Ibrahim Gamji
Bahaushe / Activiste Hausa
جماعة أحباب رسول sufi/صوفي
cosmologist
If you see a tribalist in me, you are no doubt seeing a reflection of you in me.
09/06/2026
Bahaushe shi ne wanda ya ce maka shi Bahaushe ne, cike da alfahari, ba bukatar amincewar wani.Bahaushe shi ne wanda babansa Bahaushe ne Babu wani Hausa-Fulani.
Kowane mutum kabilar mahaifinsa yake bi, ba ta kakansa ba, ko da kuwa (in ma it’s logically possible) su saɓa.
Domin dai uban mutum ya zama Bahaushe ne saboda shi ma ubansa Bahaushe ne, and so on, sai dai idan a cikinsu akwai wanda ya yi amfani da assimilation ya canza kabilarsa.
Misali:
Annabi Muhammadu (SAW) ya zama Balarabe ne ta hanyar assimilation tunda za a iya tracing kakaninsa na wajen mahaifi har zuwa Annabi Ibrahim wanda shi kuma Hebrew ne, ba Balarabe ba.
The irony of it, Manzon Allah SAW bai taɓa kiran kansa da Hebrew-Arab ba kamar yadda waɗannan confused people ɗin suke so mu yarda da Hausa-Fulani.
Ibrahim Gamji
09/06/2026
"ya ya sunan macen kunkuru da hausa?" Kunkuru na daya daga cikin dabbobi mafiya tsawon rai a duniya. Masana sun ce yana kai har fiye da shekara dari biyu. A raye.
Sannan ku sani akwai na tudu sannan akwai na ruwa. Kmr dai kwadi.
Kuma Nasan wani zai tunanin shin za a iya cire wannan kokon bayan nasa? Sam ba zai yiwu ba.
Kokom bayansa Wani ƙashi ne wanda yake hade da gangar jikinsa yana da Jijiyoyi, har cikin jikinsa.
Yana amfani dashi wajen kare kansa. Kuma Idan aka matsa masa ta ƙarfi ko aka buge shi, yana iya jin zafi kamar yadda mutane ke ji Idan aka buge Su Akan ƙashi.
Sannan yanada Jini da ke zagayawa ta ciki. Shi ya sa idan da zai samu rauni ko ya tsage, zai zubar da jini kamar dai sauran sassan jikinsa.
Sannan Masan sunce Kunkuru na daga cikin dabbobin da s**a fi juriyar yunwa da ƙishirwa a duniya.
Wasu daga ciki s**an kan jure har watanni ba tare da cin wani abu ba idan yanayi yayi tsanani.
Macen Kunkuru tana yin ƙwai ne. ba wai haihuwar jarirai kai tsaye ba.
takan tona rami a cikin ƙasa kamr yanda kadangare yakeyi sannan ta ajiye ƙwan.
Tana yin kwai har zuwa 30.
Bayan ta gama, se ta rufe ramin ta bar ƙwai din a cikin Ramin Har ya isa kyankyashe kansa da kansa ba Wai uwar ce take kyankyashe Kwan dakantaba.
Kuma Jariran kunkuru da zarar sun kyankyashe kansu.kai tsaye suke fara tafiya su shiga ruwa ko daji, ba uwarsu bace ke rainon su.
Sannan masana sun ce wani nau'in kunkurun na haihuwa sau ɗaya a shekara.
Wasu sau uku (3).
Sai dai duk da cewa kukuru na yin kwai da yawa ammaa bayan sun kyankyashe kan su sanadiyyar rashin kulawar uwa kadanne ke tsira.
Ga tamabaya ya ya sunan macen kunkuru da hausa?
Ibrahim Gamji
08/06/2026
Ban kara jin Sheikh Ibrahim Inyass ya burgeni ba sai bayan kallonsa ta bangaren boko da gwagwarmaya, ba ta bangaren addini ba.
Shehu Ibrahim na cikin farkon Malaman da s**a wayar da kan musulmai a kan cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne.
Da a ce Sheikh Ibrahim ba ya yin suna a matsayin malamin addini ba ne, to da ba makawa sai ya yi shihura a duniya a matsayin babban philosopher da duniya za ta rinka bege. Sai dai shuhurar maluntarsa ta danne wannan fage.
A da saboda ma su allantar da Sheikh Ibrahim sai karsashin so da kaunar da nake masa na neme na rasa… ta fita fita kaina tas.
Sai daga baya na gane cewa a duk lokacin da wani mutum mutane s**a rabu gida biyu a kansa, tsakanin mai kambamashi har ya kai shi matsayin allantaka da kuma mai zaginsa ya mayar da shi tamkar shaidan; ka tabbatar akwai abubuwan izini a rayuwar wannan babban mutum da ya kamata a lura da su duba na tsanaki.
Kamar yadda Sheikh Ibrahim Inyass ya rabu gida biyu a gurin musulmin Yammacin Afirka, tamkar yadda Sayyidina Ali ya rabu tsakanin “Ghullatush Shi’a” masu allantar da shi da kuma Banu Umayya masu zaginsa. Tamkar Annabi Isa (AS), tsakanin Yahudawan da s**a yi zaton sun kashe shi da kuma Kiristocin da s**a allantar da shi.
Da a ce za ku ajiye addini a gefe ku bincike wane ne shi, da ko ba komai za ku sanya shi a jerin manyan malaman falsafar Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Kuma wallahi ba wai ina kaunar Sheikh Ibrahim ba ne don kawai mahaifina ya saka mini sunansa ko don na tashi a gidan sufaye, a’a har a da har kin sa na yi… Ina son shi ne kawai don fara gane wane ne shi.
Malami ne da yake daidai da zamani, idan ka karanta littafin “Beyond Timbuktu” za ka ƙara sanin wane ne shi. Akwai ra’ayoyinsa da mutane ke boyewa don kada su ruguje abun da s**a dukufa a kan me tsarki ne… kamar jihadin Shehu Danfodio.
Shehu Ibrahim (RA) ya taimaka wa addini da kayan zamaninsa da ya tarar, waɗanda Turawan mulkin mallaka s**a yi amfani da su.
Shi ne farkon Musulmin da ya yi amfani da su kuma ya halatta haka. Ya yi amfani da rediyo, telephone, rikoda, da kamara wajen isar da sakon Musulunci.
Har yau akwai ustazun musulmi da ke ganin yin hoto kafirci ne, amma Shehu Ibrahim ne ya wayar da kai a kan amfani da waɗannan kayan a cikin addinin Musulunci.
Haka nan ya yi amfani da motoci, jirgin sama, lasifika, agogo, da zuwa asibitoci.
Idan ba ku manta a tarihi ba, akwai lokacin da a tsohuwar Turkiyya (Daular Usmaniyya), s**a ce bai halatta a yi amfani da bindiga ba saboda wuta ce, kuma s**a haramta amfani da wuta wajen hukunci. To a yanzu wace ƙasar musulma ce ta ƙai su makamai? Ai sai dai ko pakistan da iran wata kila.
Kuma idan ba ku manta ba, akwai lokacin da a ƙasar Saudiyya s**a tsai da haddin kisan kai ga duk malamin da ya halatta yin wa’azi a rediyo. Haka kuma sun haramta yin alwala da ruwan famfo ɗan murɗeba (sun ce alwalarka ba ta yi ba idan ka yi), sun haramta yin ayyukan addini da kamera, rediyo, speaker, microphone, television, da telephone.
A wancan lokacin sun zagi Sheikh Ibrahim saboda ya halatta kuma ya yi amfani da su wajen harkokin addini. A yau kuma wannan duk ya zama tarihi, inda duniya ta karɓe su hannu biyu.
Shehu Ibrahim na cikin farkon Musulmin da s**a wayar da kan musulmai a kan cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne.
Shi ne farkon malamin da ya yarda cewa Turawa sun je duniyar wata a shekarar 1969 (Apollo 11) har ma ya yi littafi a kan wannan. Malaman Saudiyya sun ce duk wanda ya yarda da hakan kafiri ne, su ma na Al-Azhar (Misra) sun ce sam ba zai yiwu ba.
Amma Shehu Ibrahim ne ya gamsar da su da hujja har s**a yarda da abin.
Shehu Ibrahim (RA) ya kewaya kasashen duniya har Chana, Beijing, Hong Kong, da sauran sassan ƙarshen Asiya don taimakon Musulunci. Ya haɗa kan Musulmi Larabawa da Bakar Fata. Yana da kishi na gaske a kan addininsa na Musulunci mai tsabta, ba na ta’addanci ba.
Ibrahim Gamji
08/06/2026
Na daina bautar ƙungiyar addini tun tuni. Da ni ɗan ganin kashinin batijjane ne, ba kowa ni ke gani a matsayin musulm ba, musamman ma Shi’a. Kallon gara arna nike musu. In har malami ba batijjani ba ne, ko me zai fada ba zan saurara ba. Idan aka ce batijjanen malami ya yi kuskure, to ba zan taɓa yarda ya yi ba.
Daga baya na fara confusing, na fara judging ƙafatan tijjaniyawa da ayyukan wasu, na rika kallonsu a matsayin mushrikai. Sai kawai na canza na koma Salafi.
Na saba da abubuwa ba tare da tsattsauran ra’ayi ba. Na saba da girmama duk wani abu da ya shafi Ma’iki. Ina yarda da hadisai kowane iri, sai kawai na ji ƙwalkwale-kwalkwalenn abubuwan da kaina da zuciyata ba za ta iya ɗauka ba. Na fice na yi kundun bala na koma Imamiyya Shi’a, ba Rafidi ba. Can kau ko zama, ban yi ba, na yi fitar burtu.
Daga baya na yi tunanin kodai in zama sectless tun da kowanne yana da ra’ayinsa da ban yarda da shi ba, ko kuma in buɗe sabuwar Darika tawa ta kaina, in ɗauki hayar muridai kafin samun permanent.🤨
A Tijjaniyyance, ban yarda da wasu tatsuniyoyi ba, da wasu karamomin da s**a wuce misali. Amma ina girmama bayin Allah.
A Salafance, ban yarda da tsattsauran ra’ayin addini ba. Daga Alƙur’ani sai hadisai mutawatir na yarda 100%, amma hadisi Ahad wani lokaci ni kan zaɓi “Mashhur” ko “Aziz” kawai dai Ina zaɓar wanda bai ci karo da Alƙur’ani ba, kuma yake koyar da ilimin zamantakewa ko zaman lafiya. Amma ba na yarda da wanda ke koyar da tsattsauran ra’ayi ba.
A Shi’ance, ba na da wani hadi da su wanda ya wuce su masoya Ahlul Baiti ne. Kuma ba za mu bar masu ƙaunar Ahlul Baitin su kadai ba. Mutum ya daɗe bai kirana danShi’a ba in har don faɗar falalar iyalan Annabi ne. Ina girmama Khulafā’ur Rāshidīn dukkansu, muna son matan Manzon Allah dukkansu.
Na ga kowanne ina da jibi da su, na rasa matsaya. Sai kawai na duba na ga wani malami na fi so… sai ga Sheikh Burhan al-Khaulahi ne… Daga nan kawai na koma Sufi ɗan kan katanga.
A yanzu musulmi a wajena shi ne wanda ya ce shi musulmi ne, bana bukatar amincewar wasu akai.
Kuma kasancewar mutun mutumin kirki wanda bai cutar da kowa wanda ke alfanar al'umma shi ne mafi mahimmanci a wajena fiye da kasancewarsar dan akidara ko addini na, ka daɗe ba ka buɗe sabuwar ƙungiyar addini ba, kai ka daɗe ma ba ka buɗe sabon addini ba... kai ta shafa.
Ibrahim Gamji
08/06/2026
This guy is a Local Government Chairman who is planning to build a flyover right in the corner of his own house. 😂
Bro, at this point, the country really needs to pass a law: before giving anybody any position, they must first send the person for a mandatory brain scan.
Ibrahim Gamji
Forest trading ya fi forex trading kawo muggan kudi, shi yasa abun ya ki karewa Digal-bandits na investing a Bandits-company.
📌Gamji📌
08/06/2026
Ban taba ganin laptop me Rikon caji irin na wannan ba, Sunanta GeoBook ba China 🇨🇳 ba ce, kirar kamfanin "Geo Computers" ne da ke UK- suna yin manyan laptops da tablets.
Wannan tawa ke nan, kuma zan siyar da ita, wanda zai siya yai magana, na siyeta ne A December na 2025 a (75k) Ba ta da matsalar komai zan ba da guarantee. Ba ta sha wahalar komai ba sai zaman banza.
Baka ce wulut kuma karama mini ba katuwa ba.
On the left side you can see: USB-A port, headphone jack, micro HDMI, and what looks like a microSD slot or another USB-C port
Full-size keyboard with a Windows key, so ad
Processor: Intel Celeron or Intel N-series chip
RAM: 4GB or 8GB DDR4
Display: 11.6" or 14" HD/Full HD IPS screen
Battery: 6-8 hours on light use
OS: Windows 11 S Mode or Home
Jama'a ko ina labarin
Asadud-Bandits?
07/06/2026
"The government should seized the guns of the local people. After that, Fulani bandits tricked them by collecting their rifles in exchange for cows, or machine guns in exchange for herds of cattle (hundreds )and sometimes even cars or houses" "~Gumi~
Click here to claim your Sponsored Listing.