Zulfiqa Redio

Zulfiqa Redio

Share

Welcome to Zulfiqa Redio
Wannan Gidan Jaridar na Online ne

17/02/2026

Yanzu-Yanzu.

Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky(H). sun sanar gobe Laraba zai zama 1 ga Watan Ramadana.

Photos from Zulfiqa Redio's post 18/01/2026

Kisan uwa da 'yayanta a Kano: 'Yansanda sun k**a dan 'yar uwar marigayiyar da wasu mutane 2 da ake zargi da kisan

Rundunar ’Yansanda ta jihar Kano ta k**a mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar wata uwa da ’ya’yanta shida da aka yi a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi.

Kamen ya biyo bayan wani aiki na musamman bisa bayanan sirri, wanda aka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ’Yansanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawar kwamishinan ’Yansanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.

A cewar rundunar, an k**a wadanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar daga karfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa karfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.

Wadanda aka k**a sun hada da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu da aka fi sani da “Chebe”, mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi; da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi kira “Wawo”, mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharada.

’Yansanda sun bayyana cewa wanda ake zargin jagorantar kisan, Umar Auwalu, wanda dan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Haka k*ma, ya bayyana cewa sun aikata wasu kashe- kashe masu tada hankali a wasu sassan Kano a baya-bayan nan.

Daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin akwai tufafi masu tabon jini, wayoyin salula biyu na marigayiyar, adda, gora, kudi da ake zargin an kwace a wajen da abin ya faru, da wasu mak**ai masu hadari. Rundunar ta ce bincike na ci gaba.

Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta yaba wa jami’an da s**a gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da hadin kai. Rundunar ta k*ma tabbatar wa jama’a kudirinta na ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya.

04/09/2025

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Tsohon Gwamna El-Rufai Bisa Zargin Kalamai Masu Barazana

Kaduna, Najeriya – 4 ga Satumba, 2025
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta aike da takardar gayyata ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, *Malam Nasir Ahmad El-Rufai*, bisa zargin *kalamai masu tayar da hankali da barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

A cewar majiyoyi daga cikin rundunar, gayyatar na da nasaba da wasu kalamai da El-Rufai ya furta a cikin wani taron addini a baya-bayan nan, inda ake zargin cewa *jawabinsa na iya haddasa rikici da rarrabuwa tsakanin al’ummomin jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda, ya bayyana cewa an aike masa da gayyatar don ya bayyana gaban huk*mar domin karin bayani, ba wai an k**a shi ba.

> “Rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci kowanne irin yunkurin tayar da hankali ba, musamman daga manyan mutane da ke da tasiri cikin jama’a,” in ji jami’in hulɗa da jama’a.

Kawo yanzu, El-Rufai bai mayar da martani kai tsaye ba, sai dai wasu daga cikin magoya bayansa na cewa kalamansa an fassara su da wata manufa ta siyasa.

Zulfiqar Redio za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari domin kawo muku cikakken bayani yayin da abubuwa ke ƙaruwa.

---

**

Photos from Zulfiqa Redio's post 02/09/2025

RANAR MASOYA: SK PRESS TV Ta Shirya Bidiyo Na Musamman Don Tunawa Da Auren Sayyida Khadīja (AS) da Manzon Allah (S)

— Real ßàqír Yúsûf Adam

A ci gaba da bikin tunawa da ranar auren Sayyida Khadīja (AS) da Manzon Allah (S), Tashar SK PRESS TV ta gudanar da babban shiri na musamman da ya haɗa da ɗaukar bidiyo da waƙar soyayya mai ma’ana wacce ta janyo hankalin al’umma.

An shafe kwanaki biyu ana gudanar da wannan aiki a birnin Kano, inda wakilan tashar daga sassa daban-daban na ƙasar s**a hallara domin aiwatar da aikin tare.

Fitaccen mawaƙin Annabi da iyalansa, Sidi Uzairu Badamasi, shi ne ya rerawa wannan waƙa mai daɗin sauraro da cike da saƙonnin soyayya da ladabi.

A cewar wakilan tashar, an kammala aikin cikin nasara k*ma za a sako bidiyon a shafukan su na Facebook, YouTube, TikTok, da sauran hanyoyin sada zumunta.

Al’umma musamman matasa an gayyace su su nishadantu da zafafan hotuna da bidiyo da ke ɗauke da saƙo na tarihi da soyayya mai tsarki daga rayuwar Sayyida Khadīja (AS) da Manzon Allah (S).

ZULFIQAR REDIO
"Tsage gaskiya duk ɗacin ta."

Photos from Zulfiqa Redio's post 01/09/2025

RUNDUNAR YAN SANDAN JAHAR KATSINA TA CAF-KE MASU SADARAR MAKAMAI A JAHAR KATSINA.

— Real ßàqír Yúsûf Adam

An Cafke Mutane 2 Dauke da Bindiga da Harsasai Sama da 1,200 a Jihar Katsina

A ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025, jami’an tsaro sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da laifin mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, a yankin Ingawa, jihar Katsina.

Wadanda aka k**a sun hada da *Abdulsalam Muhammad*, mai shekaru 28, da *Aminu Mamman*, mai shekaru 23, dukkansu ‘yan asalin *garin Baure*, karamar huk*mar *Safana*, jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa an k**a mutanen ne dauke da *bindiga kirar mashin gun* da *harsasai 1,295*, a cikin wata *mota kirar Golf, mai launin shudi, lamba RSH 528 BV*.

Wannan samame ya faru ne a kan hanyar garin *Karkarku* da ke karamar huk*mar *Ingawa*, yayin da wadanda ake zargin ke kan hanyarsu daga *Hadejia*, jihar Jigawa zuwa *Katsina*.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa bincike ya na cigaba, k*ma za a gurfanar da su a gaban kuliya bayan kammala cikakken bincike.

A ƙarshe, huk*momi sun nemi goyon bayan jama’a da addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya da dakile aikata laifuka a yankin.

---

— Zulfiqar Redio Nigeria

29/08/2025

🗓️ ZULFIQAR Redio – Shekara 6 Tare da Ku! 🙏📻

Assalamu Alaik*m ƴan uwa da abokan Hulɗar mu na gaske!
A yau, muna murnar cikar shafinmu shekaru 6 da buɗewa. Wannan nasara ba za ta samu ba sai da gojon bayan ku – masu sauraro, masu bibiya, da masoya.

Mun gode ƙwarai!
Zulfiqar Redio ba kawai rediyo ba ne – gida ne na gaskiya, ilimi, nishadi da labarai masu amfani.

---

Mun koyi da ku, mun girma da ku, k*ma muna alfahari da ku!
Ga masu bibiyarmu tun daga farko har zuwa yanzu – kun zamo ginshiƙai a wannan tafiya.

---

✨ Idan kana sabon mai bi, to yanzu lokaci ne:

🔴 Bi shafinmu
📡 Saurari shirye-shiryenmu
🗣️ Raba da abokanka
📨 Aiko da ra’ayinka ko shawara

---

29/08/2025

Alhmadulillah Allah Celebrating my 6th year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

Photos from Zulfiqa Redio's post 29/08/2025

MAULIDIN MANZON ALLAH NA HALKAR NA'IBAWA.
Jiya da yamma 28/08/25, yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na Da'irar Kano da kewaye sun gabatar da Maulidin Manzon Allah na zaune. Jiya Alhamis shi ne rana ta biyu da fara Maulidin Halkoki na cikin Birnin Kano.
An gabatar da Maulidin ne a Halkar Imam Ali Amurulmunina wanda ya gudana a unguwar Sallari kusa da Makarantar Hassan Gwarzo.
An fara da budewa da addu'a sai k*ma karantun Kur'ani, daga nan k*ma aka karanto Ziyarar Manzon Allah daga nesa. Bayan nan an baiwa Mawakan Halkar Musulunci filin, Mawaka da yawa ne s**a baje kolin fasaharsu a cikinsu akwai Ammar dan Tinka daga Zariya da k*ma Sidi Uzairu Badamasi wadanda s**a baje kolinsu a wajen, yan uwa k*ma s**a gwangwajesu da Likin Kudi k**ar ba sa so.
Bayan nan an gabatar da Mai jawabi na musamman Dr Sunusi Abdulkadir Wakilin yan uwa na Da'irar Kano. Wanda ya yi jawabi akan Maulidi da wanda ake yiwa Maulidin Wato Manzon Allah. Ya fara cewa yanzu ba lokaci ne na kariya akan halascin Maulidi ba, ya ce an shige wajen da za a zo ana ta kare Maulidi ana cewa bidi'a ne ko ba Bidi'a bane. Dr Sunusi ya ce suma masu cewa Bidi'a ne akwai bidi'o'i da yawa da suke aikatawa idan ka tambayesu ba za su iya kare kansu su. Ya ce abin da s**a saba fada akan kare Bidia'rsu shi ne ai ba addini bane ba lada suke nema a wajen Allah. Nan ne ya karanto Ayar Kur'ani da take fadin cewa Rayuwa da Mutuwa da Sallah da Yanka dukkansu don Allah aye yinsu. Ya ce yanzu Mutum idan ya gidan Masallaci ya saka lasifik ya saka Carpet da Tiles sai a ce ba lada yake nema ba?
Bayan nan ya kawo Matsayin Manzon Allah a wajen Allah ta'ala daga cikin Kur'ani da Hadisai.
Bayan nan k*ma a karshe ya yi magana akan kokarin da ake da karfi da Yaji sai an abkar da Yaki a tsakanin Hausawa da Fulani. Ya bada misalai da Kasashen da aka abkar da irin wannan Yakin a tsakanin al'ummar da suke zaune lafiya. Ya k*m bayyana hanyoyin da ake bi wajen tabbatar da an abkar Yakin.
Dr Sunusi ya kawo misalin wani da ya fallasa tayin da aka yi masa na za a bashi Makudan Kudade da zai sayi gidan da za a dinga boye Mak**ai, ya kara da cewa akwai wasu Matasa da aka kai haramtaciyyar Kasar Isra'ila ana koya musu yadda za su yi amfani da mak**ai wajen karkashe Mutane.
Bayan ya kammala an gabatar da Jawabin gudumowar Ilimi daga bakin Wakilin Halkar Malam Hamza Muhammad Daurawa wanda ya ce bana Halkar zata samar da Kujerun Zama na Dalibai da na Malam a wani aji a Science Collage da ake ginawa a Rijiyar Lemo.
An raba kaya bukatun ga wasu yan uwa a Halkar Na'ibawa. Daga nan an raba Walima ga Mahalarta. A lokacin da ake raba kayayyakin k*ma a gefe daya wasu Matasa yan Daba suna ta fada da sare-saren Junansu. Amma dai ba su zo wajen da ake Maulidin ba, a tsakaninsu suke gwabzawa. Har aka gama lafiya babu wata Barazana ga yan uwa an kammala lafiya an k*ma koma gida lafiya duk da a gefe ana ta sare sare. Kowa da kiwon da ya karbeshi. Muna Maulidi wasu na kashe kawunansu.

Photos from Zulfiqa Redio's post 24/07/2025

📸Yadda Huda Abu Al-Naja ke kallon hoton ta kafin yunwa ta canza mata halitta 🥲

Kamar yadda kuke gani cikin hotuna wannan yarinya mai suna Huda Abu Al Naja mai kimanin shekaru 12 a duniya ke riƙe da hoton ta da aka ɗauka kafin Isra'ila ta jefa su cikin ƙangin azababbiyar yunwa.

Huda ƴar yankin Al-Mawasi ce dake Kudancin zirin Gaza, tana fama da matsananciyar yunwa wadda a yanzu ake tsammanin har ta kamu da cutar "Celiac disease".

Huda ɗaya ce daga cikin dubbunnan Palasdinawa da yunwa ta illata sak**akon toshe hanyoyin shiga da abinci zirin Gaza da Isra'ila ta yi.

Zulfiqar Redio - Daga Gaza

16/06/2025

Akwai yiwuwar Amurka zata shiga yaƙin a bayyane, ba ɓuya a bayan Muzra'ila ba k**ar yadda tayi tun farkon yaƙin. Saƙon Donald Trump a Twitter na neman mutanen Iran su bar Tehran ya nuna haka.

نصر من الله وفتح قريب.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Kano Kofar Waika
Kano
NAIBAWA