Hamza
Gaskia Jarin Dan Adam
12/05/2026
Eugene Daniel Bakar Fata Dan Shekaru 16 Da Aka Rataye Saboda Tsorata Yarinya Farar Fata 'Yar Shekara 16
A watan Satumba na shekarar 1921, a ƙaramin garin Pittsboro da ke gundumar Chatham cikin jihar North Carolina a kasar Amurka, Eugene Daniel, ɗan shekara 16, ya zama wanda aka zalunta, kuma ɗaya daga cikin munanan ayyukan cin zarafin bil'adama saboda bambancin launin fata na zamanin Jim Crow. Abin da ya fara k**ar wasa ya ƙare da wani babban bala'i.
Eugene Daniel wani yaro bakar fata ɗan shekara 16, wanda ke zaune tare da iyayensa a kusa da Pittsboro. A ranar 16 ga Satumba, 1921, mahaifinsa ya aike shi gidan maƙwabtansu, don ya aro masa igiya. Ya kwankwasa kofar gidan, amma shiru babu wanda ya amsa. Abinka da yaro sai ya jingina da ƙofar gidan, sai ƙofar ta buɗe, sai ya shiga ciki, yana Excuse me don ganin ko akwai wanda ke gidan.
Duk da yake babu wani abu da ya aikata, amma ƙaramar 'yar mai gidan Gertrude ta firgita, wacce ke barci a ɗakin kwananta lokacin da ya shiga gidan na ɗan lokaci. Cikin tsoro, ta fita daga ɗakin. Da ya fahimci yadda za a iya yiwa lamarin mummunar fahimta, Eugene ya gudu ya bar gidan cikin sauri ya koma gida.
Tsoron da yarinyar ta ji ya jawo hankalin manya a gidan cikin sauri, kuma a cikin yanayin wariyar launin fata na lokacin, an mayar da abinda ya faru mai tsanani fiye da yadda yake a zahiri. Mutane sun yaɗa labarin cewa wani matashi Baƙar fata ya shiga ɗakin kwanan wata yarinya farar fata, saboda tsauraran ƙa'idodi da rashin adalci na zamantakewa na Jim Crow South, an ɗauke shi a matsayin barazana duk da cewa bai yi wani laifi ba.
Washegari, 'yan sanda sun yi amfani da karnukan bin diddigin Daniel, s**a k**ashi su ka kai shi gidan yarin gundumar Chatham da ke Pittsboro. Maimakon kare shi ko binciken lamarin, yan sandan sun zama sababin abinda ya biyo baya.
A daren nan, wasu fararen fata kusan hamsin s**a taru a wajen gidan yarin, s**a k**a Daniel s**a tilasta masa shiga mota. Ƴan daban turawan sun yi tafiya mai nisa da shi daga gabashin garin zuwa wani yanki kusa da wata gada a tsohuwar hanyar Raleigh. A can, cikin duhun daren ranar 18 ga Satumba, gungun turawan su ka rataye Daniel da sarka kuma s**a rinka harbinsa akai-akai.
Gawar da aka rataye ta zama abin kallo ga al'ummar yankin. Mazauna yankin fararen fata sun ɗauke ta a matsayin abin jan hankali ga jama'a, ba tare da nuna girmamawa ga Daniel a matsayin ɗan adam ba. Mutane suna zuwa daga wurare daban-daban don kawai su ga gawarsa da aka rataye suyi dariya.
Zuwa ranar Litinin, 19 ga Satumba, 1921, kimanin mutane 1,000 ne s**a yi tattaki zuwa wurin don ganin gawarsa kafin a sauke ta. Maƙwabtan wajen da jami'an yankin duk sun halarci wajen, wanda ya nuna yadda ta'addancin launin fata ya zama ruwan dare a cikin al'umma.
Shekaru da yawa, labarin Eugene Daniel ya ɓace daga tunanin jama'a, an manta da shi kuma wasu ma ba su san da shi ba. Cikakkun bayanai game da mutuwarsa da tashin hankalin da ya sha sun ɓace, an binne shi a ƙarƙashin yin shiru da sakaci.
Sai a shekarar 2021, ƙarni ɗaya bayan mutuwarsa, aka dawo da labarinsa. A bikin cika shekaru 100 da kisan gillar, Hukumar Kwamishinoni ta Gundumar Chatham ta fitar da takardar neman afuwa a hukumance kan gazawar gwamnati na kare shi, da kuma yadda shugabannin yankin s**a bar kisan ba tare da an hukunta kowa ba. Jami'ai sun fahimci cewa jami'an tsaro a wancan lokacin sun gaza wajen tabbatar da adalci ko bin doka da oda.
Ƙungiyoyin al'umma, zuri'a, da shugabannin jama'a sun yi aiki don tunawa da Daniel da sauran waɗanda aka yi wa ta'addancin bambancin launin fata a gundumar Chatham. An sanya alamun tarihi, kuma an nuna ƙasa da aka tattara daga wurin da akai ma sa kisan gilla a cikin nunin kayan tarihi na gida a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin fahimtar wannan tarihi mai raɗaɗi.
11/05/2026
Joram van Klaveren Mai Sukar Addinin Musulunci A Da Amma Yanzu Ya Musulunta Ya Zama Mai Kare Shi
Joram van Klaveren tsohon ɗan siyasa ne na ƙasar Holland kuma memba na Jam'iyyar 'Gaba da Musulunci ta Geert Wilders (PVV), wanda ya musulunta a shekarar 2019 yayin da yake rubuta wani littafi da yayi niyyar s**ar addinin. Yanzu yana aiki don yaƙar tatsuniyoyi da ya taɓa yadawa a baya, bayan ya canza ra'ayinsa gaba ɗaya bayan ya yi bincike kan tauhidin Musulunci.
A tsakanin 2010 da 2014, Van Klaveren fitaccen memba ne na PVV, ya yi kira da a haramta Al-Qur'ani, a rufe masallatai, kuma ya taba bayyana Musulunci a matsayin " addinin ƙarya".
Yayin da yake rubuta wani littafi da nufin s**ar Musulunci, Van Klaveren ya bayyana cewa binciken da ya yi kan rubuce-rubucen tarihi, da imani da Allah a Musulunci, da tattaunawa da malamai ya sa ya rungumi addinin. Ya sanar da musuluntarsa a bainar jama'a a watan Fabrairun 2019.
Van Klaveren ya rubuta littafi game da musuluntarsa kuma yanzu ya mayar da hankali kan haɓaka fahimta da wargaza ra'ayoyin da ba su dace ba game da Musulunci.
Ya bayyana cewa matsayinsa na kin Musulunci a baya ya dogara ne akan bayanai marasa tushe, yana mai cewa, "yana daga cikin manufofin PVV na danganta duk wani mummunan abu da Musulunci ta kowace hanya.
Labarin tubansa an rubuta shi a cikin littafinsa De afvallige (The Renegade).
10/05/2026
Al-Nabigha
Al-Nābighah ( النابغة الذبياني ), wanda aka fi sani da Al-Nābighah al-Dhubiyānī ko Nābighah al-Dhubyānī, wani mawaƙi ne na Larabawa mai matuƙar muhimmanci wanda ya rayu tun da daɗewa, kafin addinin Musulunci ya fara. Sunansa na ainihi shine Ziyad ibn Muawiyah, kuma ya rayu daga kimanin 535 AD zuwa 604 AD. Sunan "Al-Nabigha" a zahiri yana nufin " hazaka " a cikin Larabci, wanda ke nuna yadda yake da hazaka!
Wanene Al-Nābighah?
Al-Nābighah yana ɗaya daga cikin manyan mawakan ƙarshe na lokacin kafin zuwan Musulunci. An san shi da ƙwarewa mai ban mamaki wajen iya magana. Kabilarsa, Banu Dhubyan, tana zaune a wani yanki mai nisa da birnin Makka mai tsarki.
Rayuwarsa da Tafiye-tafiyensa
Duk da cewa kabilarsa tana kusa da Makka, Al-Nābighah bai zauna a can ba sosai. Ya shafe mafi yawan lokacinsa yana tafiya yana zama a fadojin masu iko. Ya ziyarci fadojin a wurare k**ar Hirah da Ghassan. Waɗannan fadoji k**ar gidajen sarauta ne inda sarakuna da shugabanni suke zama. Mawaka k**ar Al-Nābighah s**an nishadantar da masu mulki da waƙoƙinsu.
Tafiyarsa zuwa Hirah da Ghassan
Al-Nābighah ya fara zama a Hirah tare da wani sarki mai suna Mundhir III. Bayan Mundhir III, ya zauna tare da wani sarki wanda ya karɓi mulki a shekara ta 562 AD.
Daga baya, ya yi tafiya zuwa fadar Ghassan. Amma daga ƙarshe ya koma Hirah don yi wa wani sarki mai suna Numan III hidima. Wani abu ya faru bayan ya yiwa Sarauniya waƙa, yasa dole ne ya bar Hirah da sauri. Ya gudu zuwa Ghassan don neman mafaka. A kusan shekara ta 600 AD, ya sami damar komawa Hirah. Lokacin da Numan III ya mutu kimanin shekaru biyar bayan haka, Al-Nābighah ya yanke shawarar komawa ya zauna tare da ƙabilarsa.
Waɗanne Irin Waƙoƙi Ya Rubuta?
Al-Nābighah ya rubuta nau'ikan waƙoƙi daban-daban. Yawancin waƙoƙinsa ko dai waƙoƙin yabo ne ko kuma na barkwanci.
1. Waƙoƙin farin ciki, da ke yabon wani ko wani abu, sau da yawa wani mai iko ko jarumi mai jarumtaka.
2. Waƙoƙin zambo, da ke yin ba'a ga wani ko wani abu, sau da yawa a kaikaice.
Waƙoƙinsa sau da yawa suna magana game da rashin jituwa da faɗa tsakanin sarakunan Hirah da Ghassan. Ya kuma rubuta game da rikicin da ke tsakanin ƙabilarsa, Banu Dhubyan, da wata ƙabila da ake kira Banu Abs.
Shahararrun Wakokin Mu'allaqat Masu Shahara
Ana ɗaukar Al-Nābighah a matsayin ɗaya daga cikin mawaƙa shida mafi muhimmanci tun kafin Musulunci. Waƙoƙinsu suna da matuƙar daraja har an tattara su tun da wuri. Ana ɗaukar waɗannan waƙoƙin a matsayin mafi kyawun misalan waƙoƙin Larabci. Wasu ma suna tunanin Al-Nābighah shine mafi mahimmanci daga cikin waɗannan mawaƙa shida.
Waɗannan mawaƙa sun rubuta wakoki masu tsayi da ban sha'awa. An san su da Muʿallaqat (معلقات). Kalmar "Muʿallaqat" tana nufin "Wadanda aka rataye." Saboda an ce an rataye waɗannan wakoki na musamman a bangon dakin Kaaba a Makka. An yi hakan ne don kowa ya yaba da karanta su.
Gadonsa da Ayyukansa da aka Tara
Duk da cewa ya rayu tun da daɗewa, an adana waƙoƙin Al-Nābighah a hankali kuma an yi nazari a kansu. Wilhelm Ahlwardt ne ya tattara waƙoƙinsa da aka tattara a cikin wani littafi mai suna Diwans of the Six Ancient Arabic Poets in London a shekarar 1870. H. Derenbourg shi ma ya buga waƙoƙinsa daban-daban a birnin Paris a shekarar 1869.
27/04/2026
Tarihin Sahabbai
Mus'ab bn Umayr (RTA). : مصعب بن عمير.
Muṣ'ab ibn ʽUmair (RTA) wanda aka fi sani da Mus'ab al-Khayr sahabi ne na Annabi Muhammad (SAW). Daga Banū ʽAbd al-Dār reshen kuraishawa, ya musulunta a shekara ta 614 miladiyya kuma shi ne jakadan Musulunci na farko. Ya rasu a yakin Uhudu a shekara ta 625 miladiyya. Yana da Shekaru 30. Mahaifinsa shi ne Umair bin Hashim, Mahaifiyarsa kuma ita ce Khunaas Bint Malik.
Ba a san ainihin tak**aiman shekarar haihuwarsa ba; ana kyautata zaton an haife shi ne a tsakanin shekara ta 594 zuwa 598 miladiyya, tun yana karami ya musulunta a shekara ta 614 Miladiyya, iyayensa sun kasance ma su arziki.
Musulmin farko, kafin Musulunci ya yi karfi, sun kasance suna ganawa da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam a gidan Al-Arqam da aka fi sani da Cibiyar Koyon Musulunci. Mus’ab ya yi sha’awa, ya ziyarci gidan domin neman karin bayani game da Musulunci. Sak**akon jin karatun Alkur'ani da wa'azin Annabi Muhammad Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.
Bayan ya musulunta da farko Mus'ab ya buye Imaninsa don yana tsoron ka da mahaifiyarsa ta sani" Sai dai wata rana wani dan kuraishawa mai adawa da Annabi, Uthman bn Talha, ya gan shi ya shiga gidan Al Arqam, yana shiga yayi salla tare da musulmi, sai labarin ya bazu, daga karshe dai labari ya isa wajen mahaifiyarsa, ta daure shi a gidansu da nufin ta sa shi ya ya koma Kafirci, Mus’ab ya kasance mai kwarin gwiwa a kan imaninsa, kuma ba zai barranta daga imani ba. Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya shawarce shi da ya shiga cikin sahabban don yin hijira zuwa kasar Abisiniya, don ka da a sake muzguna masa.
An nada Mus’ab bn Umayr a matsayin jakadan Musulunci na farko kuma an aika shi zuwa Yasriba (Madina) don shirya garin don Hijira. bayan mubaya’ar farko ta ansar (Mazauna Madina), wani mutumin Madina mai suna Asad bn Zurarah ya taimake shi. Bayan sun yi wa'azin Musulunci, mazauna Madina da yawa sun musulunta, ciki har da Sa'ad bn Mu'adh, da Usayd bn Hudayr da Sa'ad bn Ubadah (duka Allah ya kara musu yadda).
Yakin Badar.
Ya halarci yakin Badar tare da sojojin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda su ka hada da Sayyadina Ali (AS) Sayyida Hamza, (AS) sai Az-Zubair bn Al-'Awwam, (RTA) da Ammar bn Yasir, (RTA) da Abu Dharr al-Ghifari (RTA). Haka kuma musulmi sun taho da rakuma saba’in da dawakai biyu, ma’ana ko dai mafi yawansu sun yi tafiya a kasa ko kuma a sanya mutum uku zuwa hudu a kan kowane rakumi. Duk da haka, yawancin musulmi a lokacin basuyi tsammanin za a hwabza wani mummunan yaki ba.
Shahada A Yakin Uhudu
A yakin Uhud an gwabza a shekara ta 624 miladiyya, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya sanya Mus'ab bn Umayr ya dauki tutar musulmi.
A lokacin yakin, da wasu musulmi su ka ga amfara samun nasara akan kafirai, sai su ka bar kan dutsen da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama yayi musu umarni da su tsaya, ashe ba su sani ba Khalid Ibn Alwalid (sannan bai musulunta ba) yana bayan dutsen da shi da wasu dakaru, su na ganin haka sai su ka biyo ta bayan mummunai da sara, kafiran da a ka farawa rararakawa da su ka ga rundunar Khalid daga baya sai s**a juyo su ka sanya Musulmi a tsakiya su ka fara kisa har wasu dakarun kafirai s**a nufi inda Manzon Allah Sallallahu Alaihi yake domin su kai masa hari,
Da Mus'ab yaga haka ya fahimci hatsarin da ke tattare da hakan, sai ya daga tutarsa ya yi ta kabbara (ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR ) da nufin karkatar da hankalin makiya zuwa ga da kansa, don subar Annabi (SAW), cikin hakan a ka kai wa Mus'ab hari, aka yanke hannunsa na dama da ke rike da tuta, amma sai ya ci gaba da maimaita kalmar ALLAHU AKBAR, ya dauke tutar da hannun hagu. Lokacin da aka yanke hannunsa na hagu sai ya k**a ta da Kasangalalin hannayensa amma bai bari tutar ta fadi ba. "Daga karshe dai Ibn Kami’ah ya jefi Mus'ab fa Mashi ya yi shahada.
ALLAHU AKBAR.
Shidai mus'ab Ya taso a cikin jin dadi, gashi dan gata kuma kyakkyawa mai iya ado, dukkan wani taro baya cika idan babu Mus'ab a cikinsa. Yana cikin wannan hali ne ya sami labarin kiran musulunci ta bakin amintacce Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, bai yi jinkiri ba wajen amsa kiran duk da sanin irin matsin da zai fuskanta. Mus'ab ya hakura da dukkan jin dadin duniya, ya maye shi da dandanar kuda da azabtarwa daga mutanensa. Wata rana mus'ab ya taho gurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sahabbai sun kewaye shi, lokacin da s**a hango Mus'ab s**aga irin halin da ya shiga na kunci da takura sai s**a sunkuyar da kawunan su suna kuka saboda tausaya masa. A ranar yakin Badar shine yake rike da tutar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam babbar ta Muhajirun hak**a a yakin Uhudu inda a ranar yai shahada. An ruwaito Annabi sallallahu alaihi wasallam ya tsaya a gaban Mus'ab da sauran wanda s**ai shahada a Uhudu yana cewa: "Lallai zanyi muku shaida cewa ku shahidai ne a gurin Allah ranar Alkiyama"
27/04/2026
Tarihin Annabawa
Tarihin Annabi Ayyub (AS)
Annabi Ayyub (Ayyuba) zuriyar Annabi Ibrahim ne. Mahaifiyar Ayyub diya ce ga Annabi Ludu, kuma matarsa ta kasance zuriyar Annabi Yusuf kai tsaye. Ayyub ya zauna a Roma tare da masoyiyar matarsa Rahma da 'ya'ya goma sha hudu.
Ibn Ishaq yace Annabi Ayyub (Ayyuba) nasabarsa ita ce Ayyub Ibn Musa Ibn Razih Ibn 'Ees bn Ishaq Ibn Ibraheem (amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya).
Sai dai wasu sun ce nasabarsa ita ce Ayyub bn Musa bn Ra'ooeel bn Ees bn Ishaq bn Ya'qub (amincin Allah da amincin Allah su tabbata a gare su baki daya).
Don haka madaidaiciyar magana shi ne cewa ya fito daga zuriyar ‘Ees Ibn Ishaq Ibn Ibraheem (amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya). Dangane da sunan matarsa, an ce ita ce Leea bint Ya’qub (amincin Allah su tabbata a gare shi). Wasu kuma s**a ce sunanta Rahmah bint Ifratheem. Wasu kuma suna da'awar cewa ita ce Leea bint Mansa Ibn Ya'qoob (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Wannan shi ne ra'ayi mafi shahara. Allah Shi ne Masani.
Ayyub Annabi ne wanda Allah ya yi masa ni'ima mai yawa- yana da karfi da lafiya, yana da filaye masu yawa, da dabbobi masu yawan gaske, da iyali na kwarai kuma kyawawa; kana ya kasance shugaban al'umma wanda al'ummarsa ke matukar mutuntawa da kaunarsa.
Duk da matsayinsa da arzikinsa, Ayyub bai taba girman kai ba; ya kasance mai tawali’u a kodayaushe, ya kasance mai saurin taimakon wanda bashi da shi, kuma ya kasance yana gode wa Allah da tasbihi a kan duk abin da ya yi masa na albarka.
Ayuba ko Ayyub (da Larabci: اَیّوب ) Annabin Allah ne, ya sha fama da cututtuka da asarar 'ya'yansa da dukiyarsa. Ya kasance mai hakuri a lokacin jarrabawarsa, bai gushe ba yana yin ibada da godiya ga Allah.
Kur'ani bai ambaci cikakkun bayanai game da jarrabawar da akayiwa Annabi Ayuba ba, amma Littafin Bible da wasu hadisai na musulunci sun ruwaito cewa mutane sun fara nisantar da Ayuba (AS) saboda ciwonsa. Kur'ani bai ambaci komai game da hakan ba sai dai ya yaba masa don haƙurinsa.
A cewar malaman tafsirin, Ayuba (AS) ya yi rantsuwa cewa zai yi wa matarsa bulala dari amma daga baya ya yi nadamar yin irin wannan rantsuwa. Sai aka yi wahayi zuwa gare shi cewa ya buge ta Sau guda ɗaya da tarin Bulalai ɗari, ya kiyaye rantsuwarsa ta aiwatar da haka. Akwai sabani tsakanin masu tarihi kan dalilin rantsuwar Ayuba.
Babu tabbataccen bayani game da wurin da aka binne Ayuba (AS). Sai dai kuma akwai kaburbura da dama a kasashe daban-daban da ake danganta su gare shi, k**ar wani kabari kusa da Hillah a kasar Iraki
An ce Annabi nan aa aka ambata a cikin Al-Qur'ani Dhul-Kifl ɗan Ayuba (AS) ne, wanda sunan sa shi ne Bishr.
Ibn Jareer da waninsa sun ambaci cewa Ayyub (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rasu yana da shekara casa’in da uku. Wasu kuma s**a ce ya rayu fiye da haka.
Kafin ya rasu ya damka wa dansa Hawmal amanarsa dansa Bishr bayansa, Mutane da yawa suna cewa shi ne Zul Kifli, Allah ne Mafi sani. Su ma wadannan mutane suna da’awar cewa shi Annabi ne, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da biyar.
Ayyub (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rayu a kasar Rum tsawon shekaru saba'in bayan gama jiyarsa. Ya yi musu wa'azi da addini da tauhidin Ubangiji guda. Sai dai daga baya sun canza addinin Ibrahim (AS) bayan rasuwarsa.
Annabi Ayuba A Cikin Alkur'ani
Lalle Mũ, Mun yi wahayi zuwa gare ka, k**ar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũbu da zuriyyaraa da Isah da Ayuba da Yũnusa da Hãrũna da Sulaimãn kuma Mun bai wa Dãwũda littãfi. (Suratul Nisa'i aya ta 161-163).
Waɗanda s**a yi ĩmãni, kuma ba su gauraya imaninsu da zãlunci ba, waɗannan sune amintattu, kuma sũ, mãsu shiryuwa ne. Kuma waccan ita ce hujjarMu, Muka bai wa Ibrãhĩm a kan mutãnensa. Muna ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so. Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Masani. Kuma Muka bai wa Ibrãhĩm da Is'hãƙa da Yãƙũbu, dukansu Mun shiryar dasu. Kuma Nuhu, Mun shiryar da shi a gabaninsu. kuma a cikin zuriyarsa, Dauda da Sulemanu da Ayuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kamar haka Muke sãka wa mãsu da kyautatãwa (Suratul Anam Ayat 82-84).
Kuma (ka ambaci) Ayuba, a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, "Lalle ne, cũta ta shãfe ni, kuma Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama." Sai Muka karɓa masa, kuma Muka kuranye abin da ya sãme shi na cũta. Kuma Muka ba shi iyalansa da kwatankwacinsa tãre da su, dõmin rahama daga gare Mu, kuma da tunãtarwa ga mãsu bauta. (Suratul Anbiya aya ta 83-84).
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani ikon bayar da labarin sahihin Tarihin Annabi Ayuba mai daraja.
Click here to claim your Sponsored Listing.