KAFUR POST

KAFUR POST

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KAFUR POST, Grocers, KAFUR Road, Kafur.

15/05/2026

‎Bari ku ji abinda gwamnan jihar Ogun yayi. Ranar 6 ga watan May (yau kwana 8 kenan), Gwamnan jihar wato Dapo Abiodun ya ƙaddamar da buɗe sabon gidan wutar lantarki mallakin jihar mai ƙarfin Megawatt 4 a cikin garin Abeokuta wanda zai ke amfani da iskar Gas (wato Gas-fired independent Power Plant), sannan ya sake ƙaddamar da Onijanganjangan Self-sufficient Energy Plant mai ƙarfin 34 Megawatt wanda baki ɗaya ya miƙa ragamar kula da wuraren a hannun Ogun State Electricity Regulatory Commission. Dan ka gane karatun yadda ya k**ata, a dunƙule ina nufin gwamnatin jihar Ogun ta ƙaddamar da personal wurin samar da wutar lantarki mai ƙarfin 38 Megawatt wanda zai ke samarwa da jihar wutar lantarki 24/7 kai tsaye zuwa gidajen al'ummar jihar only banda kamfanoni. Idan baka gane ya ƙarfin 38 Megawatt yake ba, to ana nufin duk 1 Megawatt zata iya ɗaukar lodin duk wani electrical appliances na a ƙalla gidaje 1,800 tun daga kan Firji, TV, AC, dutsen guga, heater, fanka da ƙwayaye💡 iri daban-daban. Chairman gidaje 1,800 fa ba mutane 1,800 ba ake nufi ya k**ata ka san wannan 😒. Duk inda ka samu gidaje 1,800, a ƙalla za ka iya samun mutane dubu 250 averagely.

‎Wannan wutar lantarkin fa da ya samarwa jihar sa, still yanzu haka akwai sabon Private Generation Station na wutar lantarki wanda baban Devido yake ginawa a jihar wanda a ƙarshen shekarar nan za'a buɗe shi. Still kuma daman jihar Ogun ɗin tana da Papalanto Generation Station ƙarƙashin kulawar Niger Delta Power Holdings Company wanda yake samarwa da Nigeria wutar lantarki mai ƙarfin 754 Megawatt. Dalilin waɗannan wuraren samar da wutar lantarkin ne yasa jihar Ogun yanzu haka ita ce jiha ta biyu a yawan kamfanoni a Nigeria idan ka ɗauke jihar Lagos. A dunƙule dai, a yayin da wasu jihohin suke ta gogayya wajen ganin sun samarwa kansu abubuwan dogaro da kai saboda al'ummar su su zama purely independent, mu kuwa idan ka shigo jihohin mu daga auren zawarawa sai rabon abinci da tabarmi sannan a gayyaci Rarara da su Ado Gwanja da

15/05/2026

The federal representative for the Malumfashi/Kafur Federal Constituency in the Nigerian House of Representatives is Hon. Muhammad Ibrahim

(also known as Aminu Ibrahim Kafur). He is a member of the All Progressives Congress (APC) and currently serves in the 10th National Assembly as the Vice Chairman of the House Committee on Banking Institutions.You can find official contact information and track his legislative activities via the National Assembly of Nigeria or look up his detailed legislative profile on the ShineYourEye platform.

For additional information on his office, constituent services, or local state representatives in the Katsina State House of Assembly,

you can visit the official Katsina State Government portal.

11/05/2026

Karku Yarda su Wolakanta ku Don Kunyi magana akan su kutai kutu Idan sun kai ku kuyi Magana da hujja ku kiyayi cin mutumci ku sharrin ku kazafi.

28/03/2026

Marigayi Umaru Musa Yar’Adua: “The Servant Leader” — Shugaban Da Ya Zama Misalin Gaskiya Da Rikon Amana

Shin kun san cewa Umaru Musa Yar’Adua shi ne shugaban kasa na farko a tarihin Najeriya da ya fito fili ya bayyana dukkan kadarorinsa (Asset Declaration) kafin ya hau mulki?

Wannan ya nuna cewa a wajensa, shugabanci ba hanyar tara dukiya ba ce, illa hanya ce ta hidimtawa talakawa.

An haife shi ranar 16 ga Agusta, 1951 a jihar Katsina. Kafin shiga siyasa, malamin jami’a ne (Lecturer), abin da ya ba shi nutsuwa, hakuri da zurfin tunani wajen jagoranci.

Abubuwan Da S**a Bambanta Mulkinsa

Ya mayar da hankali kan:

Wutar lantarki

Harkar noma

Tsaro da gyaran kasa

Shi ne shugaban Najeriya na farko da ya amince a fili cewa zaben da ya kawo shi mulki yana da kura-kurai, sannan ya yi alkawarin gyara tsarin zabe.

Zaman Lafiya a Neja-Delta

Maimakon amfani da karfin soja, Yar’Adua ya bullo da shirin afuwa (Amnesty Programme) ga matasan Neja-Delta.
Ya ba su damar koyon sana’o’i da samun sabuwar rayuwa.

Sak**akon haka:

Fasa bututun mai ya ragu sosai

Samar da mai ya karu

Tattalin arzikin kasa ya fara farfadowa

Shugaban Mai Bin Doka

A lokacin mulkinsa:

Gwamnati tana mutunta hukuncin kotu.

Ya amince a saki kudaden kananan hukumomin Legas bisa umarnin kotu, yana mai cewa doka ta fi kowa.

Wannan ne ya sa aka rika kiransa: Shugaban Mai Bin Doka.

Rasuwarsa

Bayan fama da rashin lafiya, ya rasu a ranar 5 ga wanan Mayun Shekarar 2010, yayin da yake kan mulki. Rasuwarsa ta jefa Najeriya cikin jimami, kuma har yau ana tuna mulkinsa (2007–2010) a matsayin lokaci na gaskiya da kankan da kai.

Kalmar Da Yake Fada Akoda Yaushe Itace Ni Servant Leader Ne

Ina kiran kaina Servant Leader ne saboda ni ma’aikacin talakawa ne, ba ubangidansu ba.

Har yau, mutane da dama suna kallon Yar’Adua a matsayin shugaba mai gaskiya, tawali’u da bin doka.

Kai fa, wane abu ne ka fi tunawa da mulkin Yar’Adua? Ka rubuta ra’ayinka a comment.

27/03/2026

Indai abu zai hada da cin mutunchi wani ko wulakaci da tozarchi ga wani dan Allah kar asakani a ciki, bazan iya ba.

09/03/2026

YANZU-YANZU: Iran ta ƙara kai harin makami kan Isra’ila, Amurka da ƙasashen Gulf yayin rikici mai tsanani a Gabas ta Tsakiya.

Majiya Zuhair Ali Ibraheem II

09/03/2026
15/08/2025

Abun takaici. Babu ilmin addini babu na boko. An dauki Mugun makami anbawa jahili. Ya Allah Ka karya mana wadannan mutanen su da masu Goya musu Baya

Photos from KAFUR POST's post 06/08/2025

Jami’an Tsaro Sun K**a Wani da Ake Zargi da Kai Kayan Tallafi ga Boko Haram a Maiduguri

Dakarun Operation Hadin Kai tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na CJTF sun k**a wani mutum mai suna Ahmadu Mohammed Dogo, bisa zargin cewa yana safarar kayan tallafi zuwa wuraren da ’yan Boko Haram ke buya a jihar Borno.

An k**a wanda ake zargin ne a Maiduguri yayin da yake ƙoƙarin safarar man fetur da ya ɓoye a cikin kwalaben abin sha, da nufin kaiwa yankin Gamboru-Ngala, wani yanki da ake dangantawa da ƙungiyar Boko Haram.

Rahotannin sun bayyana cewa an k**a shi ne bisa bayanan sirri da aka samu, kuma binciken farko ya nuna cewa man da yake ɗauke da shi, ana shirin kai shi ne zuwa wani sansanin ’yan ta’adda.

Yanzu haka wanda ake zargin yana tsare a hannun hukumomi, inda ake ci gaba da gudanar da bincike. Jami’an tsaro sun ce wannan mataki na daga cikin dabarun hana ’yan ta’adda samun kayan tallafi da ke ƙarfafa musu gwiwa wajen aikata ta’addanci.

Want your business to be the top-listed Grocery Store in Kafur?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

KAFUR Road
Kafur