yan ta’adda da ake ɗaukar nauyinsu.
Muna kira ga DSS da ta binciki Alex, ta gano masu hannu a lamarin, tare da hana rikici ya ƙaru. Bai kamata ’yan ƙasa su rama ba; aiwatar da doka aikin gwamnati ne.
Amma ’yan ƙasa za su iya haɗa kai su rika kai rahoton duk wani abu da ya zama abin zargi domin tallafa wa tsaron ƙasa.
Gwamnatin Tinubu ta gaza wajen tsaro da tattalin arziki saboda ta fifita siyasa.
29/03/2026
Mutum 5 ne matsalar Nijeriya.
1— Ɓarayin ƴan Siyasa.
2— Kwaɗayayyun Maluman Addini.
3— Kidahuman Talakawan da basu fahimci manufar halittar su ba.
4— Matasa masu matacciyar zuciyar da suke jiran komi sai de a ɗauka a basu.
5— Ƴan Kasuwar da basa bambace RIBA da kuma REEBA.
In akwai abinda na manta masu muhimmanci wurin lalata ƙasar nan da hana ta cigaba, kawo mana a Comment Section.
Click here to claim your Sponsored Listing.