Bawan Allah

Bawan Allah

Share

Let's see the details and how the world is running the race with Islam and technology

05/05/2024

A fahimtata! ☮️

Kusan duk wani matashi da ya dogara da kansa musamman digitalised citizens, to abin barazana ne wa Gwamnatin Nigeria.

Ba iya ƴan crypto bane damuwar gwamnatin Nigeria.

Kusan duk wani matashi da yake ƙoƙarin dogara da kansa, ko ta hanyar Crypto ko akasin haka, musamman a ce a yanar gizo yake gudanar da harkokinsa, wato duk wani wanda yake digitalised ne, to shi ma abin barazana ne wa gwmanati.

Dalili na!

✡️ A yanzu haka matasa da yawa sun fahimci cewa gwamnati babu wani abu da za ta iya taimakarsu da shi.

✡️ Idan sun yi karatun, gwamnati ba ta iya basu aiki, idan kuma sun samu aikin gwamnatin to ɗan abinda ake ba su, ba zai iya biya musu ko da rabin buƙatunsu ba!

✡️ Dole su nemo mafita da kansu!
Hakan ya sanya wasu da yawa s**a tsunduma cikin harkokin da suke online, domin sun fahimci irin romon da yake ciki ya fiye musu tsayawa neman aiki a wurin gwamnati.

☮️ Me yasa hakan zai iya zama barazana wa gwamnati?

Dalilin shi ne...

✡️ Da yawan matasa za su zamo sun fi karfin gwamnati ta ko ina, saboda suna da hanyoyin samun kudadensu, ba sa bukatar gwamnati a cikin rayuwarsu sosai, amfanin gwamnati kawai zai zamo ɗan kaɗan ne, domin sun tsaya da kafafuwansu, sun yi karatunsu, sun nemi kuɗaɗensu duk ba tare da sa hannun gwamnati ba, ta ya ka ke tunanin gwamnati za ta iya juya su bayan babu wani abu da ta ke iya taimakarsu da shi?

✡️ So, sai ya zamo idan gwamnati ta kafa wani sharaɗi ko wata doka, sai da yawan matasa su bijirewa wannan dokar.

✡️ Ƴan siyasa za su zamo ba su da wani ƙarfi ko kuma wani abin faɗa a ji, domin matasa sun k**a abin yi, taƙamar ɗan siyasa shi ne matsayi da kuma kuɗi, to sai ya kasance wanda ka ke son juyawa ko kuma ka ke son nuna iko akansa ya ninninkaka ilimi, gogewa, wayewa, da kuma shi kansa kuɗin ma, don ɗan abin da za ka iya ba shi, zai iya samunsa cikin yan mintuna, to me za ka taimake shi da shi kenan?

✡️ Wannan ya sanya gwamnati ta ke hangen, matukar aka tafi a haka, to lalle za a zo lokacin da kowanne wayayyen matashi ɗan Nigeria ba ya buƙatar taimakon ƙasar ko kuma masu mulkin ƙasar, idan kuwa hakan ta kasance babu wani matashi da ya rage da zai iya yi musu biyayya ko kuma su juya shi yacca ransu ya ke so.

Ƙasa irin Nigeria ce kaɗai ta ke ƙokarin dakile ƴan ƙasarta yayin da suke ƙoƙarin nema wa kansu mafita, mafiya yawan shuwagabanninmu buƙatarsu kansu kaɗai ita ce a gabansu.

Allah Ka bamu shuwagabanni na gari masu kishinmu ba kishin aljihunsu ba.

Adam Abdullah Shuaib
5th May, 2024.

09/02/2024

WASANNI (SPORTS) SANA'A DA KASUWANCINSA..
(INA MUSULMI YAN AREWA)

Nayi rubutu kwanan baya, akan tasirin nishadi da wasanni (Sport nd Entertainment) ga kasuwanci da tattalin arziki a wannan lokaci da muke ciki.

Haka Kuma nayi tsokaci akan yadda muke kallon harkar wasanni musamman, da kokarin Neman halacci ko haramcin ta, duk da cewa kasashen musulmi da yawa tuni s**a yi nisa, akan sana'ar wasanni da kasuwancinsa.

Tabbas harkar wasanni a yau musamman kwallon kafa, ta zama hamshakiyar sana'a mai riba, gashi Kuma bata bukatar Jari mai yawa.

Manufar rubutun a wancen lokacin shine, mu dawo mu sake kallon al'amura a ma'aunin shari'a sosai, ba ma'aunin zato ba, kona Wani ra'ayi Wanda bashi da tushe a shari'a.

Haka kuma mu sake duba wasu abubuwan da suke Kara dakushe tattalin arzikin mu, musamman a wannan lokaci da yawan mu yake karuwa, Kuma bukatar ayyukan yi da sana'oi itama take karuwa.

Idan zamu iya tunawa na kawo fasalin alkaluma na irin kudaden da suke cikin harkar nishadi da wasanni da ayyukan walwala, Kuma duka cikin halal ba tare da an shiga wata hanya, wacce ta sabawa shari'a ba.

Harkar wasanni a yanzu ta hada da su yan wasan, Samar da kayan wasan (Sport Wears) dillancin yan wasan (Agency) tallace tallace, ga Kuma filayen wasan da sauransu.

To a yauma dai naci karo da Wani lissafi Mai ban sha'awa a hannu daya, a daya hannun Kuma Mai ban takaici.

Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria wadda a yanzu ta Kai ga wasan karshe a gasar kofin Africa, an kimanta darajar kungiyar bisa laakari da kudaden da aka sayi yan wasan na super eagles a kulob kulob.

Adadin kimar kungiyar ta Nigeria takai dollar Amurka miliyon dari uku da hamsin da takwas.
$380 million dollars.

A kwatancin Naira kudin ya Kai Biliyon dari biyar da saba'in.
=N=570 billion.

Wannan ba karamin kudi bane, balantana Kuma idan aka hada da kudaden alawus alawus na sati sati da yan wasan ke karba a kasashen da suke taka leda.

Tambayar anan itace, yan kwallon kafa nawa ka sani masu taka leda a kasar waje Kuma Hausawa da Fulani yan Arewa, a Unguwar ku, ko a kauyen ku?

Bance Babu ba, sai dai Muna iya cewa yan kwayoyi ne, idan ka kwatanta dana kudancin Nigeria.

To ka dawo ka sake lissafi, nawa wadannan yan wasa suke turowa gida Nigeria ga iyalansu da iyaye da Yan uwa a Shekara??

Babu bukatar sharri mai yawa musamman idan muka dubi yadda yan wasan kwallon kafa s**a zama hamshakan attajirai, Kuma a kananan shekaru.
Irin kudaden da ko mukamin siyasa za'a bashi ya saci kudin talakawa ba zai samu irinsu ba.

Irin wannan kudade daga harkar wasanni, zasu cike gibin da ake dashi na hanyoyin samun kudin shigar alumma, musamman matasan mu masu basira, Kuma su canja rayuwar iyalai.

Don haka yana da kyau mu sake duba al'amura, mu Kuma rika tattance fatawoyi na gaskiya da Kuma na Mai karamin Sani.

Domin akwai alaka Mai karfi tsakanin tattalin arzikin musulmi da siyasa dama kwarjinin Musuluncin.

A duk lokacin da Wani abu ya taso zakaga shahararrun yan kwallon kafa musulmi, irinsu Mohammed Salah da Kareem Benzema da Mesut Orzil da Hakimi, maganganun su ko nuna damuwar su, yafi na wasu shugabannin kasashen musulmin tasiri da amo.

Allah yasa mu fahimci siyasar zamani data kasuwanci a wannan Karni na ashirin da daya, mu Kuma shiga a dama damu sannan mu yaki talauci, mu sayi martaba da mutuncin da aka San al'ummar musulmi da ita.

Barka da juma'a.

©️ Bello Ado Hussaini
9th February, 2024.

07/02/2024

Gare ka abokina: LOKACI YAYI!

Zan fadi maka gaskiya. Ba lallai tayi dadi ba. Amma haka take. Wallahi yanzu lokacin dogara da albashi musamman karamin albashi irin namu ya wuce. Lokaci ne yanzu da mutum zai zage damtse ya cire kasala ya cire jin kai da kunyar mutane ya nemi kuddi. A halin da ake ciki babu wani aikin k’ask’anci. Duk wani aikin da zai kawo maka taro—sisi to wallahi aiki ne me daraja.

Idan Allah be kaddare ka da kwarewa a wata sana’ar hannu ko wani skills da mutane ke bukatar expertise din ka ba, to lallai ka sani cewa lafiyar da Allah ya baka da karfi shi ma jari ne. Kaga duk ayyukan ga da a da baka iya yin su saboda kai ma’aikacin banki ne ko malamin makaranta ko honorable ake ce maka ko kuma office gare ka a ministry? To wallahi lokaci yayi da zaka cire rigar jin kai ka neme su.

Babu sana’ar da ba zaka iya zamanantar da ita ba a matsayin ka na me ilimi. K**a daga wankin mota, wankau, achab’a, noma, leburanci, nomau, dako, tura baro, sayar da ruwa, da sauran su, duk wanda ya fi maka sauk’i, ina kara nanata maka ya kai abokina, duk wanda yafi maka sauki wallahi kayi abinka. A halin hanzu babu issue irin yunwa. Haka kuma babu kaskanci a neman kuddi, duk kaskanci be fi ka tsaya jiran wani yayi maka ba.

Idan kuma Allah ya sa kana iya hakurin koyon skills k**an su walda, dinki, faci, painti, POP, da sauran su, to lallai ka mayar da hankali ka iya su saboda Allah kadai ya san ranar fita wagga cakwakiya. Kun dai ga wahalar lokacin Buhari ta sa mafi yawan mutane k**a online businesses. Wasu sun samu sa’a daga nan liyafa tayi sama. To ina mai nuna maku, wanga lokaci da k’wadago yazo, wato hard labour.

Abokina me karamin albashi, zan kara nanata maka, kada ka bari kunyan makwabta ko yan mata ko tsohhin abokan karatun ka ya hana ka yin sana’ar da aka raina. Babu raini irin ka tsaya jiran ayi maka. Dukkanin wadanda kake jin kunyar suyi gulman ka cewa kana kwadago, babu wanda zai baka idan baka da.

Hasalima still sai sun yi gulmar ka din cewa ka cika rok’e—rok’e. Ka kau ga ai gara ayi gulmar cewa yanzu dako kake yi da ayi gulmar cewa yanzu baka da aiki sai rok’e—rok’e. Tunda ita dai yunwa idan ta kawo visit to ai dole a saurare ta, ka kau ga option biyu ne; ko dai k’wadago a rufa ma kai asiri, ko kuma barace—barace.

Abokina na roki Allah ya rufa maka asiri ya baka mafita a dukkanin tsanani. Ka sani cewa komi yayi zafi maganin shi Allah kuma lallai duk wanda ya nema Allah zai bud’e mashi k’ofofin arzikin sa. Ba sai mun yi kuddi mun tai Makka mun tai Dubai ba, ba sai mun sayi mota ko mun gida katafaren gida ba. A’a in dai mun samu abinda munka rufa ma kan mu asiri, to AlhamdulilLahi🙏

Credit; Unclè Anass Dukura

07/02/2024

~>Muhammad, is my first son. Duk sanda yaci abinci ya koshi yaji dadi, sai yace dani, Papa, when I grow up you would tell me the secret to choosing a good wife. He sees that his mummy is good and we always appreciate her.

Yanzu is not the right time to discuss marriage with the 8 year old Muhammad, but ina so na amsa wannan tambayar saboda matasa masu shirin yin aure sannan kuma idan bankai lokacin ba, Muhammad zai iya karanta wannan rubutun. Muje zuwa:

Yadda ake zabar mace ta gari shine: Da farko abin tushe yake samu. Idan iyaye na gari ne, to bakada damuwa, domin zasu tsaya sosai wajen ganin ka samu mata ta gari. To amma wani sirri da ba kowa ya sani ba shine. Ita mata ta gari ko miji na gari iyaye ne suke roka maka tun kana yaro, tun ma baka san kanka ba. Haka iyayen mu su kai mana. Tun muna yara ake ce mana "Allah ya baku mata nagari". Wannan ita ce nasara ta farko. Don haka idan kana da iyaye a raye, ka ce musu su rika maka adduar Mata tagari domin babu hijabi tsakanin adduar iyaye da Ubangiji.

Na biyu kuma shine, Ka zama nagari:
Nagari ne kadai yake iya gane mace tagari. Idan kai shashasha ne, dan sharholiya ne da iskanci, kuma kana bin mutanen banza, toh ba ta yadda zaka iya gane mace tagari. Yazo a cikin suratul Nur aya ta 3,inda Allah yake cewa mutumin banza baya aure sai daga macen banza, hakanan macen banza bata aure sai daga namijin banza. Don haka idan kana son mace tagari, kai ma sai ka zama na gari.

Na uku, zabi mace daga gida nagari:
Gida na gari baya buya, kowa ya sani. Ance ido ba mudu ba yasan kima. Don't underestimate that statement. Kaje Unguwa ka tambaya, indai gidan su mutanen kirki ne za'a gaya maka. Kuma tun daga inda ka fara magana da yarinya zaka gane gidan su wane irin gidane. Shaida ta farko itace, yar mutanen kirki baza ta fara tsayawa da kai ba sai ka nemi izinin mahaifin ta. Sannan a yanayin shigarta da maganar ta da kallo, da mu'amalar ta, tun anan zaka gane ita yar wane irin gida ce. K**ar yadda za kayi bincike akanta, haka za kayi akan Baban ta da Babar ta. Dan uwa idan Allah yasa kayi dacen surukai k**ar yadda nayi, to 80% na matsalar aure ka gama da ita.

Na hudu, Ilimi da Tarbiyya:
Bayan ka gamsu da ita da iyayen ta, ya k**ata ka duba ilimin ta da aqeedar ta. Anan bawai so ake ta zama malama ba, inda akwai basics na addini da tarbiyya, shikenan. Dama ita mace, mijin ta shi ke ilmantar da ita bayan iyayen ta. Mahaifiya ta har ta rasu tana da shekaru hamsin da motsi bata daina zuwa makarantar Islamiyya ba. Mahaifin mu ya ci gaba da tsayawa akan karatun ta. Don haka ba lalle sai ka auri wadda ta haddace Qur’ani da littittafai ba. Kaima malamin ta ne.

Na Biyar, Ka cire kyau da arzuki daga lissafin ka:
Babu laifi ka bi kyau da arzuki; sunnace, amma kar ka bari ya zama shine babban dalilin ka na zabar mace. Mafi kyawun kyau shine hali nagari, tarbiyya da addinin. Kyau yana gushewa, arzuki yana karewa, amma hali nagari baya gushewa ko bayan sheraka miliyan ne. Kuma shi kyau, kai ne kake assasashi, kai kake kalatoshi daga jikin mace. Wata macen duk kyan ta idan aka baka ita sai ta lalace, saboda ba ka gyara ta. Don haka idan kana son kyau a mace, kai ne zakai mata shi, ta hanyar kulawa da ita.

Na karshe, barin bid'oin Aure:
Zaka iya dacewa a duka abu biyar din da nayi bayani akai. Amma sanya bid'a a cikin aikin ka, zai iya rusa rayuwar ka da ta iyalan ka. Ita bid'ar aure tana kwashe albarkar aure. Aure ibada ne. K**ar yadda shigar da bid'a cikin ibada (misali Sallah) yake lalata ibadar haka shigar da bid'a yake lalata aure. Idan kazo aure kayi aure irin na musulunci. Ka biya sadaqi irin wanda sunnah tace, kar yayi tsada, kuma kar yayi arha. Domin Manzon Allah SAW ya ce duk auren da akayi shi da sauki yafi albarka. Wannan hidimomi da ake na aure a tara makada da maza da mata a cakude, kar kayi. Sannan shigar banza da amare suke yi, kaga an bayyana tsiraici da surar mace duk kar kuyi. Ya zamana cewa a wannan rana ta bikin ku mala'ikun rahama ne suke sauka suke muku addua. Idan shaidanu su kayi yawa sai dai tsintuwar Allah da ta mala'ikun. Ina aure zai albarka?

Ni a ganina ta haka ne kake dacewa da mace tagari irin wacce yaran ka ma idan s**a gani zasu ce Baba Allah ya saka da alkhairi, ka aura mana uwa ta gari. Kai kanka sai kayi alfahari da kanka a wannan lokacin. Tabbas tasirin uwa tagari babbane. Duk sanda akayi maganar uwa ta gari kissar mutane biyu tana zuwa kaina: Imam Ahmad Bin Hambal wanda mahaifiyar sa ta tsaya tsayin daka wajen ganin ya samu ilimi da tarbiyya. Wadda ta dalilin tarbiyyar ta da gudunmawar tane yau Duniyar Ilimin Hadithin take tak**a da Iman Ahmad. Na biyu shine kissar yaro wanda mahaifin sa ya kai kara wajen Sayyidina Omar akan cewa, ɗansa yana zagin sa. Da aka kira dan sai yace ai laifin baban sa ne da ya aura masa uwa mutuniyar banza.

Toh Allah yasa mu dace.

✍️Muhammad Ubale Kiru
🌐

02/02/2024

Shekara 40 data wuce, Naira ta fi Dollar tsada inda ake chanzar da Dollar ƙasa da Naira ɗaya, $1 tana daidai da ₦0.75 a January 1984.

Ga yadda farashin ya rinƙa chanzawa a tsawon shekaru a gomnatance:
A shekarar 1981 — $1/₦0.61 Kobo
In 1982 — $1/₦0.67 Kobo
In 1983 — $1/₦0.72 Kobo
In 1984 — $1/₦0.76 Kobo
In 1985 — $1/₦0.89 Kobo
In 1986 — $1/₦2.92..
In 2000 — $1/₦102.11..
In 2020 — $1/₦358.81

In 2024 — $1/₦896.89 (farashin gomnati)
In 2024 — $1/₦1,409.28 (A kasuwar bayan fage)

26/01/2024

Jima'i A Yau
~~~~~~🔞

A yan shekarun nan matsala jima'i na daga cikin matsalolin da suke lalata rayuwar aure. Ire-iren matsalolin sun hada da rashin yin jima'i shi kansa, rashin lafiyar gaba, sihiri, tasirin po*******hy wato blue film da sauran su. Amma a yau, ina so nayi focussing ne akan matsalar da po*******hy ya haifar a wannan zamanin.

A Yau yana wahala ace akwai saurayi matashi ko yarinya matashiya da basu taba kyella ido akan wannan fim na badala da ake kira da blue film ko p**n ba. Kusan duk a cikin mutum 10, to 8 zun taba kallo, ko dai so daya, ko sau biyu, ko ma fiye da haka. Wasu ba sun kalla bane da niyyar ci gaba da kallo, ko don suna so. Sun kalla ne watakila saboda sun ji wani yayi zancen, ko kuma sun ci karo da shi wajen kallon fina-finan Amurkawa, ko kuma don kashe kwar-kwatar ido (Allah ya tsare mu).

Kusan ya zama al'ada yanzu, idan matasa za suyi aure sai sun kalla, ko dai saboda curiosity, ko kuma saboda neman ilimi, wanda kuskure ne hakan. Domin kuwa Malamai magabata sun tabbatar mana da cewa lamarin jima'i lamari ne daga Allah, kuma dan Adam baya bukata a koya masa, Allah ne yake bada ilimin idan lokacin yayi. Shi yasa idan ka balaga abu na farko da kake fara gani shine mafarki kana saduwa. P**n ba shine ya dace ya koyarwa kai ilimin jima'i ba, saboda haka ne ma nake so a cikin wannan rubutu na bayyana mana wasu abubuwa da yawa da muke ji, ko muke gani, ko ake fada game da jima'i da kuma illar da p**n ko blue film yake bari a kwakwalwar mutane.

Kallon wannan fim na badala ya canja mindset din matasa da yawa, kai har ma da wasu manyan. Domin kuwa yanzu ana iya samun mace ta koka akan cewa mijin ta baya iya gamsar da ita yadda take so. Ko kuma namiji yaji a ran sa idan bai laga-laga da mace ba, to bai cika namiji ba. Ko kuma wasu suji, ai kai ba jarimi bane sai idan zaka iya hour kaza, ka kayi jima'i a dare sau kaza, shine ka cika jarima. Hakan nan idan kaje kasuwanni magani, da chemists, za kayi ta cin karo da maza suna karbar magunguna Manpower don zaburar da kawunan su. Su ma matan ba'a bar su a baya ba, domin kuwa basa zama ba tare da sun sha ko sun ci wani abu mak**ancin wannan ba. Bana manta labarin wata baiwar Allah da muka kashe auren ta saboda mijin ta yana shan magani manpower sosai, a rana maganar bakwai ake zuwa goma. Wallahi wannan ne sanadiyya mutuwar auren.

Abin da mutane da yawa basu sani ba shine: Jaridar Cosmopolitan ta wallafa wani interview da tayi da jaruman blue film su 40. A inda bayanansu s**a nuna cewa shi film din blue film ko p**n, film ne k**ar kowane irin film. Yana dauke da scripts, wato labari, action, fiction da sauransu. 70-85% na abubuwan da ake bayyana wa a p**n ba gaskiya bace zalla, akwai zuki-ta-malle wato fiction. Za'a iya nuna jarimi da jaruma sun shafe hour daya zuwa biyu suna abu daya, amma a bayan fage, sun tsaya sun huta sama da sau biyar. To amma a camera an yanke don kar ka gani. Saboda haka ake so ka yarda.

S**a kara da cewa, badan suna hadawa da magani ba, da ko minti 10 baza su iya yi ba, kuma ba don taimakon camera ba, da shima hakan bazai samu ba. Wata daga cikin wanda akai wa interview din ta kara da cewa, ko iface-iface da suke yi, saka su akeyi don karawa kallon armashi. Ta kara da cewa, wasun su, a cikin tsananin zafi suke, saboda abin ya wuce hankalin da kuma limit da jikin dan adam zai iya dauka. Don haka Director ne zai ta cewa ayi ta ihu don a inganta scene din da ake. Don haka ba gaskiya bane. Wani jarima shima ya tofa albarkacin bakin sa inda yace, shi mai aure ne, kuma tunda yake saduwa da matar sa, bai taba wuce min 20 ba. Wanda idan da kuwa a film ne, har mai hour uku yayi.

Idan ka koma bangaren litittafen Hausa da Novels, suma sun taimaka kwarai wajen sanyawa matasa tutani mak**ancin wancen, da burika wajen mu'amalar auratanya. Wannan shima koma bayane sosai, domin kuwa mata s**an kalli mazajen su a matsayin malalata, ragwaye, marasa kuzari, saboda su a tunanin su, namiji shine wanda yake lasting minti 30 zuwa hour daya. Sannan bayan ya sauka, ya sake komawa, idan ya sauka ya sake, akalla sau uku ko hudu kafin Asuba. Tabbas akwai maza jarumai wadda zasu iya haka. To amma tambaya anan shine, meye matsayin hakan a lafiyance sannan da kuma addini?

Yazo a cikin Sahih Bukhari, Manzon Allah SAW yana cewa mu guji yin abubuwa over, domin duk abinda ya wuce hankali yana zama cuta ne ga dan adam. Jaridar Pl***oy ta Amurka ta wallafa wani bincike da tayi akan adadin mutanen da ya kai dubu hudu, a inda binciken nunawa cewa kaso 50% daga cikin participants din only lasted 9 minutes 40 seconds a lokacin saduwa. Kaso 30% kuma minti 14 da second 10. Kaso 20% kuma minti 20 daidai. Sai masana s**a karkare cewa average mutanen duniya a yadda Allah ya tsara halitta, basa wuce minti 4 zuwa minti 9 a lokacin saduwa (Saduwa anan yana nufin sanda aka hade tirmi da tabarya). Sannan mafi yawancin mutanen duniya suna saduwa ne sau uku kacal a kowane sati. Kadanne daga cikin mutane suke saduwa kullum ko kuma fiye da sau daya a kowane wuni. Amma dai bayanai suna nuna cewa it is not normal dan adam yayi jima'i fiye da sau uku a wuni daya. Bayanai sun nuna cewa masu yin jima'i sama da 5 zuwa bakwai suna developing wata cuta mai sanya kwayayen da-namiji su fara fitar da jini a maimaikon maniyyi. Sannan yi din da yawa ta hanyar amfani da maganin sanya dadewa yana kawo mutuwar gaba ta dindindin bayan shekaru sun ja.

Don haka ina so na ja hankalin ma'aurata da su sani cewa. Abinda suke karantawa a littafi ko suke kallo a film, ba wani abu bane illa shirin film ne kawai. Shirine don kayatarwa da nishadatarwa. Sannan binciken masana ya nuna k**ar yadda yazo a mujallar PentHouse cewa ma'auratan da suke ta'ammali da p**n basa iya gamsar da juna a lokacin saduwa. Jaridar ta kara da cewa, wannan matsalar tana haddasa mutuwar aure da 9% a kasar Amurka duk shekara. Sannan ta kara da cewa: bayanan sirri na p**n industry sun nuna cewa industry din tana fuskantar kalubale na shara'a da mutane da dama wanda s**a dauka cewa p**n gaskiya ne, domin a cewar su, yayi destroying expectations na su kuma ya lalata musu rayuwar aure.

Bari na dakata anan. Allah ya bamu ikon fadin gaskiya da kuma aiki da ita, ya kuma ganar da mu gaskiya duk rintsi, sannan ya kare mana idanuwan mu daga zinar ido.


✍️Muhammad Ubale Kiru
📅26/01/2024
🌐

07/01/2024

InnalilLahi Wa Inna Ilaihir Rajiun!

Jiya na tsinkayi Viden wannan yaron.

Allah Ka tsare mu da tsarewarKa.

Photos from Bawan Allah's post 10/11/2023

YADDA AKE SAMUN KUDI A FACEBOOK TA HANYAR "Facebook Stars" A (Professional Mode ko Page)

Facebook Stars wani tsari ne da facebook ke baiwa mutun damar samun kudi daga wajen followers dinsa ta hanyar posting dinda yake. Mabiyansa ko "Followers" dinsa zasu iya siyan "Stars" su turamasa a duk wani posting dinda akwai damar hakan ko ince anyi Enabling din Stars din. Posting din zai iya zama Video Post, Hoto, text dama ko wane iri harma da live video. Ga kowane Star da mutun yasamu facebook zai biyashi $0.01 USD dai dai da 4.41 a Naira. Idan yazama kai mai yawan posting video da Reels ko posting haka, Facebook zai iya sak**a Facebook Stars automatically basai kayi apply ba, idan kuma ba'a saka maka ba sai kayi apply. Sai dai wannan tsarin ba kowa Facebook ke baiwa ba sai wanda yacika ka'idar samun shiga tsarin, basai mai Page kadai ba Har wanda ke professional mode na iya samun damar shiga.

Daya daga cikin ka'idojin shiga wanna tsarin ga masu professional mode shine dole mutun yazamto yanada followers wanda bai gaza dubu ba (1000 followers) har tsawon kwanaki 60. Yana da kyau kafin mutun yayi apply ya tabbatar yacika ka'idojin, domin dubawa ko mutum yacika ka'idojin sai abi wannan hanyar.

Ga masu Professional Mode:
1. Da farko mutun yaje profile dinsa sai ya danna wajen digo guda ukun domin yakai shi dashboard dinsa.
2. Daga nan yadanna "Tools to Try" daga nan "Stars" don ganin ko ancika ka'idar.

Ga masu Pages:
1. Da farko mutun yaje Creator Studio ta wannan link din https://business.facebook.com/creatorstudio/home
2. Daga nan sai adanna "Monetization" dake gefen hagu. Ananne za'aga ko ancika ka'idar.

Idan mutun yacika ka'idojin ga yadda ake setawa ko ince Apply

Ga masu Profession Mode:
1. Da farko mutun zaije inda "Tools to Try" yake, sai ya danna "Stars".
2. Yayi accepting "Terms and Condition" tun daga nan mutun zai fara ganin Stars din sun fara bayyana a post dinsa, sai dai mutun bazai fara samun earning dinsa ba har sai ya seta Payment account dinsa.
3. Daga nan za'a tambayi payment details din mutun. A payment details din Mutun zai iya saka "Bank account" ko "PayPal" sannan sai uploading "Tax Form".
4. Daga sai ayi reviewing bayanan da mutun ya bayar ya tabbatar dai dai ne shikenan.
5. Idan mutun yanaso yaga stars din da yasamu zai iya shiga Your Tools daga nan Stars.

Ga masu Pages:
1. Da farko aje Creator Studio ta link dinda na bayar a sama sai "Monetization"
2. Ayi accepting terms and condition
3. Daga nan za'a tambayi payment details din mutun. A payment details din Mutun zai iya saka "Bank account" ko "PayPal" sannan sai uploading "Tax Form".
4. Daga sai ayi reviewing bayanan da mutun ya bayar ya tabbatar dai dai ne shikenan.
5. Idan mutun yanaso yaga stars dinda yasamu zaije "Creator Studio > Monetization > Stars".

Za'a iya withdraw idan mutun yasamu $100 USD. Ko kuma yasamu 10,000 Stars.

Bayan wannan akwai hanyoyin samun kudi a Facebook yakai hudu da in nasamu lokaci zan kawosu.

- Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
10/11/2022.

01/11/2023

3𝗠𝗧𝗧 𝗡𝗔 𝗡𝗜𝗧𝗗𝗔; 𝗧𝗔𝗤𝗔𝗜𝗧𝗔𝗖𝗖𝗘𝗡 𝗕𝗔𝗬𝗔𝗡𝗜

Duba da yace na ga ana da buqatar qarin bayani akan jerangiyar karatuttukan da NITDA s**a fitar don mutane su qaru da ilimin na kimiyya da fasaha, ga sharhi zan yi akan dukkan kwoursa-kwasan da s**a lissafa zasu koyar, amman kafin nan, Abu me muhimmanci shine ya k**ata mu musamman en arewa mu sani, eh fa ana samu sosai ma, amman ba fa kasafai lokaci daya ake samun kuɗi daga shiga harkar tech ba.
Na ga ma har wasu tambaya suke nawa za su bayar in sun yi register? Me sa su samu ? Da dai sauran wasu tambayoyin da be k**ata ba gaskiya. Su waɗannan kwoursa-kwasan da s**a lissafa, kan mutun ya samu koyan su ma biyan kuɗaɗe aka masu matuqar kauri kan a ma samu a koya wa mutun su (ku duba Google ku gani), nan kam kyauta za a koyar.
Abu na qarshe, ina fata in kun samu kun fara koya kar se an fara tafiya duk Ku zo ku bar karatun don hakan ya faru a course din Blockchain din da BSV s**a bada scholarship a baya.
Allah ya sa mu dace ya bamu ilimi mai amfani kuma mai amfanar wa.

_____
1. 𝙎𝙤𝙛𝙩𝙬𝙖𝙧𝙚 𝘿𝙚𝙫𝙚𝙡𝙤𝙥𝙢𝙚𝙣𝙩
Wannan shi ilimi neh wanda ake amfani da shi wajen qirqran manhajar (apps) da ake amfani da su a kan wayoyi ko laptop (systems). Akan yi amfani da wasu yaruka neh da computer ke ganewa wajen hada su, irin su Python , javascript da sauran su. Fanni neh kuma mai buqatar tunani gaskiya

2. 𝙐𝙄/𝙐𝙓 𝘿𝙚𝙨𝙞𝙜𝙣
Wannan shi ake amfani da shi wajen fitar da samfurin manhaja kan a gina su , wannan ke bada damar ganin yacce fasalin manhajar da za a gina zae fito ko zai kasance tun kafin a gina manhaja (apps & website) ta hanyar " Software development" ko in ce "coding"
wannan zae fi daɗin koya ga masu son graphic design da zane

3. 𝘿𝙖𝙩𝙖 𝘼𝙣𝙖𝙡𝙮𝙨𝙞𝙨 & 𝙑𝙞𝙨𝙪𝙖𝙡𝙞𝙨𝙖𝙩𝙞𝙤𝙣
Ilimi neh da ake amfani dashi wajen tarawa, tacewa da kuma fitar da bayani ciki wani tsari na musamman don fitar da bayani masu amfani a yanayi mai sauqi.
Akan yi amfani da ilimin statistics neh da taemakon wasu manhajun da aka ƙriƙira musamman don hakan, irin su Power BI ko MS excel

4. 𝙌𝙪𝙖𝙡𝙞𝙩𝙮 𝘼𝙨𝙨𝙪𝙧𝙖𝙣𝙘𝙚
Toh, wannan su ke taemaka wajen tabbatar da chewa manhajar da aka ƙirƙira ya chin wa manufar da ya sa aka ƙirƙire su. S**an kuma yi aiki neh tare da masu gina manhaju domin gane gyararrakin da ya k**ata.
S**an gwada manhajun da aka ƙirƙira neh ta hanyar gwaji da gano kurakurai (bugs)

5. 𝙋𝙧𝙤𝙙𝙪𝙘𝙩 𝙈𝙖𝙣𝙖𝙜𝙚𝙢𝙚𝙣𝙩
Su product managers su ake ba wa ragamar gannin chewa duk wani manhajar da za a gina sun kula da shi tun daga farkon gina shi har ei zuwa a gama gina wa har a fitar da shi kasuwa ko wa mutane don aiki da shi.
K**ar dai yacce muka san manajoji ke yi a companoni

6. 𝘿𝙖𝙩𝙖 𝙎𝙘𝙞𝙚𝙣𝙘𝙚
Wannan fanni neh da ya hade ilimin computer, kididdiga da lissafi don fitar da ilimi masu amfani daga wasu tillin bayanan da aka tattara (data)
Su kan samo mafita neh ga fannoni daban daban da ilimin da suke da shi

7. 𝘼𝙣𝙞𝙢𝙖𝙩𝙞𝙤𝙣
A sauqaqe wannan ilimin zane neh ta hanyar amfani da computer ko kuma in che da shi ake amfani wajen fitar da ire-iren hotuna masu motsi na ƙyawatarwa da kuma vedos irin wadanda muka fi sani da cartoon

8. 𝘼𝙄 / 𝙈𝙖𝙘𝙝𝙞𝙣𝙚 𝙇𝙚𝙖𝙧𝙣𝙞𝙣𝙜
Ilimi neh da ake amfani da shi wajen hada-hadar manhaja masu ban mamaki wanda ke iya aiki irin na bil'adama ta hanyar koyo da kansu da kuma Koyarwa ko amfani da abin da s**a koya. Misali→ mota mai tuqa kanta

9. 𝘾𝙮𝙗𝙚𝙧𝙨𝙚𝙘𝙪𝙧𝙞𝙩𝙮
Ilimin neh na bada kariya ga manhaja don kare masu kutse daga iya shiga chikin manhajar don yi barna ko kwashe bayanai da duk wani abinda ya shafi tsaro na manhaja

10. 𝙂𝙖𝙢𝙚 𝘿𝙚𝙫𝙚𝙡𝙤𝙥𝙢𝙚𝙣𝙩
K**ar dai yacce kuka ji sunan neh
ilimin qirqiran manhaja neh wasa wanda ke fitowa a sumfuri irin na Vedio tsakanin masu wasa.

11. 𝘾𝙡𝙤𝙪𝙙 𝘾𝙤𝙢𝙥𝙪𝙩𝙞𝙣𝙜
Wannan ilimi neh na ajiye bayani chikin iska ba tare da damuwa ko siyan wajen aje bayanai ba masu Chika waje ga masu amfani da bayanai
__Nayi chikaken bayani kan cloud computing a baya, za ku iya bibiya ku duba.

12. 𝘿𝙚𝙫 𝙊𝙥𝙨
Wannan wani tarin masu ilimin fasaha neh da ya qunshi ilimin gina manhajoji da kuma ilimin kula da aiki da su.
S**an yi aiki neh wajen haduwa don sauqaqe tsarin gina manhaja har ei zuwa a saki wannan manhajar don amfani
A sauqaqe hadakar masu ilimin gina manhajoji neh (senior men)

____
Ga bayani nan an yi in sha Allah
Shin har yanzu ki/ka kasan sanin wanne ya k**ata ku koya a cikin su ??
To karanta wannan rubutun nawa : https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1014165513259178&id=100039972169173&mibextid=Nif5oz

- Za a fara karatun neh 14 ga watan nan da muke chiki (November) , 2023. Kuma iya mutane 30,000 za su dauka.
- Za kuma suyi gwaji kan a dauki waenda za a fara karatun da su don zaɓen waenda s**a Chan chanta.
- Ba kuma iya wannan karan kadai bane, za a kuma wasu sabbin karatun lokuta masu zuwa nan gaba. Wannan horarwan kuma kyauta neh, an dauki nauyin Koyarwn. Wannan horarwan kuma zae kasanche neh online da kuma Koyarwa na gani da ido (physical)

NITDA Nigeria
___________
✍️ Naim Hussain

NITDA NigeriaNaim Hussain

07/10/2023

✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani
Wanne ne Bidi'a tsakanin Maulidi da Tafsiri a Watan Ramadhan?

Asali 'Yan Bidi'a sun yarda Maulidi Bidi'a ne. Sun san babu dalili na Shari'a da ya yi nuni a kan bikin Maulidin. To ganin Ahlus Sunna sun matsa musu da inkari, saboda Annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya yi bidi'a an mayar masa", kuma ya ce: "Kowace Bidi'a bata ce,, kuma tana wuta", to sai suke neman abokan bata, abokan shiga wuta. Ma'ana su ba za su dena bidi'ar ba, amma ku ma Wahabiyawa kuna yin bidi'a, don kuna yin Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi.

Wannan shi ake kira "Ilzami" a ilimin "Jadal da Munazara", amma sai dai hujja ce mai rauni a wajen "Mu'aradha", sai dai a yi amfani da "Ilzami" don nuna bacin ra'ayi ko bacin dalili, wannan kuma ba shi ne muhallin maganarmu da su ba.

Don haka abin tambaya shi ne; shin da gaske yin Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi bidi'a ne, ko yana da asali a Shari'a?

Lallai ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
«كان رسول الله صلى الله عليه وسلم أجود الناس، وكان أجود ما يكون في رمضان حين يلقاه جبريل، وكان يلقاه في كل ليلة من رمضان فيدارسه القرآن، فلرسول الله صلى الله عليه وسلم أجود بالخير من الريح المرسلة»
صحيح البخاري (1/ 8)، صحيح مسلم (4/ 1803)

"Manzon Allah (saw) ya kasance mafi kyautan mutane, kuma ya kasance mafi kyauta a cikin watan Ramadhan, lokacin da Mala'ika Jibril (as) yake haduwa da shi, ya kasance yana haduwa da shi a cikin kowane dare na watan Ramadhan, sai su yi DARASIN ALKUR'ANI TARE, lallai Manzon Allah (saw) ya fi iska mai kadawa yawan kyauta da alheri".

Wannan Hadisi ya nuna cewa; Lallai Annabi (saw) da Mala'ika Jibril (as) suna haduwa suna yin darasin Alkur'ani a kowane daren Ramadhan har ya kare.

Shi ya sa Ibnu Battal ya ce:
"ومدارسته له القرآن فى كل رمضان. وخص رمضان بذلك، لأن الله تعالى أنزل فيه القرآن إلى السماء الدنيا، ولتتأسى بذلك أمته فى كل أشهر رمضان، فيكثروا فيه من قراءة القرآن، فيجتمع لهم فضل الصيام والتلاوة والقراءة والقيام".
شرح صحيح البخارى لابن بطال (1/ 40)

Sai ya ce: suna yin Darasin Alkur'anin a kowane dare na Ramadhan ne don a Ramadhan din aka sauke Alkur'anin, kuma DON AL'UMMARSA SU YI KOYI DA SHI, su ma suna yin Darasin Alkur'anin a kowane watan Ramadhan.

Malamai masu sharhin littatafan Hadisai sun tabbatar da cewa; wannan Darasi na Alkur'ani a cikin Ramadhan MUSTAHABBI ne, saboda wannan Hadisi. K**ar al-Nawawiy, al-Ainiy, inda ya ce:
"ومنها استحباب استكثار القراءة في رمضان ومنها استحباب مدارسة القرآن وغيره من العلوم الشرعية".
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (1/ 77)

In kun lura shi har ma ya kara da sauran Ilmomin Shari'a, duka dogaro da wannan Hadisi na Ibnu Abbas (ra).

Sannan akwai Hadisin Abu Huraira (ra) wanda Muslim ya ruwaito, wanda ya fadi ladan masu haduwa a Masallaci suna Darasin Alkur'ani: Annabi (saw) ya ce:
«وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله، يتلون كتاب الله، ويتدارسونه بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده،».
صحيح مسلم (4/ 2074)

"Babu wasu mutane da za su taru a daki daga cikin dakunan Allah (Masallaci), suna karanta Littafin Allah, suna Darasinsa a tsakaninsu, face nitsuwa ta sauka a kansu, rahma ta lullube su, Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah zai ambace su a wajen wadanda suke wajensa".

Malamai sun yi sharhin Hadisin inda s**a bayyana cewa; Hadisin yana nufin mutane su taru a Masallaci, sashensu yana koyar da sashe, k**ar yadda Alkali Iyadh ya fada, inda ya ce:
"قال القاضى: قد يكون هذا الاجتماع للتعلم بعضهم من بعض، بدليل قوله: "ويتدارسونه بينهم"، ومثل هذا لم ينه عنه مالك ولا غيره".
إكمال المعلم بفوائد مسلم (8/ 195)

Shi kuma al-Dibiy shi ya fito da ma'anar DARASIN ALKUR'ANIN A FILI, inda ya ce:
"و"يتدارسون" شامل لجميع ما يناط بالقرآن من التعليم والتعلم، والتفسير، والاستكشاف عن دقائق معانيه."
شرح المشكاة للطيبي الكاشف عن حقائق السنن (2/ 665)، وانظر: مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح (1/ 287)

Ya ce: "Ma'anar suna Darasinsa" ya kunshi dukkan abin da yake rataye da Alkur'ani na koyarwa da koyo da TAFSIRI, da kuma binciko boyayyun ma'anoninsa".

Kuma wannan bai takaita ga Masallaci kadai ba, k**ar yadda Imam al-Nawawiy ya ce:
"ويلحق بالمسجد في تحصيل هذه الفضيلة الاجتماع فى مدرسة ورباط ونحوهما إن شاء الله تعالى ويدل عليه الحديث الذي بعده فإنه مطلق يتناول جميع المواضع ويكون التقييد في الحديث الأول خرج على الغالب لا سيما في ذلك الزمان فلا يكون له مفهوم يعمل به".
شرح النووي على مسلم (17/ 22)

Saboda haka idan mun lura da wadannan Hadisai guda biyu za mu ga cewa; MUSTAHABBI ne ana haduwa a Masallaci ko wani wajen daban, a cikin watan Ramadhan ana yin Darasin Alkur'ani, har watan ya fita.

Kuma Malaman sun ce: Ma'anar Darasin Alkur'ani shi ne a samu bangarori guda biyu suna karanta Alkur'ani, suna TAFSIRINSA, suna bayanin ma'anoninsa, sauran mutane kuma suna sauraro suna koyon ilimi.

Da wannan muke cewa; Tafsirin Alkur'ani a watan Ramadha yana cikin Addini, kuma Sunnar Annabi (saw) ne, kuma Mustahabbi ne. Aikin lada ne mai girma. Don Allah zai saukar da Mala'iku su kewaye su, kuma nitsuwa za ta sauka a kansu, rahama za ta lullube su.

Wannan shi yake nuna cewa; Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi SUNNA NE BA BIDI'A BA. Ba k**ar Maulidi yake ba, wanda shi kam bidi'a ne da bata mummuna.

* Kun ga dai duka wadannan Malaman da na kawo maganganunsu babu Bawahabiye ko daya.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Kano