Abdhallah Talk
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdhallah Talk, Video Creator, Zaria Road, Kaduna State.
10/06/2026
MASU AMFANI DA P O S YAKAMATA KUSAN WANNAN...👇
Idan customer ya saka card, ya shigar da PIN, kuma transaction ya riga ya wuce (approved), ba a iya CANCEL kai tsaye.
Abin da ake iya yi kafin PIN shi ne cancel. Amma da zarar PIN ya tafi kuma banki ya amince da payment, sai dai:
🔹 REVERSAL
🔹 REFUND
Wannan ba “setting” ne na POS agent ba, tsarin banki ne da network ke sarrafawa domin kare tsaro da hana fraud.
⚠️ Don haka ku sani:
Cancel = kafin PIN kawai
Bayan PIN = transaction ya kammala
Dole sai an bi hanyar banki don reversal ko refund
💡 Ku rika fahimtar tsarin POS don kaucewa rikici tsakanin customer da agent.
Allah ya sa mu dace 🤲
゚
09/06/2026
ABDUL TURAKEEY SHI KADAI NE SHUGABAN KARE MUTUMCI NA AFIRKA...📌
Saboda Ibrahim mai shunku ya kare mutumci ne ta hanyar cin amana, shi kuma mai gida Abdul Turakeey a matsayin sa na shugaban kungiya na Afrika yana kare mutumci ne ta hanyar dawo da matasa zuwa ga hanya madaidaiciya.
Nasan yanzu kun fahimta da kyau, don haka a daina kakabawa (Mai shunku) wannan sarautar domin bai can canta ba.😌
Shin menene ra'ayin ku.?
ABDHALLAH TALK ✍️
゚
09/06/2026
Da alama Dauda Kahutu (Rarara) tauraronsa ya dishashe...😯👇
Nan a wajen wani taro ne da s**a gabatar, shine yake cewa "Nigeria"... "Nigeria"... (Yana so ace sai Tunubu) Amma wallahi mutane s**a ki amsa wa, sai da yace Kano ne ma aka samu wasu s**a dan ce "sai Abba" 😄
Shin a ganinku har yanzu tauraron Rarara yana nan ko ya ɓace.?
Abdhallah Talk ✍️
09/06/2026
Innalilahi...😢👇
Yan Bindiga Sunkashe Daya Daga Cikin Dattawan Da S**a K**a Allahuakbar Allah Yajikansa Sukuma Allah Ya Mana Magninsu
Wallahi muna wani hali a ƙasar nan...👇😢
゚viralシ ゚
Allah yasa mudace...😢🤔
゚viralシ ゚
09/06/2026
WASU MUTANE SUNA SHIGA IRIN WADANNAN HARKOKI SABODA SON ZUCIYAR SU...😢👇
Akwai kasuwanci da yawa da ake yi a ɓoye waɗanda doka ba ta amince da su ba. Irin waɗannan kasuwanci suna jawo matsaloli ga al'umma, suna lalata rayuwar matasa, kuma suna hana ci gaban ƙasa.
Wasu mutane suna shiga irin waɗannan harkoki saboda son kuɗi cikin sauri. Amma abin da ba sa fahimta shi ne cewa duk kuɗin da aka samu ta haramtacciyar hanya ba sa kawo zaman lafiya ko albarka. Sau da yawa suna jawo matsaloli, tsoro, da asarar mutunci.
Abin da ya kamata matasa su fahimta shi ne cewa babu wata hanya ta gajeriyar nasara da ta fi aiki tuƙuru, ilimi, da haƙuri. Duk wata dukiya da aka gina a kan gaskiya tana da daraja fiye da babbar dukiyar da aka tara ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya kamata mu ƙarfafa matasa su koyi sana'o'i, su nemi ilimi, su rungumi kasuwanci na halal, kuma su kasance masu amfani ga al'ummarsu. Domin ci gaban ƙasa yana farawa ne idan matasanta sun zaɓi hanya madaidaiciya.
Kada son kuɗi ya sa mu manta da darajar mutunci. Mutum na iya rasa kuɗi ya sake samun su, amma idan ya rasa mutuncinsa, dawo da shi ba abu ne mai sauƙi ba.
Nagode da sauraro
ABDHALLAH TUDUN WADA ✍️
09/06/2026
Daga yau mun daina...🔥👇
Assalamu alaikum jama’a! Ni ne Abdhallah 😎. K**ar yadda kuka sani, wannan page ɗin yana cike da dariya da cartoons… amma yanzu lokaci yayi da zamu ɗaga mataki! 🚀
Daga yau, page ɗin zai zama na ilimi, shawarwari, da tips na rayuwa domin taimaka muku ku samu nasara kuma ku sauƙaƙa rayuwa. 💡✨
Kada ku damu, zan ci gaba da ɗan fun da abubuwan nishadi — amma yanzu tare da karin ilimi da practical advice.
Ku kasance tare da ni, ku bi page ɗin, mu girma tare! 💪📚
09/06/2026
🇳🇬 Najeriya na bukatar canji!
Rashawa, talauci, rashin tsaro, da rashin ilimi suna kawo koma baya. Amma canji yana farawa daga kanmu!
💡 Wayar da kai, aiki tukuru, da haɗin kai sune mabuɗin gina kasa mai kyau.
✨ Mu canza halinmu, mu gina Najeriya mai kyau!
Mune matsalar Nigeria ba shugabanni ba.🔥🤔
゚viralシ
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Zaria Road
Kaduna State