TajTech
We empower people with modern digital skills needed for today’s world.
At TAJTECH, we provide professional computer training, internet services, and tech education to help students, graduates, and entrepreneurs succeed.
24/04/2026
Kafin Kasai ko wache kalar iphone yaka Mata kasan wannan
Idan kaje Siyan iphone musanman UK used zakaga sticker wadda a jiki an rubuta
DM ko DDM
Mutane dayawa suna tambata me wannan yake nufi
As a big guy yaka Mata ache kasan wannan Kar amai daka mage 🤗
Abunda wannan yake nufi shine aduk lukachin dakaje Siyan waya kaga anrubta DM
Wannan yana nufin (Display message) wannan yana nufin antaba chanzawa wannan Wayar wani part Wanda Kai bakasan ko menene ba
Shi DM yana nuna part daya aka chanza watu ko dai screen, camera ko Kuma battery Wanda sune dama important part da ake consider
Know this bro 😌
A dayan bangaren Kuma idan kaga an rubuta DDM yana nufin (Double Display Message)
Idan kaga wannan yana nufin ba part daya aka chanzaba anchanza part sama da daya
Zai iya zama battery da screen ko Kuma camera da screen ko wani Abu maka manchin haka
me yasa nake su kasan wannan shine
Mafi yawan masu saida waya bazasu fadama wannan ba they will assume kawai tunda gaka sticker to ya wadatar
Dan haka ni nake fadama
Yazakai kasan part da aka chanza akan iphone da kake mafarkin siya?
Yadda zakai kasan taka Mai man part da'aka chanza shine kaje setting
Kataba general
Kayi scrolling zuwa about
Taba inda akasa (part and service history)
Idan kaga
Display – An chanza screen
Battery – An chanza battery
Camera – An chanza camera
Face ID / TrueDepth camera – idan an taba gyra Face ID
Genuine Apple Part ✅ – Yana nuna company ne s**ai gyaran
Unknown Part ⚠️ – yana nufin iphone din bata iya recognizing na abunda aka gyra ba
A kullun Ina fada muku Siyan waya Mai display ba issues bane inda matsalar take a siyar ma da ita a matsayin non display ko Kuma ka Siya baka sani ba
To wannan shine
21/04/2026
Slimmer. Sleeker. Samsung. 🤌
Sabon 5G yana zuwa da ingantaccen ƙarfi da dogaro, tare da kyakkyawan zane na zamani, baturi mai ɗorewa, allo mai haske da cikakken bayani, da kuma mafi ƙarfi a cikin jerin A Series — domin ka tafi ko’ina cikin sauƙi.
21/04/2026
KAMFANIN META YA JANYE DAGA KENYA, INDA MA'AIKATA 1,108 SU KA RASA AYYUKANSU
Kamfanin Meta (mamallakin Facebook) ya kawo ƙarshen yarjejeniyar da yake da ita da kamfanin SAMA na ƙasar Kenya, wanda hakan ya yi sanadiyyar sallamar ma'aikata 1,108 a birnin Nairobi.
Wannan mataki ya biyo bayan kwashe shekaru ana fuskantar ƙalubale na shari'a, ɗabi'un aiki, da kuma matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa dake tattare da aikin tace bayanai wato (content moderation) da kamfanin Sama yake yi wa Meta a yankin kudu da hamadar Sahara.
Ma'aikatan da abin ya shafa su ne waɗanda ke kula da tantance hotuna da bidiyo da saƙonni dake yawo a Facebook da Instagram domin tabbatar da ba su saɓa wa ƙa'idojin kamfanin ba.
Wannan aiki ya haɗa da duba abubuwa masu tada hankali kamar kisan kai, tsiraici, da cin zarafi, wanda hakan ya janyo wa ma'aikata da dama matsalolin damuwa da firgici (trauma).
Tarihin Takaddamar:
Shari'a a Kotu: Kamfanin Meta da Sama sun sha fuskantar ƙararrakin shari'a a Kenya, inda tsofaffin ma'aikata s**a yi zargin ana nuna musu wariya, ana biyan su albashi mara kyau, kuma ba a kula da lafiyarsu bayan sun ga abubuwa masu tada hankali a aiki.
Janyewar Sama: Kafin Meta ta soke kwangilar, kamfanin Sama ya riga ya sanar da cewa zai daina aikin tace bayanai domin mayar da hankali kan wasu ayyukan na daban.
Wannan sallama ta raba mutane sama da dubu ɗaya da hanyar neman abincinsu a lokaci guda, wanda hakan babban koma-baya ne ga tattalin arzikin birnin Nairobi, musamman ga matasa masu fasaha dake aiki a kamfanonin waje.
Yayin da Meta take neman wasu hanyoyin na daban ko amfani da fasahar AI wajen tace bayanai, wannan lamari ya sake tayar da muhawara kan yadda manyan kamfanonin fasaha na duniya ke amfani da ma'aikata a ƙasashe masu tasowa da kuma irin kariya da ya kamata a ba su.
20/04/2026
SHUGABAN KAMFANIN APPLE, TIM COOK ZAI YI MURABUS DAGA MATSAYIN SHUGABA BAYAN SHEKARU 15
Babban labarin da ke girgiza duniyar fasaha a yau shi ne murabus ɗin da Tim Cook zai yi daga matsayin Shugaban Gudanarwa (CEO) na kamfanin Apple. A tsawon kusan shekaru 15 yana jan ragamar kamfanin, Cook ya samu nasarar mayar da Apple katafaren kamfani mai darajar biliyoyin daloli, tare da faɗaɗa nasarorin da wanda ya kafa kamfanin, Steve Jobs, ya bari.
Kamfanin ya sanar da cewa John Ternus, wanda a halin yanzu yake matsayin Babban Mataimakin Shugaba a fannin Injininiyan Na'urori (Hardware Engineering), shi ne zai karɓi ragamar jagorancin kamfanin.
Ternus ya dade ana kallonsa a matsayin amintaccen jami'i wanda ya fahimci tsarin Kamfanin Apple sosai.
Sabon Matsayin da Tim Cook Zai Karba.
Daga ranar 1 ga watan Satumba, 2026, Cook zai koma matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa (Executive Chairman), inda zai ci gaba da bayar da shawara ga kamfanin.
A karkashin Cook, Apple ya ƙaddamar da manyan fasahohi kamar su Apple Watch da AirPods, waɗanda s**a sauya yadda mutane ke amfani da na'urori a rayuwarsu ta yau da kullum.
Darajar kamfanin Apple na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin kamfanoni mafi daraja da tasiri a kasuwannin duniya baki ɗaya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tim Cook ya bayyana cewa: "Kasancewa Shugaban Apple shi ne babban gata mafi girma a rayuwata. Na gode da amanar da aka ba ni na jagorancin wannan kamfani mai cike da fasaha da hazaka."
Wannan canji na zuwa ne a daidai lokacin da Apple ke fuskantar sabbin ƙalubale na gasar fasahar AI da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.
Mutane da dama na zuba ido su ga irin sabon salon da John Ternus zai zo da shi.
Sanarwa: Wannan labari ne da ya ke faruwa yanzu-yanzu. Za mu riƙa kawo muku ƙarin haske ya yin da labarin ke ci gaba da fitowa...
20/04/2026
Aci gaba da yin uzuri wa juna, kowa akwai abin da yake damun sa a wannan Rayuwar.
20/04/2026
Iphone ko Samsung ka Zabi daya wacce tafi?.
20/04/2026
Lokacin da aka fara fitar da iPhone 17 Pro Max, launin orange ne yafi daukar hankali Mutane sosai. Saboda mutane da yawa suna son wannan color, yawanci ana sayar da shi da karin ₦50k zuwa ₦100k fiye da silver ko blue.
Suppliers ma sun lura da wannan demand din na Mutane, sai suma s**a kara farashi ga vendors da suke son sake siyo wannan color din.
Yayin da lokaci ya fara tafiya kuma
Mutane da yawa s**a fara cewa orange din ba kamar yadda s**ayi zata bane 😅
Sai kuma mutane da yawa s**a koma son silver color.
Saboda haka yanzu ma, a wasu lokutan silver din yana iya zama yafi tsada.
Wasu suppliers suna kara ₦30k zuwa ₦80k akan silver saboda yanzu shima ya zama daya daga cikin colors da akafi nema.
Saboda haka idan kaga wani color yafi wani tsada yawanci ba wani abu bane na bababn Chin aiki ko performance face demand
Color din da mutane da yawa suke so a wannan lokacin
Shine yawanci yafi tsada 💯
Achikin colors na iphone 17 promax Wanne kafisu Yafi burgeka ?👇
Wanda yafi Elon Musk arziki, shi ne, wanda ya yi raka'o'i biyu na alfijir.
22/03/2026
A wannan lokacin da kowa ke dogara da wayar hannu wajen aiki, sada zumunci, babu abin da ke tada hankali kamar ganin batirinka ya kusa karewa (low battery) alhali kana bukatar sa.
Masana fasaha sun fitar da wasu matakai guda uku masu sauki wadanda za su iya tsawaita rayuwar batirinka da kashi 30% zuwa 50% kowace rana.
Ga yadda za ka yi cikin takaitaccen bayani:
1. Rage Hasken Fuska da Kunna "Dark Mode" - Hasken fuskar waya (Screen Brightness) shi ne abu na farko da ke cinye wutar batir. Idan wayarka tana da fuska irin ta OLED ko AMOLED, yin amfani da launin baki yana kashe fitilun fuskar gaba daya, wanda hakan ke rage janye wutar batirin ka.
Mataki: Janyo saman wayarka ka rage haske (Brightness), sannan ka shiga Settings ka kunna Dark Mode.
2. Kashe "Background Apps" da Sanarwa (Notifications)
Manhajoji irin su Facebook, Instagram, da WhatsApp suna ci gaba da aiki a boye koda ba ka amfani da su. Suna neman network da sabbin sakonni, wanda hakan ke sa batir ya riga ya kare.
Mataki: Kashe sanarwar manhajojin da ba ka bukatar jin duriyarsu a kowane lokaci. Haka kuma, ka rika kashe Bluetooth da Location (GPS) idan ba ka amfani da su.
3. Kunna Yanayin Kare Wutar Batir (Battery Saver Mode)
Kusan kowace waya tana da tsarin "Battery Saver" ko "Power Saving Mode." Wannan tsarin yana takaita duk wani aiki na boye da wayar ke yi wanda ba lallai ba ne ka sani, kamar duba imel ko wasu dabarun AI na wayar.
Mataki: Kada ka jira har batir ya kai kashi 20%. Zaka iya kunna Battery Saver tun lokacin da batirinka yake kashi 50% domin ya kai ka har dare.
Guji barin wayarka tana zafi sosai, domin zafi shi ne babban makiyin batir.
Idan kana lura wayar tana yin zafi lokacin caji, cire mata murfin baya (pouch) domin ta sami iska.
Ta hanyar bin wadannan matakai guda uku, za ka rage yawan damuwar neman chaja a kowane lokaci, sannan batirinka zai dade bai lalace ba.
Engr. Mustapha AA
Kano State, Nigeria
Click here to claim your Sponsored Listing.