Arewa News Update

Arewa News Update

Share

Shafin Gidan Jaridar Arewa News Update Yanakawo Muku Sahihan Labarai Masu Inganci.

26/02/2026

ADC da NNPP sun watsi da sabuwar dokar zaɓe da Tinubu ya sanya wa hannu

Jam’iyyun ADC da NNPP sun yi watsi da dokar gyaran zaɓe ta 2026 da aka sanya wa hannu, suna mai cewa tana barazana ga dimokuraɗiyya kuma tana ƙoƙarin jefa ƙasar cikin tsarin jam’iyya ɗaya.

Shugaban NNPP na ƙasa, Ajuji Ahmed, ya bayyana haka a Abuja a madadin jam’iyyun adawa, inda ya ce za su yi amfani da duk hanyoyin da doka ta tanada domin dakile aiwatar da dokar.

Jam’iyyun sun kuma buƙaci majalisar dokoki ta sake duba dokar tare da cire tanade-tanaden da s**a ce ba su dace ba, domin tabbatar da sahihin zaɓe mai ‘yanci da gaskiya a Najeriya.

26/02/2026

Matasa na barazanar fara tattakin mutum miliyan 1 a Abuja kan ci gaba da tsare El-rufai

Zanga-zanga ta ɓarke a wasu sassan Jihar Kaduna kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, inda matasa s**a nemi a sake shi nan take.

Masu zanga-zangar sun ce tsare shi duk da shari’ar da ke gaban kotu na tayar da tambayoyi kan bin doka, tare da barazanar shirya tattakin mutum miliyan ɗaya a Abuja idan ba a sake shi ba.

Wasu ‘yan adawa sun danganta lamarin da abin da s**a kira takura wa muryoyin adawa, suna mai cewa har da k**a tsohon AGF, Abubakar Malami.

Zanga-zangar ta zo ne yayin da jami’an DSS s**a gaza gabatar da shi a kotu kan zargin laifukan yanar gizo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an gudanar da zanga-zangar a Kaduna da Kafanchan cikin lumana, ba tare da rahoton tashin hankali ba.

18/02/2026

Hisbah a Kano ta haramta wa direbobin Adaidaita Sahu sanya wando 'three-quarter' cikin azumi

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta haramta wa direbobin babura masu kafa uku, da aka fi sani da adaidaita sahu, sanya wandon uku-kwata a duk tsawon watan Ramadan.

Matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamandan hukumar, Mujahid Aminuddeen, ya fitar a ranar Laraba.

18/02/2026

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin tafisirin azumin Ramdana a masallacin fadar shugaban ƙasa, ranar Laraba.

A cikin jawabin nasa, Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kai domin kawo ci gaba.

18/02/2026

Shugaba Tinubu ya dakatar da ciccira kudin mai, ya umurci a tura kudaden kai tsaye asusun tarayya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan wata doka da ta soke yadda ake ciccira kudaden mai da gas, inda ya umurci kamfanin NNPC Limited da sauran masu aiki a bangaren su rika tura Royalty Oil, Tax Oil, Profit Oil, Profit Gas da sauran kudaden da s**a dace kai tsaye zuwa Federation Account.

Dokar ta kuma dakatar da kaso 30% na Frontier Exploration Fund da kuma management fee na 30% da NNPCL ke rike da su, tare da sauya kudaden Gas Flare Penalty su rika shiga asusun tarayya.

Gwamnatin ta ce matakin na da nufin rage asarar kudade, inganta gaskiya da kara kudaden shiga domin tallafa wa muhimman bukatun kasa k**ar tsaro, ilimi da kiwon lafiya.

Photos from Arewa News Update's post 18/02/2026

Yadda Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe mai cike da takaddama da za a yi amfani da ita a zaben 2027

17/02/2026

Babu wata tattaunawa da muke yi don komawa ta Real Madrid - José Mourinho

Tsohon kocin ƙungiyar Real Madrid, José Mourinho, ya ce babu wata tattaunawa ko damar komawarsa horar da Real Madrid a halin yanzu, inda ya jaddada cewa a babu wani abu da ke nuna zai koma ƙungiyar.

Mourinho ya ce har yanzu yana da sauran shekara ɗaya a kwantiraginsa da kungiyar da yake jagoranta Benfica.

Photos from Arewa News Update's post 17/02/2026

Da ɗumi-ɗumi: Sowore ya tabbatar da zargin El-Rufa’i kan shigo da sinadarin guba Najeriya Yace an fara amfani da gubar a kansu.

Dan gwagwarmaya a fannin siyasa, Omoyele Sowore, ya ce zargin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi na cewa an shigo da sinadarin guba mai suna thallium sulphate zuwa Najeriya ya fara tabbata bisa alama.

Sowore ya bayyana hakan ne yayin wata zanga-zanga da suke gudanarwa a harabar Majalisar Ƙasa kan batun dokar zaɓe, inda ya yi ikirarin cewa jami’an ‘yan sanda sun harba musu wani irin gas da ba barkonon tsohuwa ba ne k**ar yadda aka saba amfani da shi wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Ya ce abin da aka harba musu na iya kasancewa wani nau’in guba, yana mai ƙara da cewa tun da farko El-Rufa’i ya yi gargadin cewa an shigo da sinadari mai matuƙar haɗari cikin ƙasar.

Haka kuma ya tunatar da cewa tsohon gwamnan ya rubuta wasiƙa ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin neman ƙarin bayani kan dalilin shigo da wannan sinadari.

Har zuwa yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye da ke tabbatar ko musanta zargin ba, lamarin da ke ƙara jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan ƙasa.

17/02/2026

Alhamdulillah anga watan Ramadan a Saudi Arabia 🌙

Photos from Arewa News Update's post 16/02/2026

Yaune Gwamna Jahar Kano Eng Abba Kabir Yusuf Akai Taron Bikin Komassa Jam'iyar APC Saida Naga Wasu Mutane Tari Guda Dakaya Irin Na Firsinoni Komai Hakan Yake Nufi?

Cewar Waleed Adamu Kawu Uba Dan Gwagwarmaya.

15/02/2026

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin jajantawa da kuma tallafa wa waɗanda gobarar kasuwar Singa ta shafa.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, da ya sanar da haka a ranar Lahadi, ya ce tawagar, wadda za ta taso daga Abuja gobe, za ta miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga yan kasuwar da s**a yi asarar biliyoyin Naira sak**akon gobarar da ta tashi a kasuwar.

A madadin gwamnatin tarayya, tawagar za ta kuma yi alƙawarin bayar da tallafin kuɗi domin taimaka wa ƴan kasuwar da abin ya shafa, tare da tallafa wa gwamnatin jihar Kano wajen gaggauta buɗe kasuwar domin komawa harkokin kasuwanci.

15/02/2026

Rukunin farko na sojojin Amurka da jiragen yaƙi sun iso Najeriya

Rukunin farko na sojojin Amurka tare da jiragen yaƙi guda biyar sun iso arewa maso gabashin Najeriya domin fara haɗin gwiwar farmaki kan ‘yan ta’addan ISWAP.

Jaridar The New York Times ta rawaito cewa wani jirgin sojan Amurka ya sauka a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a daren Alhamis, yayin da ake sauke kayan aiki daga wasu jirage da s**a iso.

Kamfanin Reuters ya ce Amurka za ta tura sojoji 200 domin horas da rundunar sojin Najeriya, tare da ƙara wa wasu jami’an Amurka da ke ƙasar ƙarfi.

Wannan mataki na zuwa ne bayan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu. A makon da ya gabata, kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka ya ziyarci Abuja inda ya gana da Shugaba Bola Tinubu da manyan jami’an tsaro.

Jami’an Amurka sun ce sabbin sojojin za su mayar da hankali kan tattara bayanan sirri da kuma tallafa wa sojojin Najeriya a yaƙi da ta’addanci.

Telephone

Website