Muhammad kauji

Muhammad kauji

Share

whenever news of my death reaches you, please forgive me and pray for me 🙏

11/06/2026

Yanzu fa wallahi mata sunfi maza son mata

07/05/2026

Nasota daga Zuciya
Nasota daga gaskiya har cikin zuciyata. Sai da hartakai nake ji kamar zan iya yin komai akanta.

Ka san cewa ba ka shirya aure ba, amma ka zo ka saka yar mutane ta soka daga gaskiya, har ta kai tana jin kai kamar wani bangare ne na rayuwarta. Kuma daga ƙarshe ka gujeta. To wannan zalunci ne mai girma.

Hakika Allah ya sanya wa kowane ɗan adam feeling na emotion. Amma na wani yafi na wani ƙarfi.

Tsakanin maza da mata, ba za ka iya cewa su wa s**a fi ƙarfin emotion ba, saboda hakan yana da alaƙa da abin da ake so.

Amma abu a bayyane yake, mata sun fi maza rauni a wasu bangarori. Saboda mace idan tana sonka daga gaskiya, wani lokacin hankalinta gushewa yake yi, idonta ya rufe akan ka. Ta shirya tayi komai saboda kai, sai dai wacce Allah ya kare ta.

Wani lokacin ma har a cikin maza akan samu hakan, amma ba kasafai yake faruwa ba.

So da haka wani namiji zai yi anfani da irin soyayyar da mace take masa, ya kwashi romon dimokuraɗiyya, ya kara gaba, domin tun da ya gama da wannan tainuwar, sai ya koma wata sabuwar.

Musamman idan ya lura cewa tana son abin duniya da yawa. ( Kodayake waye baya son abin duniya? 😅 Ni kaina ina so Yasin 😂😂 )

But let’s be serious… wani namiji zai iya anfani da wannan damar. Amma wani lokacin nafi ganin laifin matan, saboda babu kazar da zata yi egg 🥚 without zakara.

Duk lokacin da k**e magana da shi, ki dinga lura da kalamansa da kuma body language dinsa. Idan kika ga wani sabon salo ko yanayin maganarsa yana neman shiga offside, sai ki gaya masa cewa hakan bai dace ba.

Amma wani lokacin yayin da namiji yake soyayya da mace, ba zai taba bayyana mata manufarsa ta fasikanci ba, har sai ya ga an bashi kofa. Ko da yar karama ce, dama abin da yake jira kenan, ya samu shiga yadi na 18. Koda bai yi scoring ba, ya samu yayi penalty. Dan yanzu ko Real Madrid ba kullum suke scoring da penalty ba.

Za ka ga wai a matsayin soyayya yake rike hannunta, yana shafawa, musamman idan tayi lalle a hannunta. Ita kuma muna-fuka, sai tayi shiru tana kallonsa. Shi kuma munafiki, lokacin da ya rike mata hannu shi kadai yasan yadda yake ji.

Wai duk a hakan soyayya ake, ta kasa gane cewa shi ɗin ɗa air ne. Karshe ma har pictures zata dauka ta saka a status tace: “With Habibi.” Kuma fa aunties za su ga status din, suyi liking, wani lokacin ma har da comment.

Wani lokacin ma haka namiji zai zo gidanku, kuna hira gaki gashi, amma sai yace miki:

“Baby yaushe zamu hadu?”

Kaji dan iska. A sati zai zo gidan ku sau uku ko sau hudu, amma kuma yana tambayar yarinya yaushe zasu hadu.

To dan ufanka, ko Real Madrid da Barcelona ma sau biyu suke haduwa a shekara a laliga 😭😂

Zai ce mata:
“Baby kishirya zamu je shan ice cream.”
Ke kuma kin yi karya a gida cewa Zainab ba ta jin dadi, za ki je ki duba ta.

Kin yi karya da sunan Zainab, to da farko dai Allah ya saka wa Zainab 😂

Kin fita babu kunya, kin bi shi kin tafi. To kanin ubanki ne da za ki bi haka?

Shi kuma alimiri ya gama aikinsa, ke yake jira. Sai daga baya idan an samu matsala, sai ace ya lalata mata rayuwa. Ai haka kaddararta tazo, ko Kuma haka Allah ya kaddara, ehhh munsan da kaddara, Amma meya tunda farko ba atuna Allah ba saiyanzu.

So hajiya/alaji, gaskiya daman can yar ku ita yar air ce. Domin wallahi duk macen da take soyayya da namiji, idan mutumin kirki ne zata sani. Idan kuma mutumin banza ne, shima zata sani.

Lokacin da yake siya mata abubuwa, yake kashe mata kudi, ba ku ce komai ba. Amma idan abin ya lalace sai ku fara magana. Idan ku iyaye ne na gaskiya, kamata yayi ko da data kawai kuka gani a wayar yar ku, ku tambayeta a ina ta samu.

Amma yanzu idan kana da kanne mata, ka fiye sa ido akan al’amuransu, sai ace kana takura musu. Kai waye ya takurawa rayuwarka?

Yo idan baka sawa kannenka mata ido ba, kafa ake so ka barsu?

Daga ƙarshe dai ina cewa Allah ya kare yan uwammu mata daga shiga sharrin samarin zamani. Mu ma Allah ya kare mu, ya kare imanimmu daga aikata alfasha da kannen wasu.

Muhammad kauji 🖋️

07/05/2026

Kai kasan cewa baka shiryama aure ba Kuma kazo kasa yar mutane ta soka, hartaji ka kaman wani bangare na rayuwar ta, Kuma daga Karshe kagujeta, to wannan zalinci Mai girma 💔🥲

17/04/2026
31/03/2026

Shiyasar Nigeria daban take da tako ina

16/03/2026

Tana neman shawarar ku, kubata sharawa.
Zan kashe aure na Malama miji na kullum 8k yake bani kudin cefane, Ni da yarana hudu nace ya kara yaki, Kibani sharawa yazanyi

07/02/2026

mutum 10 masu HIV su aje
opay din su a comment section

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano