BAGA GIDA

BAGA GIDA

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from BAGA GIDA, Photographer, BAGA WARDS, Maiduguri.

Ƙaunar gaskiya, ciyar da al'umma gaba, da kare martabar addini da al'ada. βœοΈπŸ“š
Mai raba ilimi, faΙ—akarwa, nishadi da gina tunani. πŸ’‘
Biyo ni don abun da ke da amfani a yau da gobe! πŸ”₯

02/09/2025

*πŸŒ™ Daren Alheri Masoya Gaskiya!*

Yau da dare muna roΖ™on Allah da Ya kawo *zaman lafiya* a Arewacin Najeriya da tafkin Chadi gaba Ι—aya.
Mu daina Ι—aukar zalunci da rikici a matsayin jarumta β€” *jarumta gaskiya shine yafiya da sulhu.*
Idan ka mallaki zuciyar ka, ka riga ka ci nasara a rayuwa.

πŸ•―οΈ *Ya Allah Ka kare mana rayukan bayinka, Ka gafarta mana kurakuranmu*
🀲🏼 *Ka tabbatar mana da shugabanni na gari da malamai na kwarai*

*Ka tuna:* Ranar Allah bata da dare β€” komai nisan dare, gari zai waye!

β€” *Ibrahim Musa Dan Hijira*
πŸ“Baga Town, Taraba State
’a πŸŒ™πŸ•ŠοΈπŸ“ΏπŸ‡³πŸ‡¬

02/09/2025

_β€œRayuwa ba ta tsaya ga wanda ya ci nasara ba kawai, har da wanda bai daina Ζ™oΖ™ari ba duk da shan kaye.”_

🀲🏼 Ya Allah! Ka sa mu kasance daga cikin waΙ—anda s**a san darajar rayuwa, s**a san al’umma, s**a san Addini, kuma s**a tsaya tsayin daka wajen kare gaskiya da neman zaman lafiya a duniya baki Ι—aya.

πŸ’­ Kada zuciyarka ta mutu saboda kalaman mutane. Ka tsaya da gaskiya, ka Ζ™arfafa zuciya. Ranar mu tazo.

β€” *Ibrahim Musa Dan Hijira | BAGA GIDA*














πŸŒŸπŸ•ŠοΈπŸ“ΏπŸ“–πŸ’ͺπŸ½πŸ•ŒπŸ“’πŸ«±πŸΌ

---

02/09/2025

*πŸ•ŠοΈ *BARKA DA SAFIYA* πŸ•ŠοΈ*

*β€œGaskiya tana da nauyi, amma tana kawo nutsuwa. Addini shine mafita, ka kasance mai tausayi, ka yawaita addu'a, ka zama mai jawo zaman lafiya.”*

Ya Allah! Ka kawo mana zaman lafiya a Arewa da Tafkin Chadi, da Duniya baki Ι—aya. 🀲🏽

**✍🏽 Ibrahim Musa Ladan
πŸ“ Baga Gida**

β˜€οΈ
πŸ•ŠοΈ
πŸ™πŸ½

01/09/2025

Wannan shine mu'ujizar Allah cikin Al-Qur’ani Mai girma! πŸ“–πŸŒŠ*

*"Marajal baharaini yaltaqiyan – Bainahuma barzakhun la yabghiyan."*
*(Suratul Rahman: Ayoyi 19-20)*

*Ma’ana:* Allah Ya bar ruwan teku biyu su hadu, amma akwai shinge tsakaninsu – *ba sa cakudewa!*
Subhanallah! Wannan karara ne ga ikon Allah da basirarsa wajen tsara halittunsa ba tare da kuskure ba. 😲✨

Duk mai kaunar Allah yace: *"Allahu Akbar!"* πŸ™Œ
*Ni kuma nace: ALLAHU AKBAR!*

πŸ“ *Nasiha:* Kada mu daina nazarin Al-Qur'ani da tunani akan ayoyin Allah – akwai ilimi, hujja da tsarkaka a cikinsa. πŸ•‹πŸ’‘

πŸ“’ *Kayi sharing domin wasu su amfana – Al’ummar Manzon Allah ο·Ί suna bukatar tunatarwa.*

*Daga:* *Ibrahim Musa (Dan Hijira)*
*Haifaffen Baga, mazaunin Taraba State* 🏑

---

* *

πŸŒŠπŸ“–βœ¨πŸ•‹πŸ’šπŸ™ŒπŸ€²πŸ•Œ

01/09/2025

DAREN JIYA WATA YA YI RASHIN LAFIYA 🌘, amma komai ya dai-daita πŸŒ“.*

*Ya Allah!* Kamar yadda kake juyar da wata daga cikakke zuwa kankarewa, sannan ka dawo da shi sabo da haske πŸŒ•βœ¨,
ka juyar da *damuwarmu zuwa farin ciki*, ka cika *rayuwarmu da alheri, salama da rahamarKa* a kowane lokaci. Amin πŸ€²πŸ»πŸ’«

*Rayuwa juyi ce, kuma komai zai canza da izininKa, Ya Rabb.* πŸ•ŠοΈ

*Daga:* *Ibrahim Musa (Dan Hijira)*
Haifaffen Baga – Mazaunin Taraba 🏑

* *

πŸŒ™πŸ•‹βœ¨πŸ’šπŸ€²πŸ»πŸ“ΏπŸ•ŠοΈ

01/09/2025

*πŸŒžπŸ•Œ BARKA DA SAFIYA!*
Assalamu Alaikum warahmatullah!

Ina taya *β€˜yan uwa Musulmai* na duniya da *masu bin akidar Ahlulbayt (as)* murnar wannan safiya mai albarka, musamman a cikin wannan lokaci mai tarin daraja na zagayowar ranar haihuwar *Sayyidil Khalqi Muhammadu (SAW)* – wanda yafi kowa daraja da falala a dukkan halittu. πŸŒΉπŸ•ŠοΈ

*Ya Allah! Ka cigaba da tsare mana Al’ummar Manzonka (SAW), ka ba mu zaman lafiya, ka albarkaci masoyansa, iyalan gidansa masu tsarki da duk wanda ke biyayya gare su cikin gaskiya.*

Ina miΖ™a gaisuwa ta girmamawa ga *dukkan Masoyan Manzon Allah (SAW)* da suke cikin Ζ™auna da biyayya. Allah ya Ζ™arfafa mu a wannan hanya mai albarka, ya haΙ—a mu da su a duniya da lahira. πŸ€²πŸ½πŸŒ™

**Daga Ibrahim Musa (Dan Hijira)
Haifaffen Baga – Mazaunin Taraba State** πŸ’š

* *

πŸ•ŒπŸŒΉπŸ•ŠοΈπŸ’šπŸ•‹πŸ€²πŸ½πŸ“Ώβœ¨

28/08/2025
28/08/2025

🚨🚨 TRENT ALEXANDER-ARNOLD WILL FACE LIVERPOOL AT ANFIELD! 🀯

21/08/2025

🦁 *Zaki*, sarkin daji, ya tara dabbobi yana yanke sabbin dokoki:
β€œDuk dabbar da bata da hankali, za a fitar da ita daga daji!” πŸ˜€πŸ‘‘πŸŒ³

🐺 *Kura* ta tashi da sauri ta ce:
β€œRanka ya daΙ—e, don Allah ka bar ni, bana da hankali sosai, amma ina da azanci! Na fi jaki a hankali!" πŸ™πŸ˜‚

🐴 Sai *jaki* ya ce:
"To ai wannan dokar nawa ce! Ni tun tuni ban da hankali, kuma ko da na da shi, ba zan yi amfani da shi ba!" πŸ˜…πŸ€£

🦁 Zaki ya yi dariya sosai ya ce:
β€œWannan kuwa gaskiya ne. Kura da jaki ku zauna, amma sai kun rika kawo dariya a kowane mako!” πŸ˜‚πŸ¦

Haka aka bar *kura* da *jaki* cikin daji, saboda dariyarsu na sa ko zaki yana jin daΙ—i! 🀣🌿

---

*✍️: Dan Baga Town*
Mai son barkwanci da nishadi daga yankin masoya dariya! πŸ˜„πŸ™Œ

---

** 🐾
πŸ˜‚
🀣
πŸ€”
πŸ˜†
🦁
😜
πŸ’―
πŸ˜„
🌟**

---

21/08/2025

Ka tashi ka nemi na kanka, Kabar batun dangi da abokai.

WaΙ—an nan sunfi bada gudunmuwa alokacin jana'iza Ɗan Uwa !!!

Want your business to be the top-listed Photography Service in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

BAGA WARDS
Maiduguri