Yunusa Rabiu Tahir
Allah yasa aljanna makomarmu
Alhamdulillah
19/08/2025
WALE EDUN, DAKE SHUGABANTAR KUNGIYAR SHIRIN TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA, YA GANA DA GWAMNAN BABBAN BANKIN NAJERIYA DON KARFAFA HADIN GWIWAR TSARE-TSAREN KUDI DANA KASAFI
Mai Girma Ministan Kudi da kula da tattalin arzikin ƙasa, Mista Wale Edun, wanda shi ne kuma shugaban Ƙungiyar Shirye-shiryen Tattalin Arzikin Ƙasa, a yau ya gudanar da muhimmin taro tare da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dakta Olayemi Cardoso, a Hedikwatar CBN dake Abuja. Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS), Dakta Zacch Adedeji, shi ma ya halarci taron.
Wannan tattaunawar ta matakin koli ta nuna muhimmancin daidaita manufofin kudi da na kasafi a ƙarƙashin jagorancin Edun domin tabbatar da zaman lafiyar tattalin arziki, ƙarfafa gwiwar masu zuba jari, da kuma hanzarta cigaban dake karkashin jagorancin masu zaman kansu.
Mista Edun ya jaddada cewa, hadin kai tsakanin hukumomin kula da kudade dana kasafin kudi nada matuƙar muhimmanci wajen aiwatar da shirin gyaran tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, wanda ke tabbatar da cewa an takaita hauhawar farashi, an tara kudaden shiga yadda ya kamata, kuma rancen kudi yana tafiya yadda ya dace zuwa sassan tattalin arzikin dake samar da aiki daci gaba.
19/08/2025
Kungiyar GEPIn Ta Yabi Ministan Kuɗi, Wale Edun, Bisa Ƙarfafa Daidaiton Kuɗin Ƙasar Najeriya
Kungiyar Global Economic Policy Initiative (GEPIn) ta yaba wa Mai Girma Ministan Harkokin Kuɗi da Daidaita Tattalin Arzikin Ƙasa, Mista Wale Edun, bisa ci gaban da aka samu wajen daidaita tattalin arzikin Najeriya a ƙarƙashin jagorancinsa.
Da yake jawabi a madadin ƙungiyar, jagoranta, Mista Bernard Okri, ya bayyana cewa biyan bashin fiye da naira tiriliyan 2 na kuɗaɗen kasafin kuɗin manyan ayyuka da s**a rage daga shekarar 2024 na nuna jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen dawo da sahihancin kuɗi, ƙarfafa amincewar masu zuba jari, da tabbatar da ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a fadin ƙasar.
A cewar GEPIn, wannan matakin ya riga ya fara haifar da sakamako mai kyau.
“Ta hanyar biyan waɗannan bashin, Gwamnatin Tarayya ta rage wa ‘yan kwangila da masu ba da kuɗin ayyuka nauyin da ke kansu, wanda hakan ke ƙarfafa sabon kuzari a ayyukan gina muhimman abubuwan more rayuwa, faɗaɗa damar samar da ayyukan yi, da kuma tallafawa shirin bunƙasar tattalin arzikin gwamnatin nan.”
Kungiyar ta kuma yaba da ƙarin ingancin kuɗin jihohi, inda ta ce ragowar kuɗin jihohi ya ƙaru daga naira tiriliyan 2.8 a shekarar 2023 zuwa naira tiriliyan 7.1. Wannan, a cewar GEPIn, zai ba jihohi damar amfani da ƙarin kuɗaɗen wajen zuba jari a sassa muhimmai kamar gine-gine, kiwon lafiya, da ilimi – waɗanda kai tsaye ke inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
“Waɗannan gyare-gyaren na nuna tsari mai ƙa’ida wajen tafiyar da kuɗin gwamnati da kuma bin manufofi da ke ɗan-dan daidaita tattalin arzikin ƙasa,” in ji Mista Okri. “Mun yi imani cewa idan aka ci gaba da wannan tafiya, ba wai kawai zai hanzarta murmurewar tattalin arziki ba ne, har ma zai samar da ginshiƙin da ya fi ƙarfi don bunƙasar da ta shafi kowa da kowa a fadin ƙasa.”
GEPIn ta ƙara kira ga masu ruwa da tsaki da su ba da goyon baya ga ci gaba da gyare-gyaren gwamnatin tarayya, tana mai jaddada cewa haɗin kai ya zama wajibi domin a maida ribar tattalin arziki ta yi tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.
“Kwakwanso will not join the APC unless Tinubu resolves the Emirate issue in Kano… Inji Buba Galadima
Salon da s**ayi lokacin shari'ar zabe 😂😂
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano Outlying