Aerial FLASH Updates
Hausa/ English
Aerial Flash kafar isar da labarai ta kafafen sada zumunta ce da zata rinka kawo muku labarai da dumi-duminsu masu tasiri ga cigaban rayuwa da zamantakewar al'umma tare da raya al'adu da ci gaban tattalin arzikin kasa a dukkan fannoni.
17/02/2026
Sama da masu karamin karfi dari biyu ne s**a karbi tallafin kayan abinci daga wakilan al`umomin Sinawa mazauna Kano dake arewacin Najeriya albarkacin shigowar watan Azumin Ramadana wanda ya fara daga yau laraba 18 ga wata.
Kayan abincin sun kunshi Shinkafa da kuma Talilya, kuma an rabar da kayan ne a harabar gidan abincin Sinawa na Red China Restuarant a unguwar Nasarawa GRA dake birnin Kano.
A lokacin da yake rabar da kayan, mamallakin gidan abincin Mr Lok yace a duk lokacin irin wannan na shigowar watan Azumi akan bayar da wannan tallafi ga mabukata karkashin kulawar sa domin dai saukaka rayuwar mutanen da suke da karancin samu.
Yace hakika akwai magidanta da suke cikin matsanancin hali na rashin wadatar abinci tare da iyalan su, wannan ya basu kwarin gwiwar kirkiro da shirin tallafin abincin wanda ake gudanarwa tun sama da shekaru 5 da s**a gabata.
Mr Lok ya cigaba da bayanin cewa watan azumin na bana yazo dai dai da lokacin da al`ummar Sinawa a Kano dana sauran sassan duniya ke bukukuwan bikin sabuwar shekarar gargajiya, inda yace yana daga cikin al`adar bikin taimako da tausayin juna, a don haka wannan tallafin kayan abinci da aka bayar wani bangare na bukukuwan sabuwar shekarar tare da maraba da wata mai alfarma a Ramadan.
17/02/2026
Al`ummar Sinawa mazauna Kano sun gudanar da liyafar murnar shigowar sabuwar shekarar gargajiya kasar Sin.
`Yan kasuwa Sinawa mazauna birnin Kano a arewacin Najeriya sun bi sahun sauran Sinawa na duniya wajen gudanar da shagalin bikin murnar shigowar sabuwar sharkarar gargajiya ta kasar Sin da ake yiwa lakabi da shekarar Doki.
Sinawan sun taru ne a daren jiya litinin jajiberin bikin na bana a gidan abincin Red China dake rukunin gidajen Nasarawa G R A a birnin Kano, inda aka ci, aka sha tare da musayar sakonnin fatan alheri ga junan su.
A lokacin da take jawabi yayi bikin, Mr Jiang Jum `yar kasuwa data fito daga lardin Guandong wadda kuma take harkokin ta a jihar Kano ta bayyana bikin na bana a matsayin na daban wanda yazo da abubuwa da dama na alheri da zai amfani kasar Sin da sauran sassan duniya.
Ta bayyana liyafar cin abinci da aka shirya dacewa wata hanya ce mai fa`idar gaske da zata kara hada kan Sinawa dake zaune a jihar Kano tare da tunatar da juna tasirin al`adun kasar Sin a zamantakewar dan adam, sannan kuma liyafar ta kasance mahada ta kara sanin juna.
“Bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin biki ne da yake da mutukar mahimmanci ga kowanne dan kasar China akan hake ne a kowacce shekara ake gudanar da bikin sheda wannan rana”
Mrs Jiang Jum ta cigaba dacewa baya ga liyafar cin abincin daren da aka shirya a jiya litinin, a yau kuma talata ranar da shekarar ta fara mu Sinawa dake nan Kano zamu gayyaci sauran abokannan mu `yan Najeriya zuwa gisajen mu domin yin wata liyafar duk dai domin nuna farin cikin mu da shigowar wannan sabuwar shekara.(Garba Abdullahi Bagwai)
02/02/2026
Gwamnan jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Umar Namadi ya yabawa rundunar sojin kasar bisa irin kokarin da take kanyi wajen shawo kan mastalolin tsaro tare da tabbatar da doka da oda a jihar bakin daya.
Gwamnan yayi wannan yabon ne yayin bikin wasannin gargajiya na shekara ta 2026 wanda sojoji s**a sabayi a duk shekara, wanda kuma aka gudanar a harabar barikin rundunar dake Yagaba a birnin Dutse.
Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan wanda aka rabawa manema labarai ranar litinin 2 ga watan janairu a birnin Dutse, gwamnan jihar ta Jigawa yace hakika rawar da dakarun soji s**a taka wajen shawo kan matsalolin satar shanu da garkuwa da mutane da rigingimu tsakanin makiyaya da manoma a jihar abun a yaba ne mutuka. . .
02/02/2026
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani shiri na tsawon shekaru 10 da za a kashe dalar Amurka miliyan 250 domin farfado da hanyoyin dogaro da kai da kyautata tattalin arzikin al`umomin da sauye- sauyen yanayi ya tilasta kauracewa muhallan su.
A lokacin da yake jawabi yayin bikin kaddamar da shirin a ranar alhamis 29 ga watan janairu a birnin Abuja, sakataren gwamnatin tarayya Mr George Akume, yace take shirin dai shine karfafa hanyoyin rayuwa da zasu iya jure sauyin yanayi ga mutanen da aka raba da muhallan su .
Sakataren gwamantin tarayyar ya bayyana shirin a matsayin matakin gusawa daga tsarin ayyukan jin kai na gajeren zango zuwa tsari mai nisan zango da zai fifikon bukatun al`umma kai tsaye da nufin samar da damarmakin da zasu tabbatar da dorewar ingantacciyar rayuwa ga al`umma.
Mr Geoge Akume haka kuma ya cigaba dacewa shirin zai mayar da hankalin sa sosai wajen bullo da wasu damarmakin na daban a fannin tattalin arziki, da tsarin noma dake iya jure kowanne irin yanayi, kasuwancin kayayyakin makamashin da ake sabuntawa, samar da ayyukan yi a bangaren fasahar dijital wanda duka wadannan fannoni mata da matasa ne zasu fi cin gajiya. .
01/02/2026
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa wajen tabbatuwar tsarin kalandar karatu a jami`oi da kyautata walwalar malamai da kuma samar da ingantaccen tsarin wutar lanraki a daukacin jami oin kasar.
Shugaban ya tabbatar da hakan ne ranar asabar 31 ga watan janairu yayin bikin yaye dalibai karo na 45 na jami`ar Ahmadu Bello dake Zaria, yace baya fatan nan gaba a sake lalata tsarin kalandar karatu a harabobin jami`oin dake fadin kasar .
Shugaban na tarayyar Najeeiya wanda ya sami wakilcin karamar minista a ma`aikatar ilimi Farfesa Suwaiba Sa`id Ahmad tace batun ilimi jami`oi yana daya daga cikin batutuwan da gwamnati ke baiwa fifiko.
Shugaban a ta bakin ministar, gwamnati ta bullo da tsarin bayar da rance ga malamai da kuma sauran ma`aikatan da ba a bangaren koyarwa suke ba a jami`oi da sauran manyan makarantun kasar duk dai domin tallafawa rayuwa da kuma kyautata kwazon su ta yadda zasu mayar da hankali wajen koyar da dalibai da sauran harkokin su na bincike. .
01/02/2026
Taron masu ruwa da tsaki kan bunkasa shiyar arewa maso yammacin Najeriya yayi kira ga ma`aikatar bunkasa shiyoyi ta kasa data himmatu wajen aiwatar da tsare tsaren ta na cigaba a shiyar domin amfanuwar al`umma.
A jawabin sa yayin bude taron wanda aka shirya bisa hadin gwiwa da majalissar dattawa da ta wakilai da kuma hukumar raya shiyar arewa maso yamma ranar asabar 31 ga watan janairu a a garin Kaduna, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani yakawo shawarar cewa kamata yayi irin wannan babban taro ya rinka mayar da hankali wajen warware matsalolin da shiyyar ke fuskanta, bisa la`akarin da yadda shiyyar ke cigaba da samun koma baya duk da dinbun arzikin da take dashi.
Gwamnan jihar ta Kaduna yace shiyyar arewa maso yamma na da damar iya kasancewa babbar cibiyar noma da sarrafa kayan amfanin gona da hada- hadar kasuwanci sannan kuma zata iya kasancewa shiyyar da ake kyankyasar kwararru a fannoni daban daban .
Haka kuma gwamnan jihar ta Kaduna ya kawo shwarar cewa akwai mutukar bukatar a gaggauta zakulo bangarorin da ake bukatar yin hadin gwiwa ta hanyar tantance rawar da gwamnatin tarayya zata taka da wanda hukumar raya shiyyar zata taka da kuma bangaren da jahohin zasu iya bayar da gudumuwa. .
30/01/2026
Gwamnatin jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da wasu kamfanoni guda biya domin kafa masana`antar samar da farantar wutar sola wato mai amfani da hasken rana a jihar.
A kulla yarjejeniyar ce ranar juma`a 30 ga wata a birnin Dutse karkashin kulawar gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi da sauran yan majalissar zartarwar jihar da kuma wakilan kamfanin Leda Green power dake birnin Beijing da kuma Tesni Energy dake Najeriya
Dayake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, gwamnan jihar ta Jigawa yace aikin yana daga cikin mahimmin matakai da gwamnatin jihar ke dauka na kawo cigaban jihar a tsari mai nisan zango, inda yayi bayanin cewa tabbas kamfanin sarrafa farantan wutar solar zai taimaka sosai ta fuskar kasuwanci da kuma sauran bukatun jihar a bangaren samar da makamashi mai tsafta da ake sabuntawa a duk fadin jihar.
“Kafa wannan masana`antar samar da farantar wutar solar tasirin sa bai tsaya kawai ga harkar kasuwanci ba kadai, zai kasance kuma hanya da zata kai ga cimma muradun gwamnatin jihar na assasa tashar samar da wutar sola mai karfin megawtt 100 a jihar Jigawa”. . .
29/01/2026
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata kashim Shettima yayi kira ga al`umma dasu rungumi akidar zaman lafiya da kaunar juna a dukkan lamuran su , inda yace hadin kan kasa shine garkuwa ga duk wani abu daka iya zama barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalliya.
A cikin wata sanarwa daya rabawa nanema labarai ranar alhamis 29 ga wata, mashawarcin mataimakin shugaban kasar kan sha`anin kafofin yada labarai Stanley Nkwocha yace Sanata Kashim Shettima ya bukaci hakan ne da yammacin ranar larabar data gabata a fadar Gbong Gwom na Jos kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Mr Jacob Gyang Buba a karshen ziyarar daya kai jihar.
Mataimakin shugaban kasar ya cigaba dacewa Najeriya zata iya zama daya daga cikin manyan kasashen duniya muddin dai al`ummar kasar su fahimci mahimmancin zaman lafiya da juna.
Yace dukkan `yan Najeriya `yan uwan juna ne kamar dai yadda bincike ya tabbatar, a don haka abun daya hadu mu wuri guda ya zartar duk wani abu da ke hasashen zai kawo rarrabuwar kawunan mu. . .
27/01/2026
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya jagoranci bikin kaddamar da aikin ginin tashar mota ta zamani mafi girma a Najeriya a yankin karamar hukumar Chikun.
Wata sanarwa da darkatan yada labaran gwamnan ya rabawa manema labarai ranar talata 27, yace tashar mota zata dauki samada motocin bus dubu 5 a lokacin guda masu sintirin fasinjojin zuwa jahohi daban daban.
Sanarwa ta ambato gwamnan na jihar Kaduna yana bayanin cewa za a gudanar da akin ginin tashar ne a fili mai fadin murabba`in hecta 20 kuma a tsara samar da na`urorin zamani da zasu kula da harkokin tsaro da daidaita tsarin cunkoson motoci a tashar.
Ha`ila yau an tanadi na`urorin fasaha da zasu taimakawa tsoffi da kuma mutane masu lalura ta musamman wajen hawa da sauka a tashar, sannan kuma an samar da tasoshin mai fetur da man gas da kuma iskar gas domin dai amfanin motocin da zasu kasance a sabuwar tashar da za a gina. . .
26/01/2026
Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton binciken da ta kammala kan wasu jami’anta da su yi yunƙurin yi masa juyin mulki.
Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta miƙa rahoton ne wata biyu bayan tsare wasu hafsoshin soji 16, da ake zargi da yunƙurin juyin mulki ga Shugaba Tinubu, ciki har da wani mai muƙamin Birgediya-Janar.
Wasu manyan hafsoshin soji masu kusanci da binciken sun shaida wa wakilinmu cewa, sakamakon binciken ya samu sojojin da ake zargi da laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnati, kamar yadda aka tuhume su.
Duk dai hukuncin da Shugaban Ƙasa ya yanke kan sakamakon binciken, da shi za ɗauki mataki na gaba. Waɗanda aka dora wa alhakin gudanar da binciken sun kammala aikinsu, sun miƙa wa shugaban ƙasa rahoto.” .
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
700101
Opening Hours
| Monday | 07:00 - 23:00 |
| Tuesday | 07:00 - 23:00 |
| Wednesday | 07:00 - 23:00 |
| Thursday | 07:00 - 23:00 |
| Friday | 07:00 - 23:00 |
| Saturday | 00:00 - 01:00 |
| Sunday | 00:00 - 22:15 |