I.R Turunku

I.R Turunku

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from I.R Turunku, Public Figure, Kaduna.

08/03/2026

Ba a kwalliya da kayan aro. Ko wace irin ni'ima ko baiwa da Allah yayi maka, aro ya baka. Don haka ka shiga taitayinka. Ka guji yiwa mutane gori da kuri akan abun da Allah ya baka. Don idan ya ga dama, bama abun da ya baka ɗin ba, hatta kai ɗin kanka, sai ya ɗauke abunsa. Allah ba babanka ba ne ko kuma ƙanin gyatumarka ba ne ballantana ka ce kai in ya baka ba zai iya ba wa waninka ka. Ka kula da duniya, ka lura da rayuwa. In ba haka ba, zaka sha mamaki wallahi!

I.R Turunku

12/02/2026

My Interview as Stepdown Project Ambassador with Hope Behind Bars Africa and WeRise

12/02/2026

My Interview as Stepdown Project Ambassador with Hope Behind Bars Africa and WeRise

04/02/2026

A Letter to Someone Unknown.

03/02/2026

Barkanmu Da Ranar Talata

Photos from I.R Turunku's post 29/01/2026

I am profoundly grateful to have successfully completed the Millennium Fellowship, presented by the United Nations Academic Impact (UNAI) in partnership with the Millennium Campus Network

This journey has been both an honor and a defining chapter in my leadership and service path. Representing Ahmadu Bello University, Zaria, and serving as a Campus Director, I had the privilege of working with dedicated peers committed to advancing the Sustainable Development Goals (SDGs) and addressing pressing social challenges within our communities and beyond.

The Fellowship strengthened my resolve to lead with integrity, compassion, and purpose. I remain sincerely thankful to MCN and UNAI for the mentorship, trust, and global platform that made this experience possible. I am proud to join the 23,000+ strong MCN Alumni community and look forward to deepening my impact as this journey continues.

📢 Applications for the Millennium Fellowship Class of 2026 are now open at millenniumfellows.org. I strongly encourage students who are driven by service, leadership, and social impact to apply.

24/01/2026

Ya Allah Ka agaza
Kar ka bari mu gaza
Imaninmu ya girgiza
Darajarmu ka ingiza
Raba mu da cin gwaza
Kare mu shan gwabza
Mai son saka mu a haza
Sa Mala'iku su masa yankar kaza.
🙏🙏🙏

18/01/2026

ZANGA-ZANGAR LUMANA
(Rubutawa: I.R Turunku & M.S Nura)

Zanga-zangar lumana ba tada ƙayar baya ba ce ga gwamnati
Hanya ce ta isar da saƙo mai tarin amo: sauti
Kundin Tsarin Mulki ya bada damar hakan cikin wannan baiti
Na arba'in cif-cif, ayi a cikin daƙa ko ƙwaryar t**i
Ƴancinka ne bar zancen su wangalahau da tsiyau; karabiti.

Ana iya yi ta hanyar rubutu da kalmomi marasa datti
A yanar gizo ko jaridu ko a rigunar saidawa a kanti
Rawa da waƙa ma hanya ce, mu tuna gwagwarmayar Fela Kuti
Wasu na yajin aikin cin abinci, a hana komai ga bakin salati
Zama shiru zugum ba tare da furta kalma ɗai ta halbati
Zanga-zangar lumana ce kan sanya na bisa taunar kwankwalati.

Gwamnati zaɓin al'umma ce ni da kai Kuluwa da Mati
Muka kaɗa mata kuri'a lokacin zabe a dukkan akwati
In ta karkace dole ne mu yi ƙorafin maidata a kan saiti
Rashin adalci ke sanya gwamnati ta sanya wasu ƙatti
Su cusa takunkumi gare mu, in mu bijire, wasu su yi wafati.

Ƴancinmu ne daga Rabbil Izzati
Bayyana damuwarmu ga gwamnati
In muyi shiru ga wanga jar fenti
To wata rana za muyi karar faranti.

16/01/2026

Babu Mai Taimaka Mun Akan Abun Da Nake Yi

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Address

Kaduna