IMACS TV
IMAMU AHMAD CENTER FOR STUDIES TV
26/02/2026
Lokutan buÉ—a baki da sahur a jihar Kano.
Daga IMACS TV/RADIO đź“»
26/02/2026
Shugaba Tinubu ya tsawaita haramcin fitar da man kadanya har zuwa 2027
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsawaita haramcin fitar da man kade na karin shekara guda, daga 26 ga Fabrairu 2026 zuwa 25 ga Fabrairu 2027, a wani mataki na karfafa sarrafa kayayyaki a gida da bunkasa masana’antu.
Sanarwar da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce matakin na da nufin kara karfin sarrafa shea butter a Nijeriya, inganta rayuwar al’ummomin da ke noma shi, da kuma kara darajar kayayyakin da ake fitarwa.
26/02/2026
Da Dumi-Dumi
DSS sun saki Walida
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karbi Walida Abdulhadi Ibrahim, yarinyar da aka ce ta bace daga jihar, wadda ta kasance a hannun jami’an DSS.
Gwamnan ya bayyana cewa dukkan batutuwan da s**a shafi zargin sace ta za su bi hanyar doka, yana mai jaddada cewa kotuna ne za su yanke hukunci kan lamarin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a tabbatar da adalci, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati za ta bar doka ta yi aikinta yadda ya kamata.
26/02/2026
YANZU YANZU | Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya SaudiAirlines zai sake fara zirga-zirga daga Jeddah zuwa Abuja a watan Yuni, ko kuma zuwa watan Janairu na shekarar 2027".
Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Yousef Bin Muhammed Al-Balawi, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Ministan YaÉ—a Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a ranar Laraba, a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce dawowar wannan zirga-zirgar jiragen sama za ta ƙara sauƙaƙa tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da Saudiyya, tare da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
đź“· Ma'aikatar yada labarai.
26/02/2026
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano
IMAMUAHMADCENTERFORSTUDIES6