Hadejia People's Union
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hadejia People's Union, Community Organization, Hadejia.
Hadejia a farko — ita ce gaba da komai🐎
Muryar al'ummar kasar Hadejia baki ɗaya. 🗣️🤝
Ba don jam’iyya ko siyasa ba — don ƙasar Hadejia da cigabanta.❤️
Hadejia ta kafu saboda sadaukarwar magabatanmu. 🕋⚔️
Za mu bunƙasa ta koda za a zubar da jininmu🩸
16/05/2026
ALBARKAR HADEJAWA ALQUR'ANI DA SUNNAH ALHAMDULILLAH
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, ya halarci bikin saukar Alƙur’ani mai girma na Makarantar Markazul Ulumul Qur’an Islamiyya Agumau, Hadejia, wanda ya ƙunshi ɗalibai mata guda ashirin da uku (23), ’yan mata goma sha biyu (12) da matan aure goma sha ɗaya (11),
16/5/2026.
©️ HADEJIA PEOPLE'S UNION ✍️
12/05/2026
SARKIN HADEJIA SRK TARBA ALLAH KARA BAMU ZAMAN LPY YA TEMAKI JAMI'ANMU
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karɓi baƙuncin dakarun Rundunar Sojojin Najeriya masu karɓar horo na Arba’in da Takwas (48) daga Makarantar Horar da Manyan Jami’an Sojoji da ke Jaji, jihar Kaduna, waɗanda s**a kawo ziyarar girmamawa da kuma ƙara wa juna sani a fadarsa.
©️ HADEJIA PEOPLE'S UNION ✍️
11/05/2026
Innalillahi wa'innah ilaihi raju'un...
Allah ya yiwa Hon. Abba Anas Laushi rasuwa yau a hannun masu garkuwa da mutane. Allah ya jiƙansa da rahama yasa mutuwa hutuce a gare shi. Ameen...
09/05/2026
ALLAH BAMU ZAMAN LAFIYA AMEEN 🤲
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karɓi bakuncin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Jigawa, Haruna Yahaya, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a yau.
CP Haruna Yahaya ya bayyana cewa ziyarar tasa ita ce domin gabatar da kansa ga Mai Martaba Sarkin a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, tare da yi masa bayani kan dabarun da yake shirin amfani da su wajen ƙarfafa tsaro a faɗin Jigawa.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Hadejia ya jaddada aniyar masarautar wajen ci gaba da bai wa rundunar ‘yan sanda cikakken goyon baya domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
©️ HADEJIA PEOPLE'S UNION ✍️
09/05/2026
KASAR HADEJIA TUSHENA
SARKIN HADEJIA SARKINA
GARIN HADEJIA MAHAIFATA
JIGAWA ABAR ALFAHARINA ✊
09/05/2026
MUNADA WANI ZABIN BAYAN KASANCEWA A HAKA - TOH MENENE MAFITA ❓🥹
Wasu photuna da aka dauka a wasu sassa na unguwar gagulmari dake hadejia, Hakika ba iya gagulmari ce mai irin wannan wajeje bah a cikin garin Hadejia. Yayinda ake fama da matsalar cizon sauro dakuma cututtukanda s**a shafi rashin tsabtar muhalli haryanzu wasu yankunan cikin garin Hadejia a kazance suke, Mutanen wannan yanki suna matukar kokari wajen tsabtace wannan waje toh amma suna buƙatar wata madogara don tsabtace muhallin akan lokaci. Hadin kan al'ummar Hadejia yanada matukar muhimmanci haka gomnati dakuma masu hannu da shuni.
Menene mafita kan irin waɗannan matsalolin tsabtar muhalli da Hadejia take fama dashi? mu tattauna 🥹
©️ HADEJIA PEOPLE'S UNION ✍️
06/05/2026
Kasar Hadejia ✊⚔️
26/04/2026
MUNA ALFAHARI DA ASALINMU ✊⚔️
Ga Hotunan Wasu Daga Cikin Kayan Tarihin Masarautar Hadejia.
1.Bulalar Sarki Buhari
2.Sirdi Talha Na Sarki Abdulkadir
3.Sirdi Bagariye Na Sarki Usman
4.Bindigar Sarki Muhammadu
5.Dala'ilu Na Sarki Usman
6.Kundin Rubuce Rubucen Sarki Abdulkadir
7.Qur'anin Sarki Haruna Wanda Ya Rubuta Da Hannunsa
8.Wasikun Sarki Muhammadu Sarki Haru Babba Zuwa ga Sarkin Musulmi Da Wazirin Sokoto Da Sauran Sarakuna.
Click here to claim your Sponsored Listing.