M S R Hausa

M S R Hausa

Share

I am journalist
Content creator
Advertiser

Photos from M S R Hausa's post 12/09/2026

MAI MARTABA SARKIN POTISKUM YA ZIYARCI GUMEL:

Mai Martaba Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, OON, FICEN, ABSWA, CP (RTD), tare da tawagarsa, sun kai ziyarar ta’aziyya zuwa Gumel, Jihar Jigawa, bisa rasuwar Marigayi Mai Martaba Ahmed Mohammed Sani, tare da taya sabon Mai Martaba Sarkin Gumel, Lawan Muhammad-Sani, murnar hawa karagar mulki a matsayin Sarkin Gumel na 17.

Mai Martaba Sarkin Potiskum ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Masarautar Gumel, tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa Marigayin, Ya jikansa, Ya kuma ba iyalansa da al’ummar Masarautar Gumel hakurin jure wannan babban rashi.

Haka kuma, Mai Martaba ya taya sabon Sarkin Gumel murna, tare da addu’ar Allah Ya ba shi hikima, basira da ikon jagorantar al’ummarsa cikin adalci da zaman lafiya.

Allah Ya jikansa, Ya ƙara wa sabon Sarki lafiya da ikon sauke nauyin sarauta. Amin.


M S R Hausa

08/09/2026

🚨💔 ABUBUWAN DA AKA BAR A BAYA A BALLON D’OR 2026! 🚫🏆
An bar wasu manyan ’yan wasa a wajen jerin ’yan takara 30 na ƙarshe… 😳✂️
⛔️🇧🇷 Raphinha
⛔️🇫🇷 Désiré Doué
⛔️🇫🇷 Bradley Barcola
⛔️🇪🇸 Pedri
⛔️🇦🇷 Julián Álvarez
⛔️🇵🇹 Cristiano Ronaldo
⛔️🇦🇷 Enzo Fernández
⛔️🇪🇸 Mikel Oyarzabal
⛔️🇫🇷 Rayan Cherki
⛔️🏴 Bukayo Saka
⛔️🇪🇸 Dani Olmo
🤯 WANENE AKA FI BARINSA A BAYA BA TARE DA AN SA SHI BA?
👀 Ka ambaci ɗan wasa guda ɗaya da kake ganin lallai ya cancanci shiga jerin ’yan takarar Ballon d’Or! 🏆👇

08/09/2026

🚨 GA SHI! An fitar da sunayen ‘yan wasa 30 da aka zaɓa a hukumance domin neman kyautar Ballon d’Or 2026! 🌕✨

🏴🇬🇧 Harry Kane
🇧🇷 Vinicius Jr
🇪🇸 Fabián Ruiz
🇵🇹 Vitinha
🇪🇸 Ferran Torres
🇫🇷 William Saliba
🇫🇷 Dayot Upamecano
🇵🇹 Bruno Fernandes
🇪🇸 Pau Cubarsí
🇪🇸 Marc Cucurella
🏴🇬🇧 Jude Bellingham
🇫🇷 Ousmane Dembélé
🇨🇴 Luis Díaz
🇪🇸 Lamine Yamal
🇳🇴 Erling Haaland
🇧🇷 Gabriel Magalhães
🇲🇦 Achraf Hakimi
🇬🇪 Khvicha Kvaratskhelia
🇦🇷 Lionel Messi
🇸🇳 Sadio Mané
🇧🇷 Marquinhos
🇦🇷 Lautaro Martínez
🇫🇷 Kylian Mbappé
🇵🇹 Nuno Mendes
🇵🇹 João Neves
🇫🇷 Michael Olise
🇪🇨 William Pacho
🇲🇽 Julián Quiñones
🇪🇸 Rodri
🏴🇬🇧 Declan Rice

🏆 KU KAKE: WANE NE ZAI LASHE BALLON D’OR 2026? 👀🔥

Photos from M S R Hausa's post 07/09/2026

A Yau ne Mai Martaba Sarkin Potiskum Alh Umaru Bubaram ibn Wuriwa Bauya OON CCA CP RTD Sarki na Ashirin da Shida a jerin sarakunan garin Potiskum ya halarci taron ƙaddamar da aikin da Hukumar Rundunar Sojin Sama ta aiwatar ƙarkashin Jagorancin Jami'inta AVM. Idi Sani Badejo a Makarantar Sabon Gari dake garin Potiskum

Mai Potiskum ya yaba wa Rundunar Sojin Sama da AVM Idi Sani Badejo wadda ɗa ne a masarautar bisa kawo ayyukan ci gaba a garin na Potiskum.
Bayan haka Mai Martaba Sarki Ya musu addu'oi da Fatan Alkairi.

Taron ya samu Halartar Mai Girma Gwamnan Jahar Yobe Hon. Mai Mala Buni Con. (Yerman Potiskum) Wadda Kwamishinan Haɓaka Arzikin Al'umma, Hon Alh Aji Yarima Bularafa Ya Wakilce shi, Shugaban Rundunar Sojin Sama da Sauran Manyan Baki.

An aiwatar da ayyuka ne domin ƙara inganta harkar ilimi da kuma sauwaƙa wa al'ummah don samun sauƙin samu ruwan sha cikin sauƙi.

Ayyukan sun haɗa da sabunta azuzuwa a Makarantar Sabon Gari da Kuma Samar da Bohol Masu Amfani da Hasken Rana a Gurare Kamar Haka Nahuta Yindiski Gakoko Dakuma Maina Kaina Duka Acikin Garin Potiskum.

M S R Hausa

05/09/2026

LABARI MAI ZAFI: An ƙara Lamine Yamal cikin rukunin kyaftin-kyaftin na Barcelona bayan ƙuri’ar ’yan wasa! 🔵🔴
An yanke shawarar ƙara Lamine Yamal cikin ’yan wasa biyar da ke cikin rukunin kyaftin bayan da ’yan wasan ƙungiyar s**a kada ƙuri’a a cikin gida, kuma an tabbatar da hakan a hukumance.
Kyaftin-kyaftin ɗin Barcelona yanzu su ne:
🛡️ Raphinha
🛡️ Pedri
🛡️ Frenkie de Jong
🛡️ Eric García
🛡️ Lamine Yamal
A yanzu Yamal yana cikin rukunin shugabancin Barcelona yana da shekaru 19, kuma hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin ƙananan shekaru da s**a taɓa zama kyaftin a tarihin Barcelona. 🔵🔴🛡️

01/09/2026

Gwarzon ƙwallon ƙafa ɗan Argentina, Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa-da-ƙasa, wanda ke nufin ba zai sake buga wa tawagar ƙasarsa Argentina wasa ba.

Messi ya sanar da ritayar ne a saƙonsa na Instagram a Litinin 31 ga Agustan 2026, inda ya ce, “Bayan duka wannan lokaci tun daga wasan ƙarshe [na FIFA 2026], sannan bayan yin nazari sosai, ina mai sanar da kowa cewa na yi ritaya daga tawagar ƙasata”.

“Mataki ne mai ciwo, kuma har yanzu yana min ciwo a rai, amma na fahimci cewa wannan ne lokacin da ya dace. Ina mai rantsuwa cewa na sadaukar da komai, ba kawai a ‘yan shekarun baya ba lokacin da muka lashe komai, amma har kafin nan ma. Na yi yaƙi da sadaukarwa don wannan jesin, don ba ku nishaɗi da alfaharin kasancewa ‘yan Argentina ta amfani da ƙwallon ƙafa.”

29/08/2026

🚨 LABARI MAI ZAFI: Dibu Martínez ya isa domin sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Chelsea! 🔵🇦🇷
Chelsea da Aston Villa suna musayar takardun yarjejeniya bayan sun cimma matsaya a daren jiya. Jimillar kuɗin cinikin golan Argentina ɗin zai kasance £7.5m.
Dibu ya amince da dukkan sharuɗɗan cinikin tun kwanaki biyu da s**a wuce. Yau ya isa London domin sanya hannu kan kwantiragin bayan gwajin lafiya. Zai kasance a Chelsea har zuwa 2028. ✍🏼
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi zaɓin ƙara kwantiragi har zuwa Yunin 2029. 🔐
👀 Dibu na zuwa Stamford Bridge! 🔵🔥

27/08/2026

LABARI MAI ZAFI: Julián Álvarez ya sake rasa atisayen kungiyar, karo na biyu a jere. 🤒❌
“Julián Álvarez ya sake sanar da kulob ɗin cewa ba ya jin daɗi, saboda haka ba zai iya yin atisaye tare da sauran ’yan wasan ba,” in ji Marca.
Arsenal na ci gaba da bibiyar lamarin a hankali, domin ganin ko Julián zai yanke shawarar buɗe ƙofa ga Arsenal, yayin da shi kuma har yanzu yake son komawa Barcelona kuma yake dagewa kan hakan. 👀
👊🏼🇦🇷 Allah Ya ba ka lafiya, Julián!

19/08/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Turkiyya sun ce tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Real Madrid da Brazil, Roberto Carlos, ya rungumi addinin Musulunci.

A cewar rahotannin, Carlos mai shekaru 53 ya karɓi Shahada ne kimanin makonni huɗu da s**a gabata, yayin wata ziyara da ya kai wajen Sheikh Jihad Hamada, wani fitaccen malami kuma ɗaya daga cikin sanannun mutane a al’ummar Musulmi a Brazil.

Rahotannin sun ce ɗan wasan ya daɗe yana tuntuɓar Sheikh Jihad Hamada kafin daga bisani ya kai masa ziyara, inda ake zargin ya furta Kalmar Shahada tare da zaɓar addinin muslunci

Want your business to be the top-listed Media Company in Potiskum?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Gishuwa Dabuwa Potiskum
Potiskum