Kano State Grass Root Mobilization Networ

Kano State Grass Root Mobilization Networ

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kano State Grass Root Mobilization Networ, Public Figure, Inuwa dutse Road, karkasara kano, Kano.

11/12/2025

Big shout out to my newest top fans! Yakub Aliyu welcome to our new members!

11/12/2025

Big shout out to my newest top fans! Yakub Aliyu

10/07/2025

Mutane wadannan yankuna da su ka hada da Titin zuwa Katsina, Kurna, Rijiyar Lemo, Bachirawa, Kwanar Ungoggo, Gobirawa da Miltara, suna ta murna sak**akon ware kudi Naira Bilayan 24 da motsi don fadada wannan t**i na Shatale-talen Baban Gwari zuwa Miltara, da Samar da gadojin ketarawa guda biyar a kan wannan Titin. Godiya ga Gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Photos from Kano State Grass Root Mobilization Networ's post 08/07/2025

Constitutional Review Committee

Komitin Tsarawa da Rubuta Matsayar Kano dangane da Sabunta Kundin Tsarin Mulki wanda Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Engr Abba K Yusuf ya ƙaddamar, ya gudanar da taronsa na farko a Ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Kano.

A cikin matakan da aka cimma, an tsara shirin sauraron ra’ayin jama’a ta kafafen rediyo domin bawa kowa damar faɗin albarkacin bakinsa.

Abubbuwan da akeson aji ra'ayoyin jama’a akansu sun haɗa da:

1. Local Government Autonomy
2. Creation of State Police
3. National Local Government Electoral Commission
4. State Creation
5. Role of Traditional Rulers
6. Resource Control

A ranar gobe Laraba, 9 ga Yuli, 2025, ku biyo waɗannan gidajen rediyo don bada gudunmawarku:

1. Express Radio (90.3) – 8:00 zuwa 9:00 na safe (Prof. Habu Muhammad Fagge)
2. Radio Kano (89.3) – 10:00 zuwa 12:00 na rana (Hon. Barr. Maliki Kuliya da Dr. Aminu Tukur Adam )
4. Freedom Radio (99.5) – 1:00 zuwa 2:00 na rana (Prof. Bello Ibrahim, Capt. Mansur Kurugu da Hon. Sa'adatu Tudun Wada, ALGON)
5. Tech FM (91.9) – 8:00 zuwa 9:00 na safe (Barr. Tahir Ibrahim Yakasai)

Haka kuma, a ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025, kwamitin zai kasance a Mumbayya House daga 10:00 na safe zuwa 2:00 na rana domin karɓar rubutacciyar gudunmawa (written or verbal contributions) daga ƙungiyoyi masu ruwa da tsaki ko jama’a.

Wannan dama ce ta jama’a don su bayyana muradunsu kan tsarin mulki mai (constitution review). Allah Ya sa sak**akon wannan aiki ya zamo alheri ga al’umma baki ɗaya, Amin.

Photos from Kano State Grass Root Mobilization Networ's post 08/07/2025

Gwamna Alh. Abba K Yusuf, ya karbi bakuncin tawagar 'yan majalisar wakilai ta tarayya, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, wadanda s**a zo Kano domin yiwa gwamnatin jihar kano ta'aziyya kan rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Talata, 8/7/2025
Hoto: Isah Muhammad Salisu

08/07/2025

Hukumar EFCC reshen Kano ta fara bincike kan wani mutum mai suna Ahmad Salisu da jami’an Kwastam s**a k**a a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da makudan kuɗaɗe da bai bayyana ba.

An k**a Salisu a ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025 yayin binciken kayayyaki inda aka gano yana ɓoye da kuɗaɗen har $420,900 da fam £5,825 da CFA 3,946,500 da kuma CFA 224,000 na Kamaru a cikin leda da kayan sawa.

Bayan k**a shi, Salisu ya ce yana ɗaukar kuɗin ne daga Auwal Ahmad da ke Saudiyya zuwa ga wasu mutum biyu Yusuf Adamu da Abdulhamid Rabiu da aka k**a su ma bayan sun zo karɓar kuɗin.

Kwastam ta mika waɗanda ake zargin da kuɗaɗen ga EFCC domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a kotu.

Shugaban EFCC na shiyyar Kano, Ibrahim Shazali, ya ce hukumar su da Kwastam ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaki da safarar haramtattun kuɗaɗe da aikata laifukan tattalin arziki.

Shima Kwanturolan Kwastam na Kano/Jigawa, Dalhatu Abubakar, ya jaddada cewa wajibi ne a bayyana kuɗaɗen da ake fita da su ƙasar waje domin dakile safarar kuɗaɗen miyagun ƙungiyoyi da ta’addanci.

~ Martaba Fm

08/07/2025

Alhamdulillah 🥰

Photos from Kano State Grass Root Mobilization Networ's post 18/06/2025

Muna yi wa mai girma gwamna kuma amiril hajjin bana daga jihar kano barka da sauka. Allah ya karbi ibada.

18/06/2025

Muna addu’ar Allah ya sauki mai girma gwamna lafiya. Ya kuma sa hajjinsa karbabbiya ce.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Inuwa Dutse Road, Karkasara Kano
Kano
0007

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00