Bahaushe
Bahaushe kafa ce ta yanar gizo dake samar da bayanai na al'amura dake wakana a duniyar malam Bahaushe
09/01/2023
Rikici ya Barke a jam'iyyar PDP reshen Kano biyo bayan hukuncin sabawa hukunci kotu.
A baya-bayan nan ne dai rikici ya barke tsakanin tsagin Sadiq Wali da kuma tsagin Muhammad Abacha bayan da wata kotun tarayya ta tabbatar wa da tsagin Muhammad Abacha takarar Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Sai dai abin da ya rura wutar Rikicin a kwana-kwanan shine ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe da tsagin Sadiq Wali s**a yi duk da harmacin kotu akan takarar su.
Sai dai tsagin na Muhammad Abacha sun fito sun yi Alla-wadai da wannan mataki suna cewa nuna raini ne ga kotu.
To sai dai bangaren Sadiq Wali wanda ya ƙaddamar da kwamitin ya ce, waɗanda suke s**ar wannan matakin ba su fahimci tsarin ba, a cewar kakakinsu Dakta Yusuf Bello Danbatta.
09/01/2023
Ɗan takarar shugabancin ƙasa daga jam'iyyar Labour Party, Peter Obi yayi alƙawarin bawa mata kulawa ta musamman idan har ya zama shugaban ƙasar Najeriya.
Ɗan takarar yayi wannan alƙawarin ne a wani taro na " People's Townhall 2023" wanda gidan talabijin na Channels ya shirya a ranar Lahadi.
Obi yayi alƙawarin bibiyar duk ƙudurirrikan da majalisa ta tara tayi watsi da su.
A ƙarshe ɗan takarar ya tabbatar da cewa matasa da mata zasu kasance babban jigo na gwamnatin sa.
16/12/2022
IPOB : Masu sayar da abinci sun nisanci kai hajarsu Kudu musu gabas.
Shuwagabannin wasu gamayyar yan kasuwa dake kasuwanci a kudu masu gabashin ƙasar nan sun umarci mambobin su dasu ƙauracewa yankin.
Wannan hukunci ya biyo bayan kashe membobin su da haramtacciyar ƙungiyar nan ta IPOB ta yi.
16/12/2022
Gwamnatin Tarayya zata gina wurin samar da wutar lantarki na gwaji mai amfani da iska wanda zai samar da 30 megawatts a Jaredi dake ƙaramar hukumar Shagari ta jahar Sokoto.
14/12/2022
Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran shugabannin Afrika a Washington DC dake ƙasar Amurka domin halartar taron bunƙasa dangantaka tsakanin Amurka da kuma yankin Afirka.
Muna sanar da masu bibiyar mu cewa account ɗin mu na kan Instagram yana wallafa bayanai akai-akai. Ku danna wannan link ɗin domin following ɗin mu :
I'm on Instagram as . Install the app to follow my photos and videos.
10/10/2022
Ƴan Daba sun Farmaki Mai Temakawa Ganduje.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Bakarabe Kofar Na’isa, yayi zargin cewa wasu ƴan daba da yake kyauta zan ƴan kwankwasiya ne sun farmasa sannan sun ɗauke wayar sa.
Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook, inda ya bayyana cewa sun farmake shine da shida wasu mazauna a ƙofar Ɗanagundi a ranar Lahadi da yamma.
Ƙofar Na'isa ya ce : " Ƴan daba sun farmake ni da wuƙa a Ƙofar Ɗanagundi, sannan s**a ƙwace wayata dake ɗauke da layina na MTN.
Cikin yardar Allah ban samu wani babban rauni ba amma sun yi nasarar ƙwacen waya.
Ina roƙon Allah ya cigaba da kare rayuwar mu daga irin waɗannan ayyukan".
10/10/2022
Akwa Ibom Ta Cika Maƙil Tana Magoya Bayan Atiku
A yanzu haka babban birnin jihar Akwa Ibom ya cika Maƙil da magoya bayan ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar PDP, Atiku Abubakar.
A yau ne ɗan takarar ya fara gudanar da kamfen ɗinsa a hukumance farawa da jihar Akwa Ibom.
Atiku ya halarci filin kamfen ɗin tare da rakiyar mataimakinsa Gwamna Ifeanyi Okowa, da shugaban kamfen ɗinsa, da Gwamnan Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel, da kuma sauran gwamnoni da manya a jam'iyyar ta PDP.
09/10/2022
Atiku ya sauka a Jihar Uyo
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya sauka a jihar Uyo domin fara kamfen ɗin sa na zaɓen 2023.
09/10/2022
Hotunan Cincirindon Al'ummar Musulmi yayin mauludin fiyayyen halitta a ƙasar Yemen
09/10/2022
Hotunan Ƴan Kwankwasiya Yayinda Jagora zai ƙaddamar da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓe.
Yanzu haka birnin Kano a cike yake yayinda magoya bayan ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso zai ƙaddamar da Ofishin Yaƙin neman zabe.
09/10/2022
Hotunan Gangamin Marawa Tinubu Baya ya Jawo Cunkushewar Hanyoyi a Jihar Legas.
A yanzu haka dai ana zaune a cunkushe a sassa daban-daban na jihar Legas sakamakon taron hadin kan da aka yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyya mai mulki ta APC.
Musiliu Akinsanya, tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), ya sanar da gudanar da gagarumin gangamin ne ga Tinubu sakamakon magoya Peter Obi sun yi tattaki a titunan Legas a makon jiya.
Hakan yana zuwa kusan a matsayin martani ga magoya bayan Peter Obi. Inda s**a cika titunan Legas suna kirari : “Se Jagaban”, “Tinubu don shugaban kasa” .
Wannan taro dai ya haifar da cunkushewar hanyoyi wanda hakan ya sa da ƙyar ababan hawa ke wucewa.