Labari Da Gaskiya
Trusted
21/04/2026
Shugaba Tinubu ya yi garambawul a tsarin Ministocinsa yayin da Wale Edun da Ahmed Dangiwa s**a yi Murabus
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da yin ɗan takaitaccen garambawul a cikin majalisar ministocinsa, inda aka samu canjin wasu manyan ministoci biyu.
Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, da Ministan Gidaje da Raya Birane, Akitek Ahmed Musa Dangiwa, sun yi murabus.
A cikin wannan garambawul, Shugaban ya ɗaukaka darajar Taiwo Oyedele, wanda a baya yake matsayin Karamin Ministan Kuɗi, zuwa babban Ministan Kuɗi kuma Kodinetan Tattalin Arziki na Ƙasa don ya maye gurbin Wale Edun.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bayyana sunan Muttaqha Rabe Darma (PhD) a matsayin wanda aka zaɓa don ya zama sabon Ministan Gidaje da Raya Birane don maye gurbin Dangiwa.
Sanarwar ta umarci ministocin da ke barin gado da su kammala dukkan takardun miƙa rantsuwa da miƙa ayyuka ga waɗanda za su gaje su kafin ƙarshen ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026.
Sanata George Akume ya bayyana cewa:
"Wadannan canje-canje na nufin ƙarfafa haɗin kai da inganta yadda ake tafiyar da gwamnati, musamman don samar da sauyi a tattalin arzikin Najeriya k**ar yadda ajandar 'Renewed Hope' ta tanada."
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi wannan canji ne bisa ikon da sashe na 147 da 148 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi masa gyara) ya ba shi.
Shugaban ya gode wa ministocin da ke barin gado saboda gudunmawar da s**a ba ƙasa, sannan ya yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba. Haka kuma, ya tabbatar wa sauran membobin majalisar cewa wannan tsari na garambawul zai kasance mai ci gaba ne don tabbatar da cewa kowa ya yi aikinsa yadda ya k**ata.
21/04/2026
Da Dumi Dumi
Cutar COVID-19 ta sake ɓulla a Nijeriya
21/04/2026
BABBAR MAGANA 🔥: Masu Cikakken Hankali ne A Arewacin Nigeria Kadai Suke Gane Irin Alkairin Da Gwamnatin Tinuba Takawowa Yankin Arewa, Dayawan Mutane Kabilanci Da Nuna Kiyayya Kesa Basa Fahimtar Ina Ƙasar Ta Dosa, Yazama Wajibi Mufadawa Kanmu Gaskiya Domin Ko Shakka Babu Tinuba Adaline~ Inji Hussaini Sule Koki"
Ya Fadi Hakan ne A Wajen Wani Taron Daga Darajar Jam Iyyar APC Da Mawaki Dauda Kahutu Rarara Ya Shiryawa Yan Film.
Rigimar Duniya...
Ta Rinchaɓe Tsakanin Mai Keke Da Mai Mota.
21/04/2026
Da Dumi Dumi: Mutane Sun Kauracewa Taron Gan Ganin Zaɓen Shugabannin Jam Iyyar ADC Ɓangaren Hon Nafi'u Bala A Garin Abuja A Wannan Safiya.
21/04/2026
Gwamnati Ta Bude Shafin Tallafin Karatu Na PTDF Ga Daliban Injiniya
Hukumar Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ta sanar da buɗe shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026 ga ɗaliban da ke karatun aikin injiniya da sauran fannoni masu alaƙa da harkar man fetur a jami’o’in Najeriya.
Hukumar ta buɗe shafin ne a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026, inda aka tsara rufe karɓar rejista a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026.
Wannan tallafi ya shafi ɗaliban da ke matakin digiri na farko (Undergraduate) da kuma masu neman digiri na biyu da na uku (Postgraduate). Manufar shirin ita ce ƙarfafa kishin gida da samar da kwararru a fannin fasaha don rage dogaro da masana daga ƙasashen waje.
Masu sha’awa za su iya rejista ta shafin: https://scholarship.ptdf.gov.ng
Hukumar PTDF ta fitar da matakai guda goma da ya k**ata masu nema su bi:
1. Buɗe Akawun: Ziyarci shafin tallafin, sannan ka samar da akawun ta hanyar shigar da bayananka. Za a turo maka sako ta imel don tabbatarwa.
2. Shiga Shafin (Login): Yi amfani da imel da kalmar sirri (password) don shiga shafin akawun dinka.
3. Tabbatar da Lambar NIN: Wajibi ne mai nema ya tabbatar da lambar sa ta shaidar ɗan ƙasa (NIN). Hukumar ta yi kashedin cewa idan aka samu matsala wajen tantancewa, kada a riƙa maimaitawa akai-akai don gudun asarar kuɗi; k**ata ya yi a tuntuɓi sashen taimako.
4. Yarda da Sharuɗɗa: Dole ne ka karanta sannan ka amince da sharuɗɗan shirin kafin ka ci gaba.
5. Cike Fom: Shigar da dukkan bayanan da ake buƙata cikin kwarewa da gaskiya.
6. Zaɓar Karatu da Jami’a: Zaɓi jami’o’i da darusan da kake son karantawa (na farko, na biyu, da na uku). Masu neman digiri na biyu da na uku za su loda takardar bayyana manufar karatu (Statement of Purpose) ko shawarar bincike (Research Proposal).
7. Ɗora Takardu: Ana buƙatar takardar shaidar karatu, takardar haihuwa, da ta ɗan ƙasa da jiha. Dole takardun su kasance cikin tsarin PDF kuma girmansu bai fi 300KB ba.
8. Ƙarin Takardu: Za ka iya loda takardun kasancewa dan daya daga ƙungiyoyin kwararru idan kana da su.
9. Duba Bayanan da aka shigar: Tabbatar ka duba dukkan bayanan da ka shigar don gyara kura-kurai kafin ka tura.
10. Tura bayanai: Da zaran ka tura, ba za ka iya sake gyara komai ba. Don haka, a tabbatar komai ya kammala kafin dannawa a tura.
Wannan tallafi na cikin gida (In-country scholarship) ya bambanta da wanda ake fita ƙasashen waje don yi. Tallafin yana rufe kuɗin makaranta, kuɗin alawus na wata-wata, da kuma samar da kayan karatu ga ɗaliban da s**a yi nasara bisa cancanta.
Hukumar ta jaddada cewa wannan yunkuri wani ɓangare ne na dabarun gwamnatin tarayya na haɓaka jarin bil-adama a fannin mak**ashi na ƙasa.
20/04/2026
Shugaba Tinubu Ya Nada Dakta Fatima Sulaiman A Matsayin Sabuwar Shugaba A Hukumar NBMA
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dakta Fatima Suleiman Zuntu a matsayin sabuwar Shugaba kuma Babban Jami’ar Gudanarwa (DG/CEO) ta Hukumar Kula da Kwayoyin Halittu ta Kasa (NBMA).
Wannan nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, inda aka bayyana cewa nadin nata zai kwashe tsawon shekaru hudu (4) ne a karo na farko. An bayyana cewa nadin ya fara aiki ne tun daga ranar 16 ga Afrilu, 2026, k**ar yadda sashi na 5 na dokar hukumar NBMA ta shekarar 2015 ya tanada.
Dakta Fatima Suleiman Zuntu kwararriya ce a fannin lafiyar al'umma (Public Health) sannan kuma masaniya ce kan dabarun tsara manufofi. Kafin nadin nata, tana da gogewa wajen tafiyar da muhimman shirye-shiryen raya kasa wadanda s**a haifar da sak**ako mai kyau a matakin kasa.
Shugaba Tinubu ya bukaci sabuwar shugabar da ta yi amfani da dimbin iliminta da kwarewarta domin ciyar da hukumar gaba, tare da tabbatar da cewa ayyukanta sun taimaka wajen kare lafiyar ‘yan kasa da muhallin Najeriya.
Hukumar NBMA dai ita ce ke da alhakin sa ido da kuma tabbatar da cewa duk wani abu da ya shafi kwayoyin halittu (GMOs) bai cutar da lafiyar mutane ko kasa ba.
20/04/2026
Ma’aikatar Kuɗi Ta Karyata Zargin Ɓoye Kuɗaɗen Shiga Na Kasa
Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta mayar da martani kan wasu rahotannin kafafen yada labarai da suke ikirarin cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar ƙasa ko kuma ana yin “ɓoyayyen kashe-kashe.”
Wadannan rahotanni sun biyo bayan fassarar da aka yi wa sabon rahoton Bankin Duniya (World Bank) kan tattalin arzikin Najeriya.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wadannan rahotanni ba gaskiya ba ne, kuma sun samo asali ne daga rashin fahimtar yadda tsarin kasafin kuɗi da rabon kuɗi yake aiki.
Ina Kuɗaɗen FAAC Suke Tafiya?
Ma’aikatar ta fayyace cewa kudaden da ake cirewa daga asusun tarayya (FAAC) ba ɓataccen kuɗi ba ne. Ana amfani da su ne wajen kashe-kashen da doka ta amince da su da s**a haɗa da; Zuba Jari da Tanadi Don samar da gobe mai kyau; Harkar Tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya; Kuɗin da ake bai wa hukumomin tara haraji; Turawa ma’aikatu da rassa (MDAs) kuɗaɗen da ya k**ata a mayar musu.
Ma’aikatar ta jaddada cewa tura wa jihohi da sauran matakan gwamnati kuɗaɗe ba wai sace su ba ne; harka ce ta tsarin mulki da ya wajaba a biya.
Sanarwar ta zargi wasu masu sharhi da amfani da tsoffin bayanai yayin da s**a yi kunnen uwar shegu da sabbin gyare-gyaren da gwamnati ta fito da su a farkon shekarar 2026.
"Dokar da Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu kwanan nan don kare kuɗaɗen man fetur za ta ƙara gaskiya a harkar kuɗi, kuma ana sa ran za ta ƙara kudaden da ake rabawa da kimanin kashi 0.4% na arzikin kasa (GDP) a kowace shekara."
Ma’aikatar ta bayyana cewa babban sakon rahoton Bankin Duniya shi ne cewa Najeriya na kan hanya madaidaiciya. Ga wasu daga cikin nasarorin:
1. Haɓakar Tattalin Arziki: Bangarori daban-daban na bunkasa.
2. Saukar Farashin Kaya: Ko da yake har yanzu akwai tsada, matakan da ake dauka sun fara rage radadin hauhawar farashi.
3. Rage Basuss**a: A karon farko cikin shekaru goma, bashin da ake bin Najeriya idan aka kwatanta da arzikin ƙasa ya ragu.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana nan kan bakarta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkar kuɗi. Ta bukaci manema labarai da jama’a da su rika tantance bayanai kafin yadawa don gudun janyo rudani a kasa.
20/04/2026
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Ibrahim Galadima
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar fitaccen mai kula da harkar wasanni kuma jagoran al’umma a Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima.
Marigayi Galadima ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Asabar yana da shekaru 78 a duniya.
Kafin rasuwarsa, Ibrahim Galadima ya rike muk**ai daban-daban a matakin jiha da na tarayya. Ya taba zama Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, sannan ya yi kwamishina har sau biyu a jihar.
Haka kuma, ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFA), wacce yanzu aka sani da NFF, tsakanin shekarar 2002 zuwa 2006.
Bayan ya bar aikin gwamnati, an nada shi sarautar Galadiman Fagge, inda ya jagoranci al'ummarsa ta Fagge da ke birnin Kano.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Galadima a matsayin babban rashi ga harkar wasanni da ma Najeriya baki daya.
Shugaban ya jaddada cewa ba za a taba mancewa da irin gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar wajen bunkasa kwallon kafa ba, tun daga matakin karkara har zuwa matakin koli.
"Ibrahim Galadima ya sadaukar da rayuwarsa wajen ciyar da wasanni gaba. Najeriya za ta dade tana tunawa da ayyukansa," in ji Tinubu.
Daga karshe, Shugaban Kasa ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, da Gwamnatin Jihar Kano, da kuma daukacin masoya wasanni na gida da waje, tare da addu'ar Allah ya jikan sa da rahama.
Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all your support! Ahmad Auwal Suleiman, Nuraddeen Ibrahim, Abdulrazaq Abubakar, Mannir Yarima Nasarawan Kargo, Abdul Tilde Lis, Yahaya Isah, Nasiru Muktar, Muhammad Yahaya Ali, Ismail Adam, Mudassir Umar, Bello M Chafe, Kabir Namadi, Salisu Habu Amshi, Abdulrashid Rabiu, Usaini Abdulrazak, Real El-bangees Kiyako, Sen Mahmoud Usman Nalado, Jamilu Lawal, Muhammad Usaini Duss, Mai Lasting J Gale
20/04/2026
A RANAR 18/4/2026❤️❤️❤️
Shugaban Wannan Kafa Mai Suna Dr Abdullahi Dahiru Yasamu Karuwa Na Aure Tareda Matarsa Halima Shafi'u Baby"
Sakon Godiya Ga Mahalarta Wannan Biki, Dafatan Kowa Yaje Gidansa Lafiya, Allah Muke Roko Yabasu Zaman Lafiya Da Karuwar Arziki"
Daukan Hoto~ Hafsat Yusuf Jibia.
19/04/2026
NELFUND Ta Biya Wa Daliba 6,385 na Jami’ar Lafiya Kudin Makaranta Miliyan 795
Hukumar bayar da lamuni ga dalibai ta kasa (NELFUND), ta fitar da kudi har naira miliyan dari bakwai da casa’in da biyar da dubu dari bakwai da ashirin da tara da dari biyar (₦795,729,500) domin biyan kudin karatun dalibai dubu shida da dari uku da tamanin da biyar (6,385) na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafiya (FULafia), Jihar Nasarawa.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasikar godiya da jami’ar ta aika wa hukumar ta NELFUND mai dauke da sa hannun Shugaban Jami’ar (Vice Chancellor), Farfesa Mohammed Isa Kida.
A cikin wasikar, jami’ar ta nuna cewa an turo kudaden ne kashi uku tsakanin watan Fabrairu da Maris na wannan shekara k**ar haka:
A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ta biya wa dalibai 4,563 Naira 565,249,500; sai ranar 24 ga Fabrairu, 2026 da aka biya wa ɗalibai 636 Naira 82,189,000; sai kuma 3 ga Maris, 2026 da aka biyawa ɗalibai 1,186 Naira 148,291,000. Jimillar adadin ɗaliban ya k**a 6,385 wanda aka biya musu Naira 795,729,500.
Farfesa Isa Kida ya bayyana jin dadinsa da kuma yabawa hukumar kan yadda take gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da rikon amana. Ya ce wannan tallafi babban abin farin ciki ne ga daliban jami'ar, domin zai share musu hawaye tare da basu damar ci gaba da karatunsu ba tare da fargabar kudin makaranta ba.
"Tasirin da NELFUND ke yi a rayuwar dalibanmu ba abin da za a iya kwatantawa ba ne. Mun gode kwarai da gaske kan sadaukarwarku wajen bunkasa ilimi a Najeriya," in ji shi.
Wannan tallafi na zuwa ne a karkashin shirin "Renewed Hope" na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin tabbatar da cewa babu dalibin da ya rasa damar yin karatu saboda rashin hali.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kaduna