AREWA Daily-Post
News Media Organisation Own and published by Ammani Media Ventures No 2 Layin Sarki Badarawa Kaduna
01/10/2025
Hon. Sani Mahmood Sha’aban Celebrates Nigeria’s 65th Independence Anniversary By Ibrahim Ammani Hon. Sani Mahmood Shaaban, a founding member of the All Progressives Congress (APC) and a former gubernatorial candidate in the 2023 Kaduna State elections, extends heartfelt cong…
01/06/2025
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: K***n Mai Martaba Sarkin Fika A Jihar Yobe, Yarima Haruna Abali Ya Rasu Yau A Abuja, Bayan Gajeruwar Rashin Lafiya.
Allah Ya Jikansa Da Rahama!
06/12/2023
Ba Za Mu Yi Shiru Ba Sai An Hukunta Sojojin Da S**a Yi Wa 'Yan Uwanmu Ķìśàñ Ģìĺĺà A Kaduna, Haka Zalika Sai Gwamnati Ta Biya Diyyar Waɗanda S**a Yi Shahada, Cewar Sheikh Sani Khalifa Zariya
29/11/2023
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fito Da Manhajar DSO Na Aikin Talbijin Kwanan Nan, Cewar Minista
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma'aikatar sa ta na nan ta na aiki tuƙuru domin fito da sabuwar manhajar da za a yi amfani da ita a koma aiki da na'urar kwamfuta wajen aikin talbijin a duk faɗin ƙasar nan, wato 'Digital Switch Over' (DSO).
Hadimin musamman kan harkar yaɗa labarai na ministan, Malam Rabi'u Ibrahim, ya bayyana a cikin wata takardar sanarwa cewa ministan ya faɗi haka ne a Abuja a ranar Litinin a lokacin da ya ke buɗe babban taron sanin makamar aiki na shugabannin gudanarwa na Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA).
Ya ce: "Ina kuma so in yi amfani da wannan damar in nanata sadaukarwar Gwamnatin Tarayya ga tsarin 'Digital Switch Over', domin kuwa Ma'aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta na ta aiki tuƙuru kan manhajar DSO wadda ba za ta gaza ba; wadda za a yi amfani da ita a birane da ƙauyukan Nijeriya. Ana sa ran cewa hukumar NTA, a matsayin ta na babbar mai ruwa da tsaki a tsarin na DSO, za ta taka muhimmiyar rawa a ciki.”
Don haka Idris ya ƙalubalanci NTA da ta yi zuzzurfan tunani kan yadda yanayin aikin jarida ya ke sauyawa, musamman da yake sababbin fasahohin zamani na shigowa kuma zaɓin masu kallo shi ma ya na canzawa tare da kawo ƙalubale da kuma damarmaki.
Ya ce: “Sadaukarwar mu ga tabbatar da inganci da kuma karɓar sauyi shi ne gaba da komai. Tilas ne NTA ta ci gaba da rungumar canji, ta na karɓar sababbin dabaru a yayin da ta ke riƙe da darajar aikin jarida mafi girma sau da ƙafa.
“Wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da masu kallo su ke ta samun zaɓi daban-daban na inda za su samu bayanai, musamman ma da yake yanzu soshiyal midiya na da ƙarfi tare da tasiri wajen yaɗa labaran ƙarya da yaudara da ke akwai a cikin ta; don haka muhimmancin taro irin wannan ba ƙarami ba ne.”
Ya lura da cewa ɗaga ƙarfin hotuna da sautin da aka samu a NTA daga matakin 'standard definition' (SD) zuwa matakin 'high definition' (HD) ya na yin tasiri matuƙa a wajen jama'a masu kallo, ya ƙara da cewa tilas ne a samar da wannan tsarin a dukkan tashoshin NTA da ke faɗin ƙasar nan idan ana so a cimma manufar da ake buƙata.
Dangane da batun Tsarin Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) na gwamnatin Shugaba Tinubu kuwa, wanda ya bayyana da cewa ba a taɓa samun dabarar gina ƙasa ta ɓangaren zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya kamar ta ba, don haka a cewar Idris, "haƙƙi ya rataya a wuyan NTA ta ci gaba da wayar da kan 'yan Nijeriya kan nasarorin da ake samu a dukkan ɓangarori, kuma ta tabbatar da cewa 'yan Nijeriya sun fahimci alƙiblar da gwamnatin Tinubu ta fuskanta wajen yaɗa labarai da tsara shirye-shiryen talbijin.
Ministan ya buƙaci NTA da ta dage wajen dawo da martabar da aka san ta da ita a da lokacin da abubuwan da ta ke kai wa masu kallo, musamman wasannin kwaikwayo, waɗanda ban da haɓaka harkar nishaɗi a talbijin da su ka yi a ƙasar nan har ma sun kasance dalilin da ke sa mutane na rugawa gida domin yin kallo da yamma.
27/11/2023
Daga Shehu Isah Kaura
Dole mutanen nan su tsani H.E Abba Kabir Yusuf. Domin yanaso yagina yaran talakawa suyi competing da yaransu. A 2013 lokacin ina CAS Kano, wannan bawan Allah na jikin hoto ga duk wanda yake CAS a lokacin yasan direba ne wanda yake tukamu a motar makaranta.
Daga baya yakoma yayi HND har yasamu distinction. A yanzu haka danake wannan rubutu, a class daya yake lecture tareda dan gidan tsohon Minister na Science and Technology na Nigeria wato Ogbonnaya Onu; haka kuma aji daya yake karatu da dan gidan mamallakin kanfanin kera motacin Hyundai na duniya baki daya.
Kusan Koda yaushe se sun biyoshi harnan dakinmu domin yayi musu karin bayani akan darasi. Kaga ikon Allah, silar H.E Abba Kabir Yusuf dakuma Jagora Eng. Dr Rabi'u Musa Kwankwaso karkashin Kulawar Dan Aljanna Yusuf Kofarmata gashi Dan talaka, direba yana koyarda yayan shahararru a duniya. Kaga kuwa ai dole suji haushi.
Allah ka tabbatarwa da Abban Kanawa kujerarsa. Dan tsarkin mulkin Ubangiji. Ameen
Ni Kuma - Wannan Ɗin Yayanmu Ne Ɗan Unguwarmu Ne Shiyasa Muke Kwankwasiyya Ko Bazata Bamu Komai Ba Matuƙar Namu Zasu Samu Alhamdulillah.
27/11/2023
Matasa sun laƙaɗawa mutumin dake ikirarin shi magajin Bóbrísky ne na jaki, inda s**a cewa ala dole sai ya bar wannan hanyar.
27/11/2023
Jaruman Kannywood Da S**a Rasu Cikin Shekara Guda!
Allah Muke Roko Ya Jikansu Ya Gafarta Musu Allahumma Amin 🤲
24/11/2023
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani
19/11/2023
Fitacciyar Likita a Nijeriya, kuma mai wayar da kan al'umma a kafafen yaɗa labarai, Dr. Na'aima Idris ta Amarce da Angonta Bukar. Wane fata zaku yi mata?
19/11/2023
SILENT KILLER
Sarkin Yaki! Idan ana maganar iya siyasa da halinta Ganduje karshe ne a wannan bangare😁 ya karanci abin yadda baku tinani. Yasan ta ina za'a hau yasan ta inda za a sauka a lokaci. Kubar shi kawai yadda kuka ganshi. Amma ganduje karshe ne😅
Nigeria kasar mu.
✍️ Isma'il Bawa
19/11/2023
Innalillahi Wa'inna ilaihir Raji'un
Yanzu Muke Samun Labari Rasuw Malama Sadiya Allah ya jiƙan ki da gafara ya haskaka makwancin ki.
JANAZA; Ƙarfe 9:am Ɗanraka Samaru Zaria.
15/11/2023
Ɗan Nijeriya Jilani dake aiki da kamfanin ƙera motoci na Amurka ya ƙirƙiri mota me caji
Ɗan Nijeriya, haifaffen jihar Sokoto
(Jilani Aliyu), wanda yake aiki da kamfanin ƙera motoci na duniya dake ƙasar amurka, “inda ya ƙirƙiri wata mota da ake bayanin cewa; za a yi alfahari da ita a faɗin duniya.”
Kamfanin Motocin na ƙasar amurka ta wallafa mota me caji da ɗan Nieriyan ya ƙirƙira, wannan dai da kuke gani shine (Jelani Aliyu) kamar muka faɗi, haifaffen jihar sokoto ne, kuma shine shugaban “Nigeria Automobile Industry”.
Malam Jelani yana cikin jerin fitattun masu fasahar ƙera motoci na duniya kuma shine ya ƙirƙiri samfurin wannan mota Chevrolet me caji.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kaduna