Rigasar Muce

Rigasar Muce

Share

08069833709

16/04/2026

Gaskiya muna jira a kan aikin nanfa
Rigasar Muce

15/04/2026

WANNAN MAGANA HAKA TAKE

05/04/2026

MU 'YAN RIGASA BA MU YARDA DA WANNA GIDAN DANBEN BA DAN BATA TARBIYYA CE KUMA KAWO BARAYI DA KARUWAI. GASKIYA MANYAN RIGASA KU SA BAKI DAN KAR A SAMI MATSALA. MUNA CEWA RIGASA TA GYARU TO WAƊANNAN ZASU BATA MANA GARINMU. DAN ALLAH KUYI MAGANA. Rigasar Muce

Photos from Rigasar Muce 's post 26/03/2026

MUNYI MUBA'YAA.

Sabon shugaban Kungiyar IZALA (JIBWIS) Na Gundumar Rigasa da kewaye:-

Sheiak Abu Sufyan Ishaq Dumbulun Shine wanda Allah Yaba.

Allah yayi maka jagora yayi ruko da hannunka zuwa daidai.
Allah ya jikan shugaba Alh Ahmad Duka, Allah yayi masa rahmah.
Rigasar Muce

15/03/2026

RANAR MAI KAMAR TA YAU!!!

A 9 ga Maris, 2026, ne ake cika shekaru 13 da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kaduna, Sheikh Muhammad Bello Ahmad Aladamawy.

Marigayi Sheikh Muhammad Bello Ahmad Aladamawy ya kasance malami mai ƙwazo wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da Al-Qur’ani da ilimin addinin Musulunci ga al’umma.
Sheikh Dr. Muhammad Bin Uthman Kano ne ya jagoranci sallar jana’izarsa, kamar yadda malamin ya bar wasiyya tun yana raye.

A lokacin jana’izar, Gwamnan Jihar Kaduna na wancan lokaci, Alhaji Dr. Mukhtar Ramalan Yero, da kuma Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai (ɗan takarar gwamna a wancan lokaci) duk sun halarci jana’izar domin girmamawa ga wannan babban malami.

Kafin rasuwarsa, marigayi Sheikh Muhammad Bello Ahmad Aladamawy shi ne ke gabatar da Tafsiri a Masallacin Ahlus Sunnah dake Hayin Mallam Bello, Rigasa Kaduna, inda dubban mutane s**a amfana da iliminsa da wa’azinsa.

Yau shekaru 13 kenan da rabuwarsa da duniya, amma har yanzu ana tuna irin gudummawar da ya bayar ga addini da al’umma.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. 🤲
Idan tamu ta zo, Allah Ya sa mu cika da kyakkyawan ƙarshe tare da imani.

👉 Idan ka san wannan malami ko ka taɓa sauraron Tafsirinsa, ka rubuta “Allah Ya Jikansa” a comment domin yi masa addu’a.

13/03/2026

GWAMNA UBA SANI KASA IDO A RIGASAR MU DAN AN FARA CUWACUWA

Photos from Rigasar Muce 's post 10/03/2026

RIGASA ELDERS FORUM SUN NUNA GOYAN BAYANSU GA GWAMNA MALLAM UBA SANI

Rigasa Elders Forum sun ziyarci Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, Arc Abubakar Rabiu Abubakar, a ofishinsa domin taya shi murna tare da nuna goyon bayansu ga gwamnatin Jihar Kaduna da kuma bayyana amincewarsu da sake tsayawa takarar Gwamna Uba Sani takara a 2027.

Dattawan sun bayyana farin cikinsu da irin yadda Gwamna Senator Uba Sani ke bai wa Rigasa muhimmanci da duk abunda ya shafi garin Rigasa tun daga farkon mulkinsa, har zuwa yanzu da gwamnan ya sake bai wa ɗansu mukamin Sakataren Jam’iyyar APC na jihar kaduna.

Sun ce daga cikin abubuwan alheran da gwamnan yayi wa Rigasa akwai:

• Bai wa ’yayan gundumar Rigasa muƙamai masu muhimmanci.

• Aikin titunan Rigasa Township Road, da s**a haɗa da Makera zuwa Danmani da Lokoja zuwa Ado Gwaram.

• Aikin magance zaizayar ƙasa da kamfanin ACreSAL ke gudanarwa tare da tantance gidajen da aikin zai shafa.

Biyan diyya da kudi masu kyau ga gidajen da aikin titin Rigasa Township Road zai shafa.

Haka kuma sun ce a satin daya gabata gwamnan ya ziyarci Rigasa domin ƙaddamar da aikin gina sabbin makarantu 102 a faɗin Jihar Kaduna ya kuma zabi rigasa a matsayin wajan da yazo ya kaddamar da gina wannan sabbin makarantun.

Dattawan sun jaddada cewa ba'a taɓa samun gwamnan da ya karrama Rigasa kamar haka ba, tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Uba Sani da kuma tabbatar masa da kuri’u mafi rinjaye daga Rigasa a zaɓen 2027.

Rigasar Muce

09/03/2026

RIGASAR MU A YAU

09/03/2026

WANNAN BAYAN ALLAH, ALLAH YA JIKAN SA DA RAHMAN

07/03/2026

ANCI AMANAR GWAMNA MAL UBA SANI.
A IGABI.

Inji Hon Aliyu Saidu ( Danbaturia )

Mai Girma Gwamnan Mal Uba Sani ya Amince da wasu domin suyi Abinda zasu taimake shi, Amma sun kulle daki su kadai sunyi son ran su,

Don haka maganar gaskiya sunci Amanar sa.

Wannan Maganar tasa tana Kan hanya koko akwai sharhi acikin ta ?

Rigasar Muce

06/03/2026

RIGASA NA CI GABA KUMA ZAMU CI GABA DA YARDAR ALLAH

04/03/2026

Da Dumi Dumi 🔥

Dan Rigasa ya Zama Sakataren Jam'iyyar APC na Jihar Kaduna, Arc Abubakar Rabiu Abubakar.

Yaya kuke kallon wannan Matsayin ta fuskar kawo canje canje musamman acikin garin Rigasa baki daya ?

Sannan wace Nasiha ya kamata kuyi Masa ?

Rigasat muce

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

RIGASA KADUNA
Kaduna