Ashiru Rashida

Ashiru Rashida

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ashiru Rashida, .

05/12/2025

A day at the airport

A few days ago, I arrived early for my Abuja to kano flight. While waiting, I went to use the washroom and met an elderly woman who had soiled herself. The cleaner was frustrated, overwhelmed and shouting, while mama looked confused and embarrassed.

I gently reminded the cleaner that some elders struggle with incontinence and don’t even know when it happens. We don’t know people’s stories, and sometimes all they need is patience. I gave her something and begged her to treat mama with kindness.

That moment taught me again: growing old is not a crime. Life is already hard for many elderly people in Nigeria. The least we can do is show them compassion, not ridicule.

We all pray to grow old. So let’s treat our elders the way we want to be treated when our own steps slow down.
Keep your heart soft. Choose empathy. 💛
Harande Alhaj AbubakarEveryone is Included-All People, All Places, All Ways

04/09/2025

Babu mai gujewa tsufa, abin da muka yi wa tsofaffi shi za a yi mana.

20/08/2025

Shin menene matsala, menene mafita? 🤔

Gaskiya tsufa rigace ta kowa babu wanda zai guje mata. Amma abin takaici shine yadda muke barin tsofaffinmu cikin mawuyacin hali. Sau da dama zaka ga tsoho ko tsohuwa suna tsince-tsince a hanya, ko kuma suna tattara ciyawa domin su samu abin amfani.

Amma mu matasa fa?
Maimakon mu yi tunanin gobe, yawanci rayuwarmu ta fi karkata wajen nishadi da sakaci. Matashi zai iya kashe dubu hamsin ko dari a wajen shakatawa, amma idan tsoho ya nemi taimako, sai kawai a miƙa masa ashirin ko hamsin. 😔

Shin wannan adalci ne?
Ko muna manta cewa gobenmu itace yau din tsofaffinmu.
Shin wannan rayuwa ce da zata gina mana al’umma?
Ko muna manta cewa yau da muke ƙarfi gobe za mu zama irin waɗanda muke wucewa ba tare da kulawa ba?

👉 Ku faɗi ra’ayinku: ta yaya zamu gyara wannan halin?
Everyone is Included-All People, All Places, All Ways

20/08/2025

Gaskiya akwai abubuwan da ke daga zuciyata. 😢
Na ga wani tsoho ya tsayar da adaidaita, ya mikawa mai hanya ₦100 ya ce, “Dan Allah, kai ni Hotoro.” Amma mai adaidaita ya ce kudinka ba zai isa ba ya bar shi a nan. Sai wata yar makaranta ta ce, “Babana lafiya?” Tsohon yayi murmushi yace, “Kudin hannuna ne bai isa ba."

Old age is a cloak — today it’s on them, tomorrow it will be on us. 🌿
Let’s show love and kindness to our elders, for even the smallest help can become a big blessing. ❤️

20/08/2025

Gaskiya akwai abubuwan da ke daga min zuciya idan na kalli tsofaffi. Sau da yawa suna cikin yunwa, rashin lafiya ko kadaici, amma idan s**a ganka sai su yi murmushi kamar babu komai. 🌿

Jiya ina kan hanyata zuwa makaranta sai na ga wani tsoho ya tsaya bakin t**i, ya tsayar da adaidaita sahu. Ya mikawa mai adaidaita naira dari 100 cikin tausayi ya ce, “Dan Allah, kai ni Hotoro.”

Amma sai matashin mai adaidaita ya kalli tsohon ya ce, “Baba, wannan ba zai kai ka ba,” ya ja motarsa ya wuce.

Tsohon ya tsaya shiru da zuciya cike da rauni. Sai ga wata karamar yarinya, ba ta wuce shekara goma sha hudu ba, ta tsaya ta ce da shi:
“Babana lafiya? Me yasa ka tsayar da adaidaita amma baka shiga ba?”

Tsohon ya yi mata murmushi mai cike da kauna ya ce:
“’Yar Baba, Hotoro nake son zuwa, amma kudin hannuna bai isa ba.”

Nan zuciyata ta karye, hawaye s**a cika idanuna. 😢

Mu sani tsufa riga ce , yau tana kan wani, gobe tana kanmu. Mu kula da tsofaffinmu, mu basu taimako da kulawa. Ƙanƙanin taimako daga gare mu ka iya zama farin ciki da albarka a gare su. 🌿✨

Culinary Team

Attire

Telephone

Website