Abbas Marafa

Abbas Marafa

Share

There's no grantee until you find yourself in Jannah

12/05/2026

Sabon Gari zaria sai abun Al'ajabi
😅😅

07/05/2026

Da Dumi Dumin Sa YANZU-YANZU

Alhamdulilh, Hon Bello El-Rufai Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa Jam'iyyar Hadaka Ta ADC, a Hukumance

Zabe zamuyi nasara Insha Allah

04/05/2026

Zai yi wahalan gaske wanda kwakwalwarsa ke aiki daidai ya yarda cewa wannan abinda da Madugu keyi don kishin talaka yake yinshi

Photos from Abbas Marafa's post 04/05/2026

TIKITIN OBI DA RABI’U, TA WACECE?

Bari mu ƙara ma yan siyasan Facebook haske.

A shekaran 2018, Obasanjo ya fita daga PDP ya kafa jam’iyyar haɗaka ta ADC (duba hoto na 1) domin kafa sabuwar tafiya wanda dalilinsa kawai shine baya son Atiku ya zama shugaban ƙasa.

A wancan lokacin yayi amfani da su Obi da suke daga Kudu maso Gabas (South East) wanda kowa yasan yanki na da suku ba PDP ƙuri’a a dunƙule (blocked vote) domin ganin an raba ma PDP ƙuri’a. Sannan ya waiwayo Arewa yayi amfani da babban yaronsa Rabi’u yayi anti-party ga PDP (duba hoto na 2).

Wannan dalilin yasa tun farko banyi gigin shiga jam’iyyar ADC ba.

A 2023 ma dai abinda s**ayi kenan. Obasanjo yayi ƙoƙarin gwaji akan Obi da sunan addini, wanda akasarin waɗanda s**a zaɓi Obi PDP zasu jefa ma ƙuri’unsu da bai tsaya takara ba. Sannan ya sake waiwayo yaronsa Rabi’u domin ya ƙara fasa ƙuri’un jihar Kano kada Atiku ya samu gaba ɗaya. Yin hakan zai bashi daman cinma muradinsa na maida shugabanci zuwa yamma sannan ya sami amsarsa na ganin za’a iya cin zaɓe ƙarƙashin inuwar addini ko a’a.

Bayan ya fahimci cewa ba zai iya cin zaɓe ƙarƙashin inuwar addini ba, sai ya sake dabara ta hanyan tattara ƙarfinsa kan waɗannan yaran nasa guda biyu. Tunaninsa Obi zai iya sake samun ƙuri’u kamar yanda ya samu a 2023, sai su haɗa da wanda Rab’iu ke samu a Kano kaɗai suci zabe. Wanda ko da zasu sami yawan ƙuri’un dai-dai ba zasu wuce Tinibu ba idan shima ya sami nashi ƙuri’un dai-dai (duba hoto na 3).

Sai dai kash! A wannan karon zasu sha mamaki, domin addini ba zaiyi tasiri kamar yanda yayi a 2023 ba. Kaha kuma Kano ta kuɓuce daga hannun Rab’u. Sannan duk mai hankali, ba a Arewa kaɗai ba, ya gama gano su.

Sauran karatun ku nemi Askaa ya ƙarasa maku…

A ƙarshe ina mau ba yan siyasan Facebook shawara da a riƙa zurfafa bincike 🤔

copied

Photos from Abbas Marafa's post 02/05/2026

LISSAFI BAI TAFI DAIDAI BA

Ana ta yaɗa rade-radin cewa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na shirin ficewa daga haɗakar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), domin komawa wata jam’iyya inda Peter Obi zai tsaya takarar Shugaban Ƙasa, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso zai zama mataimakinsa.

Wannan rade-radi na ɗauke da wani kamshin gaskiya, musamman idan aka yi la’akari da abin da ya faru jiya, lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci ta bai wa David Mark nasara.

Bayan haka, Atiku Abubakar ya fitar da saƙon taya murna, amma har yanzu ba a ga irin wannan saƙo daga Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Idan har Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso s**a fice daga wannan haɗaka, hakan na iya zama ɗaya daga cikin manyan kura-kurai a tarihin siyasarsu. Idan haka ta tabbata, to ana iya kallon hakan a matsayin sake rarraba ƙuri’u kamar yadda ya faru a zaɓen 2023.
A halin yanzu, babu wani ɗan siyasa guda ɗaya da zai iya kayar da Bola Ahmed Tinubu ba tare da cikakkiyar haɗin kai ba. Ko da an yi haɗaka, dole ne ta kasance mai ƙarfi da gaskiya kafin a iya samun nasara.

Dukansu Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma Rabiu Musa Kwankwaso na buƙatar haɗin kai mai ma’ana idan suna son cimma wannan buri.
Dangane da batun goyon bayan yankuna, siyasar Najeriya na buƙatar haɗin kai da fahimtar juna tsakanin kowane ɓangare na ƙasa, ba tare da nuna wariya ko fifiko ga wani yanki ko ƙabila ba.
A ƙarshe, idan har Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso s**a fice daga haɗakar, hakan na iya ƙara wa Bola Ahmed Tinubu damar ci gaba da samun rinjaye.

Allah Ya ba mu zaɓi mafi alheri.

15/04/2026

zabi ya rage naku 😅

04/04/2026

Allah ya gafarta miki Hajiya Amma.

24/02/2026

ZAMAN KOTU A YAU 24/02/2026.

Bayan Samun Tabbacin cewa Mal. Sani Khalifa Zaria yana Tsare a hannun hukumar DSS Yanzu.

Sai dai kuma Zaman Kotu a yau Ya gudana ba tare da Hukumar DSS da Lauyoyin sun bayyana a kotu ba, Hakan yasa Alkali ya ɗage zaman zuwa 05/03/2026 kamar yazo mana daga Kotu a yau.

Ya kamata Gomnaty tasani cewa ba komai muke bukata ba saidai ta Gurfanar da Khalifa a gaban kotu sannan a tabbatar da Ingancin Zargin da ake masa na Tuhuma, idan ya ingata ayanke masa hukunci, idan kuma ya tabbata baida Laifi su sallame shi ya koma cikin iyalan sa da Almajiran sa cikin Ƴanci.

Cigaba da tsare Khalifa ba tare da hukuncin Kotu ba wannan zalinci ne, mu kuma bazamu yarda da hakan ba.

Allah Ka fimu sanin dukkan wani abunda yake ɓoye acikin wannan lamarin, Allah kayi mana mafita Albarkan wannan Watan, da Ibadun Salihan bayin ka acikin wannan watan.

Ameeeen.

copied.

31/01/2026

🙏

23/10/2025

Kizo da koki 😅🤣

14/10/2025

Bayan ya kai kololuwa wajen tabbatar da hujjojin da s**a kasa korewa, sai ya nemi afuwarsu cikin girmamawa da dattijantaka a matsayinsu na waɗanda Allah ya ɗora shugabanci a kansa.
Sheikh Triumph Ikon Allah!
Ya Allah, ka ƙara mana son Annabi Muhammad (S.A.W). 🙏

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Kaduna