Latest Post
Muna bayar da sahihan labarai da dumi-dumin sa.
24/03/2026
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rade-radin da ke cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya daina sanya jan hula, alamar tafiyar Kwankwasiyya.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wani umarni da aka bayar ga magoya baya su daina sanya jan hula ko fararen kaya da ke nuna tafiyar Kwankwasiyya.
Wata sabuwa!
22/03/2026
Sule Lamido ya musanta gayyatarsa APC, ya ce jita-jita ce
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta rahotannin da ke cewa an gayyace shi daga APC, yana mai cewa labarin jita-jita ne marar tushe.
Lamido, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a gidansa lokacin bikin Eid al-Fitr, inda ya ce bai san da wata gayyata daga Bola Ahmed Tinubu ko wani jigon APC ba.
Latest Post ta ruwaito cewa Lamido ya kuma karyata rade-radin da ke danganta shi da jam’iyyar ADC, yana mai danganta hakan da labaran bogi da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
’Yan bindiga sun sace masu ibada a cocin Kwara
22/03/2026
ADC ta fara sayar da fom din takara, ta sanya ranar ƙarshe 27 ga Maris
Jam’iyyar ADC ta sanar da fara sayar da fom din nuna sha’awa da na takara ga masu neman mukamai a matakin mazaba, kananan hukumomi, jiha da kuma babban taron kasa.
Sakataren tsare-tsare na kasa na jam’iyyar, Chinedu Idigo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daga hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya gayyaci dukkan mambobin da ke sha’awar tsayawa takara su sayi fom din kafin fara zabukan cikin gida.
Latest Post ta ruwaito cewa jam’iyyar ta kayyade farashin fom din nuna sha’awa kan N2,000, yayin da kudin takara ya bambanta da mukami, inda na shugabancin mazaba ya kai N10,000, na karamar hukuma N40,000
Saudiyya ta kori jami’an jakadancin Iran
22/03/2026
Yar gwagwarmaya Naja’atu tare da madugun Kwankwasiyya Kwankwaso
Me wannan ke nufi ga Kwankwasiyya?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Website
Address
Kano
700211