Offical Nuraahmad

Offical Nuraahmad

Share

Sample ManοΏ½

13/12/2022

RAYUWA MAKAUNIYA CE .....✍️

Wani Mahaukaci ya Mika wa Ma'aikacin Banki Telar sa. Se yace: "Ina so na cire N5,000 daga asusu na".

Ma'aikacin banki yace wa Mahaukacin: "Duk kudi kasa da 10k ana ciro shine ta Na'urar ATM". Saboda haka sekaje can.

Mahaukacin yayi tambaya: "Me yasa haka"?. Ma'aikacin yayi tsawa yace mar: "Hakan dokan mu yace, saboda haka ka bar Nan, Akwai layi a bayanka suna jira. Se ya mayar wa Mahaukacin takardan Cire kudin nashi.

Mahaukacin ya tsaya ya danyi zugum, sannan ya Kara mikawa Ma'aikacin telar tasa yace: "Do Allah ka taimakeni ka cire mun dukkan kudin da nake dashi cikin Asusun Banki na.

Ma'aikacin Bankin yaji Mamaki sosai dayaga kudin dake asusun Mahaukacin bayan ya duba a cikin Na'urar komfuta, ya kada kansa Kamar kadangare, Se ya zube akai guiwowinsa Yana rokon Mahaukacin, Se yace:

"Mai gida Don Allah kayi Hakuri". Kanada 3.5 Billion Naira a Asusun ka kuma wallahi Bankin mu basa da ko kwatan Wannan kudi naka a yanzu. Sedai kayi Hakuri ka dawo gobe".

Mahaukacin ya tambayeshi to yanzu Nawa nake da damar cirewa?.... Se Ma'aikacin yace zaka iya cire 300k zuwa kasa.

Mahaukacin yace a cire masa 300k daga Asusun tasa.... Ma'aikacin yayi sauri ya cire kudin ya damka masa a hannunsa.

Mahaukacin ya zari N5000 daga cikin kudin ya saka su cikin aljihunsa. Sannan ya bukaci Ma'aikacin ya tura sauran N295000 a cikin Asusun sa na Banki, ya bashi kyautarsu.

Nan-da-nan Ma'aikacin Bankin ya rude, Nutsuwa ya fice ajikinsa.

π˜Ώπ˜Όπ™π™π™Žπ™Žπ˜Όπ™‰ 𝘿𝘼 π™‰π˜Όπ™†π™€ π™Žπ™Š 𝙆𝙐 π™†π™Šπ™”π˜Ό:
✍️Tabbas Dokoki basa canzawa, Amma mu 'yan Adam zamu iya canzawa a wasu yanayin da muka tsinci kan mu.

✍️ Kar mu tsangwami mutanen da bamusan ko su wanene ba don mun gansu cikin wani yanayi na Rashin kyawun gani ko Suturar da s**a Sanya ajikinsu.

✍️ Ya kamata mu Mu'amalanci mutane da kauna, girmamawa da Soyayya da kuma kulawa . Kar mu kuskura muyi Alkalanci akan Littafin da muka Karanta bangonsa ba tare da mun Karanta abinda ya kunsa a cikinsa ba.
Kabar Ji-ji da KaiπŸ™
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

30/07/2022

Kada ka sake kayiwa wani dariya akan kaddararsa, domin bakasan yadda taka qaddarar xata kasanceba

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Hadejia