Kabir Isa Muhammad

Kabir Isa Muhammad

Share

A Computer Scientist, Marriage Counsellor, Societal Analyst

Dealers of all kinds of Cosmetics, Earrings, Necklaces, Bracelets, Anklets, Blouses, Underwears, Arabic and English Wears, Bags, Shoes, Bedsheets, Nets, Curtains, Carpets, Fabrics, Textiles and Materials, Baby Cares etc.

28/05/2025

Nothing ventured nothing gained

23/05/2023

Ƙoƙarin inganta rayuwar ka shi ne dagewar ka da jajircewar ka wajen tabbatar da cimma ginshiƙan manufofin ka masu kyau...

Lalle ka zama mai juriya da dakiya kan wahalhalu da tsananin da ka iya bujuro maka kan hanyar ka.

24/01/2023

A good leader always chooses mercy, for our Prophet chooses only the easiest as simplicity is the basis of the religion & kindness beautify everything

04/01/2023

MOTOCI HAR 100 A KOWACCE ƘARAMAR HUKUMA A IYA KANO!

Lalle! Ta ina zaka tunanin wani aiki in ya ci zaɓe, bayan hannun jari ya sanya na kasuwanci?

Jama'a dai jikin kowa ya faɗa masa kuma ya gaya masa yadda ba sai wani ya ja kunnen ku ba, kar a zo a baka wasu ƴan kuɗaɗe ƙalilan da ko karin kumallon safe ba zasu ishe ka ba, ka zaɓi ƴan jari hujja, ƴan ko me zai bayar sai nayi mulki, sannan ka tsammaci zaka da kyau a mulkin gobe, ka san yadda komai ya tashi, ya nunnuka kuɗin shi, farashin komai kullum gaba yake, abubuwan da an fi ƙarfin su yanzu sun fi ƙarfin ka faufau, babu abin da bai birkice ba, bai rikice ba, bai hargitse ba, hatta ƙarfin imanin mutane sai da aka ɓata shi, aka lalata shi.

In kunne yaji, jiki ya tsira!

In an ƙi ji, ba a ƙi gani ba, in an gani, ba a ƙi gani ba...

MUMINI dai ba a cizon shi sau biyu a rami guda...

Duk wanda yayi kuskuren zaɓar wanda bai dace ba, ya san duk wahala da wuyar da za a sha a nan gaba, sai Allah ya tambaye shi kan hujjar zaɓar wanda bai cancanta ba.

Photos from Kabir Isa Muhammad's post 12/09/2022
08/08/2022

WA KEDA HAƘƘIN KISAN SAYYIDUNA HUSAINI (R.A.)?

GAƁA TA FARKO (1):

TAMBAYA:
Su waye haƙiƙanin waɗanda s**a kashe Sayyiduna Husaini (R.A.)?

A shekara ta 60H bayan Hijra aka yiwa Yazidu ɗan Mu'awiyah caffa (mubaya'a) a matsayin Shugaban Musulmi gaba ɗaya bisa nusarwar Mahaifin shi Mu'awiyah (R.A.), wanda wasu ke ganin ba shi ya kamata ba, har suna ƙirga hakan daga kuskuren shi wannan Babban Sahabi wato Mu'awiyah ɗan Abu Sufyan (R.A.), saboda ya ƙetare wasu manyan mutane cikin Iyalan Gidan Ma'aikin Allah da Sahabbansa (R.A.), kuma shi Yazidu ɗin ba wani mutum ne mai nagarta ta azo a gani ba. Lokacin Yazidu yana ɗan shekaru 34. An samu wasu da s**a ƙi yi masa mubaya'a kamar Sayyiduna Husaini bin Aliyu bin Abu Ɗalib (R.A.) da Sayyiduna Abdullahi bin Az-Zubayr (R.A.), wanda dukkan su sun kasance a can Madinah.

Da labari ya kai ga mutanen Iraƙi na Sayyiduna Husaini (R.A.) bai yi mubaya'a ga Yazidu ba, su kuwa daman sun yi fice wajen basu buƙatar wani a shugabanci in ba Sayyiduna Ali da ƴaƴan sa ba (R.A.). Sai su kayi ta yin wasiƙu zuwa ga Sayyiduna Husaini (R.A.) dukkan na sanar da shi cewa:

"Tabbas, mun maka mubaya'a, domin ba mu riga mun ɗaurawa kan mu yin mubaya'a ga Yazidu ba, mubaya'armu taka ce kai kaɗai. Wasiƙu su kayi ta yawaita har adadin ya haura sama da wasiƙa 500, a lokacin ne Sayyiduna Husaini (R.A.) ya aika ɗan Baffan shi mai suna Muslim ɗan Aƙil ɗan Abu Ɗalib (R.A.) domin bin diddigin lamuran a can ɗin, kuma domin ya san haƙiƙanin lamarin da yadda yake a zahiri, yayin da Muslim ɗan Aƙil ya isa Kufa, sai ya shiga tambayar mutànen gari har dai ya samu tabbacin mutanen wajen basu buƙatar Yazidu, Husaini ɗan Ali (R.A.) kaɗai kawai suke yi, sai ya sauka a wajen wani mai suna Háni'u ɗan Urwah, mutane fa su kayi ta zuwa ɗaya-ɗaya, tawaga-tawaga suna yi masa mubaya'a a madadin Sayyiduna Husaini (R.A.), lokacin Nu'uman ɗan Bashir shi ne Sarki a Kufa, sai dai bai wani huɓɓasa ba wajen daƙile abin da ke gudana na lamarin Muslim ɗan Aƙil ba. Sai Yazidu ya cire ya maye gurbin sa da Ubaidullahi ɗan Ziyád.
Ubaidullahi ɗan Ziyád ya iso garin Kufa cikin ɓadda bami, har mutane s**a kasance suna yi masa zaton Sayyiduna Husaini (R.A.). Lokacin da ya isa fada, sai ya aika bararren bawan sa mai suna Ma'aƙil domin ya lalubo masa labarin lamarin kuma ya gano masa wane ke ja gaba wajen jagoranci lamarin; sai ya tafi bisa ƙaryata shi mutum ne daga Hims, kuma shi ɗin yazo da Dinare 3000 don ƙarfafar Sayyiduna Husaini (R.A.), yayi ta kai shige da fice, kai komo, jeka dawo, har sai da ya san duk irin shirye-shirye dake tare dasu, sai daga bisani ya dawo zuwa ga Ubaidullahi ɗan Ziyád bayan ya gama leƙen ashirin ya kabbarta masa komai.
Kuma tuni lokacin Muslim ɗan Aƙil ya aikawa Sayyiduna Husaini (R.A.) da ya taho, sai Sayyiduna Husaini (R.A.) ya haɗa guzirin ya fito Ranar Tarwiyya (8 ga watan Zul Hijja). Ubaidullahi ɗan Ziyád kuwa yana da masaniyar abin da Muslim ɗan Aƙil yayi na gayyato Sayyiduna Husaini (R.A.), sai yace: A kira masa Háni'u ɗan Urwah - wato wanda Muslim ya sauka wajen sa -, sai aka zo da shi, sai ya tambaye shi: "Ina Muslim ɗan Aƙil?" Sai yace, "Ban sani ba". Sai ya ƙwallawa yaron shi Ma'aƙil kira, da ya shigo wajen shi, sai yace dashi: "Ka san shi?" Sai amsa "Eh" take sai (Ma'aƙil) ya faɗi a gaban sa, nan fa (Háni'u) ya gane makirci ne fa daga Ubaidullahi ɗan Ziyád, sa'in nan Ubaidullahi ɗan Ziyád yace dashi: "Ina Muslim ɗan Aƙil?" Sai ya bashi amsa da cewa: "Wallahi, ko da ya kasance a ƙarƙashin ƙafa ta, ba zan ɗaya taba," sai Ubaidullahi ɗan Ziyád ya make shi, yayi umarni da a tsare shi..

Da labari ya isa ga Muslim ɗan Aƙil, sai ya fito da tawagar mayaƙa 4000 s**a kewaye s**a mamaye gidan Ubaidullahi ɗan Ziyád, duk mutanen s**a fita suna marawa shi (Muslim) baya, sai dai fa manyan gari suna tare da Ubaidullahi ɗan Ziyád, nan fa yace dasu kuje kuyi ƙoƙarin sanya mutanen ku su kwayewa Muslim ɗan Aƙil baya, na muku alƙawarin manya-manyan kyaututtuka, sannan ya razana su da rundunar da zata taso daga Sham, sai masu madafun ikon gari s**a yi ta sa mutanen su suna kwayewa da yayewa gabarin Muslim ɗan Aƙil, har sai da ya dawo babu wanda yayi saura tare dashi sai mutane 30 daga cikin mutane 4000, ranar wannan wuni bata faɗi ba, har sai da takai Muslim ɗan Aƙil shi kaɗai ya rage, duk mutane sun kwaye masa, ya wanzu shi kaɗai yana tafiya cikin titunan Kufa, bai san ina zai je ba, sai ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan wata mata ƴar Kinda yace da ita: Ina buƙatar ruwa, sai tayi mamakin shi tace dashi, waye kuma kai, sai yace da ita, Ni ne Muslim ɗan Aƙil, ya kwashe labari ya bata duka, na mutane sun kwaye masa baya, sai ta ajje shi wani gida ɗaki dake maƙwabtaka da ita, ta aiko masa da ruwa da abinci, sai dai fa ɗan ta ya tashi yake ya faɗawa Ubaidullahi ɗan Ziyád wajen da ya ɓuya, sai ya aiko masa da mutane 70 s**a mamaye shi, ya fito ya yaƙe su, amma dai a ƙarshe ya miƙa musu kan shi bayan sun mishi alƙawarin amintar dashi, sai s**a tafi dashi zuwa fadar sarauta.
Yayin da s**a isa, sai Ubaidullahi ɗan Ziyád ya tambaye shi: Me ne sababin fitowar ka wannan? Sai ya bada amsa: Mubaya'a ce a wuyan mu da muka yiwa Husaini ɗan Ali (R.A.). Sai yace dashi: Babu mubaya'ar Yazidu ke nan a wuyan ka? Ai kuwa kashe ka zan yi. Sai (Muslim) yace: Bari zan yi wasiyya. Sai yace: Na'am, yi wasiyyar ka. Sai (Muslim) ya hanga, sai ya hangi Umar ɗan Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas, sai yace dashi: "Kai ne mafi kusancin mutane zumunci gare ni, matso na baka wasiyya, sai ya bashi jikin garu yayi masa wasiyyar lalle ya aikawa Sayyiduna Husaini (R.A.) da ya koma, sai Umar ɗan Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas ya aika wani mutum domin ya sanar da Sayyiduna Husaini (R.A.) cewa lamari fa ya wuce, kuma haƙiƙa mutanen Kufa sun yaudare shi. Nan fa Muslim ɗan Aƙil ya daɗi shahararriyar maganar sa: "Ka koma da iyalanka, kar ka ruɗu da mutanen Kufa, domin tabbas mutanen Kufa ƙarya s**a kuma ƙarya nima s**a mini, maƙaryaci kuwa bai da tsayayyen ra'ayi".
Nan aka kashe Muslim ɗan Aƙil a Ranar Arfa, wanda Sayyiduna Husaini (R.A.) ya riga ya fito Ranar Tarwiyya, gabanin kashe Muslim ɗan Aƙil da kwana guda.

Wannan sune ƴan shiga da'awar son masu Iyalan Gidan Ma'aikin Allah (S.A.W.)

Zamu ci gaba a gaɓa ta 2 in Allah ya yarda.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Medile, Hamdala Science College Street, Kumbotso LGA
Kano
700104