AMR Hausa

AMR Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AMR Hausa, Journalist, Zawachiki, Kano.

An kirkir wannan shafi na AMR Hausa don sanar da ku halin da Duniya ta ke ciki, ta hanyar samar muku da sahihan Labarai da Rahotoni a gida Nigeria da Afrika da sauran sassan Duniya.

18/05/2026

‘Yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kai wani sabon hari kan ƙauyukan da ke yammacin garin Musawa a Jihar Katsina, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa daga gidajensu yayin da maharan s**a yi awon gaba da dimbin dabbobi.

An kai harin ne a ranar Lahadi, kamar yadda wani masani kan harkokin tsaro da rahoton rikice-rikice a Arewa maso Yamma, Bakatsine, ya tabbatar a wani sako da ya wallafa a shafin X.

Rahotanni sun ce harin ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargaba, yayin da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da satar dabbobi ke ci gaba da addabar wasu sassan jihar Katsina da ma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.

18/05/2026

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da kuma ƴan ta’adda suna aikata hakan ne saboda neman kuɗaɗen da za su kare kansu daga matsin lambar gwamnati.

Gumi ya yi wannan furuci ne yayin da yake magana kan matsalar tsaro da ta addabi wasu sassan Najeriya, inda ya ce matsin da gwamnati ke lallaba musu yana sa su neman hanyoyin samun kuɗi domin ci gaba da rayuwa da kare kansu.

Sai dai kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan Najeriya, inda wasu ke ganin kamar yana ƙoƙarin kare ayyukan ƴan bindiga da masu tada ƙayar baya, yayin da wasu kuma s**a ce yana ƙoƙarin bayyana tushen matsalar ne domin a samo mafita mai ɗorewa.

18/05/2026

Gwamnatin ƙasar Ethiopia ta ƙulla haɗin gwiwa da Dangote Group domin gina katafaren kamfanin samar da taki a garin Gode, a wani mataki na bunƙasa harkar noma da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje

Rahotanni sun bayyana cewa sabon kamfanin zai riƙa samar da tan miliyan uku na taki a duk shekara, lamarin da ake ganin zai taimaka wajen ƙarfafa samar da abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin Habasha.

Aikin na daga cikin manyan jarin masana’antu a fannin noma da aka taɓa saka a ƙasar, inda ake sa ran zai samar da guraben ayyukan yi da kuma ƙara wa manoma sauƙin samun taki a farashi mai rahusa.

Masana sun bayyana cewa haɗin gwiwar zai ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Habasha da Najeriya, tare da bai wa yankin Afrika damar ƙara dogaro da masana’antun cikin gida.

18/05/2026

Jam’iyyar PDP za ta tantance tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a ranar Talata a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya na jam’iyyar domin zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ne ya sanar da hakan, inda s**a ce Jonathan ne kaɗai ya nuna sha’awar neman tikitin takarar shugaban ƙasa a cikin tsarin tantancewar da ake yi yanzu.

Haka kuma, ana zargin wasu ƙungiyoyin magoya baya sun fara haɗa kuɗaɗe domin sayen fom ɗin takara ga Jonathan, lamarin da ya ƙara janyo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar komawarsa siyasa bayan barinsa mulki a shekarar 2015.

Sai dai har yanzu Jonathan bai fito fili ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.

18/05/2026

Bayan da aka gaza cimma matsaya ta hanyar sulhu a mafi yawan jihohin Najeriya, magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki sun fara gudanar da zaɓukan fidda gwani ta hanyar kaɗa ƙuri’a domin tantance waɗanda za su tsaya takara.

A wasu jihohi dai an samu rahotannin ce-ce-ku-ce da zarge-zargen rashin adalci daga ɓangarorin wasu ‘yan takara, yayin da a wasu wurare aka gudanar da zaɓen cikin lumana.

Ana sa ran sakamakon zaɓukan zai bayyana waɗanda za su wakilci jam’iyyar APC a zaɓukan da ke tafe.

17/05/2026

Ɗan Majalisar Jigawa Mafi Daɗewa a Kujera Ya Rasa Tikitin APC Bayan Shekaru 16

Wani babban sauyi na siyasa na ci gaba da bayyana a Jihar Jigawa bayan da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Miga/Kaugama, Hon. Sa’idu Yusuf Miga, ya rasa tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

Hon. Miga, wanda ya shafe shekaru 16 yana wakiltar mazabarsa a Majalisar Tarayya, ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisar da s**a fi daɗewa a kujerarsu a jihar ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Rashin samun tikitin nasa na zuwa ne yayin da ake ganin ana samun manyan sauye-sauye da sauyin fuska a siyasar jihar kafin babban zaɓen 2027.

Photos from AMR Hausa's post 17/05/2026

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wasu 'yan Kannywood biyu mace da namiji

Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da jaruman masana'ntar shirya finafinai ta Kannywood biyu, Adam Garba (Raba-Gardama) da Amina Uba Hassan (wadda tsohuwar matar jarumi Adam A. Zango ce), daga gudanar da harkokin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun jami'in hulda da jama'a Abubakar Sani ta ce an ɗauki matakin ne bayan bayyanar jaruman biyu a wani bidiyo da ta bayyana a matsayin wanda ya saɓa da tarbiyya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano.

16/05/2026

YANZU-YANZU: Yusuf Buhari Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani Na Kujerar Majalisar Tarayya Ta Sandamu, Daura Da Mai’adua

Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu, Daura da Mai’adua.

A sakamakon zaɓen, Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 5,849, inda ya kayar da abokin takararsa Hon. Auwal Lawal Daura, wanda ya samu ƙuri’u 21 rak.

Nasarar tasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓukan 2027 a jihar Katsina.
Daga Mutawakkil Gambo Doko

15/05/2026

Akalla mutane sama da 100 ne s**a rasa rayukansu sakamakon wata mummunar guguwa mai ƙarfi da ta haɗa da ruwan sama da walƙiya a wasu sassan ƙasar India.

15/05/2026

Atiku Abubakar ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da su gaggauta sakin Nasir El-Rufai kafin bikin Babbar Sallah.

Rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya bayyana ci gaba da tsare El-Rufai a matsayin abin takaici da kuma rashin adalci, musamman a lokacin da al’ummar Musulmi ke shirin gudanar da bukukuwan Sallah.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Juma’a, Atiku ya ce bai dace gwamnati ta yi amfani da iko wajen takura wa abokan hamayyar siyasa ba.

Ya kara da cewa duk da bambancin siyasa, El-Rufai cikakken dan Najeriya ne wanda kundin tsarin mulki ya ba shi hakkokin walwala da adalci, tare da bukatar a bi ka’ida kafin daukar wani mataki a kansa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin Kaduna su fito su bayyana dalilin tsare El-Rufai idan akwai wata sahihiyar shari’a a kansa.

Atiku ya gargadi hukumomi cewa ci gaba da tsare shi ba tare da cikakken bayani ba na iya kara tayar da damuwa kan yanayin dimokuradiyya da kare hakkin bil’adama a Najeriya.

Ya ce lokacin Sallah lokaci ne na tausayi, yafiya da hadin kai, saboda haka ya kamata a bai wa El-Rufai damar kasancewa tare da iyalansa idan babu wata hujja ta doka da ke hana hakan.

15/05/2026

Part 7

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

Zawachiki
Kano
110001