DanMasani RADIO
DANMASANI ONLINE GLOBAL RADIO. MUN SHIRYA TSAF DOMIN FADAKARWA, ILIMANTARWA DA KUMA NISHADANTARWA.
15/09/2026
Bai Kamata Rikicin Ƙasashen Waje Ya Zama Hujja Na Ƙara Ƙuɗin Man Fetur A Nijeriya Ba, Inji Atiku Abubakar
15/09/2026
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya dawo Nijeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Taron Shugabannin Ƙasashen BRICS karo na 18 da aka gudanar a New Delhi, a ƙasar Indiya.
CIKAKEN SHIRIN:
GWAJE-GWAJEN DA YA KAMATA MA’AURATA SU SANI KAFIN AURE DA KUMA BAYAN AURE!
14/09/2026
Ba Na Son Wa'azin Sheik Albany Da Sheik Idris Dutsen Tanshi Saboda Babu Tarbiyyar Musulunci A Ciki, Cewar Sheikh Ahmad Gumi
GWAJE-GWAJEN DA YA KAMATA MA’AURATA SU SANI KAFIN AURE DA KUMA BAYAN AURE!
Cikakken Shirin yana nan a You tube 👇👇👇
https://youtu.be/2oXnqc8DApQ
14/09/2026
Nawa Ne Farashin Litar Man Fetur A Yankunanku A Yanzu Haka?
14/09/2026
Da ɗumi-ɗumi: Na hannun damar El rufa'i sun Fice daga jam’iyyar ADC sun koma goyon bayan El rufa'i
Wasu fitattun jiga-jigan siyasa da aka sani a matsayin na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun koma jam'iyyar APC tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Uba Sani.
Daga cikin waɗanda aka ruwaito sun koma sansanin siyasar Uba Sani akwai Bashir Saidu, tsohon Chief of Staff na gwamnatin El-Rufai, da Sanata Abdu Kwari, tsohon kwamishina a Jihar Kaduna kuma tsohon Sanata da jafaru Sani
Sauran sun haɗa da Nasir Abdullahi Maikano, tsohon shugaban jam'iyyar SDP a Jihar Kaduna, kuma tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna na wa'adi uku da ya wakilci mazabar Ungwan Sanusi.
Rahotanni sun ce jiga-jigan sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne domin haɗa kan jam'iyyar da kuma marawa gwamnatin Uba Sani baya wajen ci gaba da ayyukan raya Jihar Kaduna.
Wannan sauyin siyasa na zuwa ne yayin da siyasar Kaduna ke ƙara ɗaukar sabon salo gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda APC ke ci gaba da ƙarfafa matsayinta a jihar.
14/09/2026
Naira biliyan 18 na bashin Nigeria Airways: NUP ta yaba wa Tinubu, ta sake neman rage radadin tallafin man fetur
Ƙungiyar ma’aikatan Najeriya (NUP) ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan biyan Naira biliyan 18 na bashin tsohuwar kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways.
Sai dai ƙungiyar ta sake yin kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan rage wa ƴan Najeriya radadin tsadar rayuwa, musamman ta hanyar samar da tallafin man fetur.
14/09/2026
Sarkin Musulmi ya bukaci ’yan Najeriya su tantance alkawuran ’yan siyasa kafin zaben 2027
Daga, Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammadu Sa’ad Abubakar CFR mni , ya yi kira ga ’yan Najeriya da su duba tare da tantance alkawuran da ’yan siyasa ke yi kafin su yanke shawarar wanda za su ba kuri’unsu a babban zaben 2027.
Sultan ya jaddada muhimmancin yin la’akari da sahihancin alkawuran ’yan siyasa da kuma irin abubuwan da za su iya kawo ci gaba ga al’umma, maimakon yanke hukunci bisa ga kalamai ko alkawuran yakin neman zabe kawai.
Ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu lura da harkokin siyasa tare da amfani da kuri’arsu cikin hikima da sanin makamar zabe.
Mai alfarma Sarkin Musulmj ya fadi haka ne a Lokacin da Shugaban Kwamitin Neman Zaben Tinubu ya ziyarci shi a fadarsa dake sokoto.
14/09/2026
RAHOTO: Obasanjo: Najeriya ba ta da dalilin zama cikin talauci
Farida Abdullahi Zarma Ayau News
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya ba ta da dalilin zama cikin talauci, saboda tana da albarkatun ƙasa, damarmakin noma da ƙwararrun mutane masu yawa.
Obasanjo ya ce ƙasar na da filayen noma, yanayi mai kyau da ruwa da za su iya samar da isasshen abinci tare da bunƙasa fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje.
Ya kuma ce Najeriya na da ma’adinai, ɗanyen mai da iskar gas, baya ga ƙwararrun ‘yan Najeriya a gida da ƙasashen waje. Ya ce amfani da waɗannan albarkatu yadda ya kamata zai taimaka wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi.
ME ZAKU CE???
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina
820221