Zance da Zafin Rai
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zance da Zafin Rai, Blogger, Kano.
A nan, muna:
- Yin dariya da abin da ya k**ata ku yi kuka a kansa 😂
- Faɗin abin da sauran ke tsoran faɗi 💥
- Nuna wa masu "allura cikin buhu" cewa ana ganin su! 🧵👀
18/05/2026
KANAWA KU DAINA BA YAN DABA GOYAN BAYA
Fadan yan daba a jihar kano rainin wayo ce kawai. Siyasa a kasar nan ya bata komai. Gaunati sun mayar da komai ya zama siyasa. Karya ne ace wai yan daba sunfi karfin gaunati. Kawai dai gaunati suna anfani dasu ne domin cimma manufar su. Haba dan Allah! Shekara nawa ana abu daya. Me yasa gaunati bazata kafa doka mai tsanani akan yan daba ba? Idan da gaunati zasu kafa doka akan cewa duk wanda aka k**a shi da laifin daba, shekara ashirin zaiyi a gidan yari da yanzu an magance wannan matsalar. Gaskiya kanawa kuna bawa Arewa kunya. Allah ya sawwake
18/05/2026
Elrufai kenen, suna jin tsoron ka fiye da Allah alhali Allah shi ke komai, shi ya chanchanta a ji tsoron sa
Bubban kotu a Abuja ta bawa mallam Nasiru elrufai beli.
18/05/2026
Allah ya kara daukaka, ya kuma kare ke da sharrin mahassada yan Arewa
Iskanci a zuciyar mai yi yake, ba'a fina finai ba.
Aliyu dahiru Aliyu
Allah yace wanda ya ga dama yayi masa biyyayya wanda ya gadama ya kafirce masa amma wasu wai dole kowa sai ya zama ustaz. Yanzu akwai gidan karuwai a kano amma kowa ke zuwa? Akwai gidan giya kowa ke zuwa? Amma yan da da su baza su iya addini ba sai da bulala da bindiga da siyasa. A hana kaza, a hana kaza, komai a hana saboda ya tsabawa akidar su. Wannan ba musulunci bane, nuna isa ce kawai
Bafa Allah yayi Duniya bane domin ustazai kadai su rayu. Duniya na ustazai da yan iska ne
16/05/2026
Sanatan Borno ta tsakiya, Kaka Lawan, ya rabawa shugabannin jam’iyyar APC da ke mazabarsa kudi har Naira miliyan 135.6 domin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah
Amma fa, anya wannan kudin bana rabawa bane lokacin primary elections? Magudan kudi haka akan teburi, shi yasa kidnappers s**ayi yawa a kasa saboda yadda ake nuna kudi a zahiri. Allah ya kyauta
16/05/2026
Amma dai wannan abunda Hukumar Hisba takeyi ba da sunan addini suke yi bako? Saboda addini baice aje ana yawo ana bincike akan wadanda suke aikata zunubi a boye ba.
Babu yadda zaace mutanen sun killace kansu domin tsoron kunya kuma ace anje an kamo su wai suna aikata sabo. To idan ma sabo s**ayi ba Allah s**a tsabawa ba?
Yaushe tsabawa Allah ya zama tsabawa alummah? Gaskiya inda sunan addini suke yi to suji tsoron Allah su daina.
15/05/2026
Wannan gayan ya nuna capacity sosai kwanannan
15/05/2026
Governor yobe mai jiran Gado daga ADC
Mutane sai a kirkiro da kalma da babu maana a zahiri. Menene kabilanci a zahiri? A zahiri kowan yana san nasa kuma so halitta ce. Ta yaya annabi zai haramta son kabilar ka tunda ma ba hurumin bawa bane. So yanayi ne ba raayi ba. Abinda annabi ya haramta shine zalunci domin soyyayya wanda ake kiransa da kabilanci, amma kawai mutane domin hausawa suna son su kafa kungiyar hausawa domin kare hakkin Hausawa sai ace haramun ne domin kabilanci ne. Ai kabilanci kalma ce da take daukan zalunci to amma yaushe kafa kungiya domin kare hakkin bahaushe ya zama zalunci
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
700102