DMN Hausa
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from DMN Hausa, Media/News Company, Kano.
DMN Hausa 📰 Gidan jarida ne da zamu rinka kawo muku Labarai masu sahihanci da inganci,Siyasa, Wasanni, Kasuwanci, da abubuwan da suke faruwa a Duniya baki ɗaya Gaskiya kafin komai ✅
Tuna baya 😂😂
07/03/2026
DA ÆŠUMI-ÆŠUMI: An Bawa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi Kyautar Sabuwar Mota
Wani bawan Allah yau Jumma'a a Kaduna ya gabatar da wannan dalleliyar mota ƙirar Toyota Land Cruiser ga Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi a matsayin kyauta ga shehin malamin domin jin daɗin zirga-zirga.
Tuna baya😂😂
A Daren Jiya Ne Atiku Abubakar Ya Ziyarci Malam Nasiru El-rufa'i Jim Kadan Bayan Jami'an Tsaro Sun Yi Yunkurin K**a Shi.
13/02/2026
Jaruma Hadizan Saima Ta Cika Shekaru 34 A Duniya
Jaruma a masana’antar Kannywood, Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadizan Saima, ta cika shekara 34 a Duniya, kamar yadda ta bayyana wa gidan rediyon Kano, Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Hadiza Muhammad ta ce tana da shekara 13 a lokacin da ta fara fim. A yanzu haka ta kwashe shekara 20 tana harkar shirya fina-finan Hausa, wanda hakan ke nuna cewa a wancan lokacin tana da shekaru 33 cif-cif a Duniya.
Wannan na nufin ita sa’a takwarorinta jarumai ne irin su Hadiza Gabon, Fati Washa, Rahma Sadau da Nafisat Abdullahi.
Ta bayyana hakan ne a shekarar da ta gabata, kuma yanzu haka tana da shekaru 34 a Duniya.
Wane fata za ku yi mata.
13/02/2026
Abinda Ya Faru Da Ni Kaddara Ce, Amma Sai Gashi A Krshe Ya Zame Mini Alkairi, Domin A Yanzu Haka Ina Samun Abinda Ba Na Samu A Baya K**a Daga Talluka Da Kuma Fatan Alkhairi, Cewar Malam Bala Dorayi Sarkin Yakin Karyar Kasar Hausa
12/02/2026
TIRKASHI: Abubakar Malam Bala Sarkin yaƙin Karyar Kasar Hausa Ya Karbi Sarautar Da Jama'a S**a Bashi Hannu Bibiyu
Inda Ya Gabatar Da Kansa Da Sunan Sarautar A Yayin Wata Tallar Data Da Ya Yi, Haka Kuma Ya Bude Shafin Tiktok Da Sunan
Me za ku ce?
10/02/2026
A yanzu abinda ake bani na je wa mutum biki miliyan 5 ne.
Amma daga yanzu duk wanda zai gayyace ni nai waka a bikin sa ya tabbatarda ya tanadi miliyan 200
Inji Mawaki Bilal Villa
10/02/2026
Yau ma an ci gaba da zanga-zangar nan ta neman a watsa sakamakon zaɓen 2027 ta intanet, inda a yau tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ke jagoranta wanda a yanzu haka ke gudana a babbar mashigar Majalisar Tarayya a Abuja.
Shin kuna goyon bayan wannan ƙudiri?
09/02/2026
DA ƊUMI-ƊUMI: Sheikh Guruntum ya musuluntar da wani maigari tare da jama'arsa mutum tamanin a wani ƙauye ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi.
Maigarn ya canza suna zuwa Abdulrahman inda ya bada tabbacin shiga tawagar masu yaɗa da'awar Musulunci domin ya shigar da su ƙauyukan waɗanda ba musulmai ba don a musuluntar da su.
Allah ya tabbatar da duga-dugansu kan Musulunci da sunnar Manzon Allah SAW.
Click here to claim your Sponsored Listing.