VON Hausa

VON Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from VON Hausa, News & Media Website, Kano.

Kafar yada labarai mai zaman kanta, tana kawo labarai kai tsaye daga Arewacin Najeriya zuwa duniya - VON Hausa Muryar Arewa

Zaku iya samun mu ta Whatsapp: 08104257364

04/05/2026

Tsohon dan takarar majalisar tarayya na Kano Municipal Engr. Yusuf Da’awah, ya fice daga jam'iyyar ADC zuwa NDC tare da Sanata Kwankwaso.

04/05/2026

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, zai rantsar da mataimakinsa, Honarabul Murtala Sule Garo, a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.

A cewar wata sanarwa da Ibrahim Adam, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, za a gudanar da bikin rantsuwar ne da ƙarfe 11 na safe a zauren taro na Coronation Hall da ke fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Ana sa ran manyan jami’an gwamnati, shugabannin jam’iyya da sauran manyan baki za su halarci bikin rantsuwar.

04/05/2026

Tsohon Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali, ya ki amincewa da zabin ’yan takara ta hanyar yarjejeniya da Jam’iyyar APC ta yi a Jihar Gombe.

04/05/2026

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar katin shaidar zama ɗan jam’iyyar a Abuja.

Matakin nasa na zuwa ne bayan ya fice daga jam’iyyar ADC, sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar, wanda Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kai a makon da ya gabata.

04/05/2026

Tsohon shugaban ma'aikatan Jahar Kano Alh Abdullahi Musa ya fice daga jam'iyyar ADC.

Photos from VON Hausa's post 03/05/2026

Kai tsaye daga fadar Gwamnatin jahar Kano yayin da ake cigaba da Zaman Sulhu tsakanin yan takarar karin Majalisar tarayya dana jahohi.

03/05/2026

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun koma sabuwar jam’iyyar NDC, ƙasa da sa’o’i 24 bayan sanar da ficewarsu daga jam’iyyar ADC.

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Anambra sun karɓi katin shaidar zama mambobin jam’iyyar ne a ranar Lahadi a sakatariyar NDC da ke Abuja.

Kwankwaso da Obi dai na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya da s**a fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, inda Kwankwaso ya tsaya takara karkashin jam’iyyar NNPP, yayin da Obi ya tsaya a LP.

Sai dai daga bisani dukkansu sun fice daga jam’iyyunsu sakamakon rikice-rikicen cikin gida da s**a dabaibaye su.

Bayan haka sun shiga ADC, amma rikicin shugabanci da matsalolin shari’a da s**a kunno kai a cikin jam’iyyar ne s**a sa s**a sake ficewa.

Shigarsu NDC na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaɓen ƙasa mai zuwa.

03/05/2026

Da Dumi Dumi: Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya koma jam’iyyar NDC a hukumance tare da karɓar katin zama mamba.

Sauya shekar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa da kuma haɗakar jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

03/05/2026

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana matsayar tasa ne a wani sako daya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya bukaci shugaban ksa Bola Ahmed Tinubu ya soke masalahar fidda dan takarar gwamna a jihar Gombe.

Photos from VON Hausa's post 03/05/2026

Tirkashi Babban Aiki: Karamar hukumar Dawakin Tofa, da Rimin Gado, Sun hallara a kotun Gwamnatin Kano Domin yaken Hukunci wazai Jagorancin yankin a Majilisar Tarayya da ta jaha, ɗaya daga cikin yankunan da siyasarsa ta fi ɗaukar ɗumi sun.

Mekuke Tunanin Zai faru?

03/05/2026

Bidiyon Yadda Jam'iyyar APC a jihar Gombe ta ajiye Professor Ibrahim Pantami a gefe, ta amince da Jamilu Ishiyaku a matsayin dan takararta na gwamna da ta cimma maslaha kansa a zaben 2027.

Photos from VON Hausa's post 03/05/2026

Alhazan rukuni na farko daga Jihar Kebbi sun fara hawa jirgin sama domin tafiya ƙasar Saudiyya, inda za su gudanar da aikin Hajji — ɗaya daga cikin muhimman rukunnan addinin Musulunci.

Tashin nasu na zuwa ne a cikin tsarin shirye-shiryen Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar, wadda ta tabbatar da cewa an kammala dukkan matakan tashi lafiya, tare da tantance takardun mahajjata da kuma ba su shawarwari kafin tafiya.

Hukumomi sun yi kira ga alhazan da su kiyaye dokoki da ka’idojin ƙasar Saudiyya, tare da yin addu’a domin samun aikin Hajji karɓaɓɓe.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Kano