Al Amsal

Al Amsal

Share

|Digital Marketing|
|Science|
|Technology|

Photos from Al Amsal's post 02/03/2026

Breaking News.

Amurka ta nemi Iran ta hanyar ƙasar Italiya a jiya, inda ta gabatar da shawarar tsagaita wuta, a cewar rahotanni.

Sai dai Tehran ta ƙi amincewa da wannan shawara gaba ɗaya, kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa yunƙurin diflomasiyyar da Amurka ta yi bai samu karɓuwa daga Iran ba, lamarin da ke nuna ci gaba da tsamin dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu duk da ƙoƙarin shiga tsakani daga wasu ƙasashe.

01/03/2026

Sun dauka MMT ta zo ne don tabbatar da Shari'a sun jahilci rayuwa. A yau babban abinda ya tsone ma arnan duniya da na Nigeria shine Shugaban kasa Musulmi,Mataimaki Musulmi. Don haka tashin hankalin su a maye Mataimaki da Wadda ba Musulmi ba ayi balance.

Sun dauki hakkin tsaro da tabarbarewan ta wa gwamnatin MMT. A yau America yarjejeniya sakanin ta da Nigeria na a dauke matsalolin tsaro da karyan zasu bada gudumawarsu shine a soke dokokin Shari'a da muke amfani da su a Kotunanmu na Arewa da bada daman auren jinsi da hakkin 'yancin yara.

01/03/2026

LABARAI.

Za Mu Bayyana Makaman da Ba Ku Taɓa Gani Ba, Muna Shirye Mu Yaƙe Ku Tsawon Shekaru — Iran

Rundunar sojin musamman ta Iran, Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), ta fitar da gargaɗi mai tsanani ga United States a yayin da ake ci gaba da rikice-rikicen da s**a biyo bayan manyan hare-haren soji daga Amurka da Israel.

Wani babban janar a IRGC ya bayyana cewa Tehran za ta bayyana nan ba da jimawa ba wasu makamai “da ba ku taɓa gani ba a baya,” yana mai jaddada cewa ƙasar tana da cikakken shiri na fuskantar Washington “tsawon shekaru.”

A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Asabar, Janar Ebrahim Jabbari, wanda ke cikin manyan kwamandojin rundunar sojin Iran, ya ce ƙarfin tsaron ƙasar ya ƙaru sosai cikin ’yan shekarun nan, kuma nan gaba kaɗan za a nuna sabbin tsare-tsare da ba wani maƙiyi ya taɓa gani ba.

Janar Jabbari bai bayyana takamaiman bayanan makaman ba, amma ya jaddada ƙaruwa da ƙarfafa ikon Iran na kare yankinta da muhimman muradunta a yayin rikici mai tsawo.

Wannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lambar soji daga Amurka da Isra’ila, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da “manyan ayyukan yaƙi” a Iran, yana danganta hakan da abin da ya kira barazanar gaggawa daga shirye-shiryen makaman roka da na nukiliyar Tehran.

Trump ya sha alwashin rusa cibiyoyin makaman rokar Iran tare da hana Tehran mallakar makaman nukiliya, yana kuma kira ga jami’an tsaron Iran da su mika wuya domin kauce wa ƙarin zubar da jini.

A nasa bangaren, Janar Jabbari ya sake jaddada cewa rundunonin Iran a shirye suke don dogon gumurzu, yana mai cewa mayaƙan ƙasar sun tanadi kayan aiki da ƙarfin da za su jure tsawon rikici tare da jawo mummunar asara ga duk wani mai kai hari.

Shin kuna ganin wannan bazai iya jawo yaƙin duniya na 3 ba kuwa?




゚viralシ

01/03/2026

IRAN S**a ce sun shirya Tsabb Jini bai fi Jini ba!

01/03/2026

Wannan ita ce Amurka, ana tsaka da tattaunawa, sun kàshe Jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Khamenei. Kar ku manta sun sacé Nicolas Maduro, shugaban kasar Venezuela fa.

Yanzu, don Allah, ku da ake tattaunawa da ku kan matsala, ku ne kuma kuke ta’àddànci. Allah Ya yi gaskiya, wallahi.

“Suna faɗi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu.” Suratu Ali-Imran 3:167.

Mu ’yan Nigeria, musamman ’yan Arewa, babu abin da wannan zai tuna mana sai mu dage da addu’a. Wallahi babu wani abu da zai dakatar da Amurka a wannan duniyar sai Allah. Kuna ganin Iran da Venezuela kawayen Russia da China ne, amma me s**a tsinana musu?

Maganar cewa ana kàshe Kiristoci a Nigeria, kuma Amurka ta dage a kai, tabbas akwai manufa a ƙarƙashinta, sunce ana take hakkin Dan adam a Iran da Venezuela ma, a jiya kawai yara kanana yan makaranta sama da 80 s**a kàshe a Iran.

Addu’a ce kawai za ta kare mu daga sharrinsu. Ya Allah ka kare mu daga sharrin zalunci.

01/03/2026

LABARAI | ABIN MAMAKI DAGA HABASHA

Wani dattijo mai suna Isaac Adamo, dan shekaru 78, ya bayyana tarihin rayuwarsa da ya dauki hankalin jama’a, inda ya auri mata 23 tare da haifar da ’ya’ya 70.

Isaac Adamo na zaune ne a garin Malabi, yankin Oromia a ƙasar Habasha (Ethiopia). Ya auri matarsa ta farko ne yana da shekara 23, kuma cikin tsawon shekaru 55 da s**a biyo baya, ya kara aure har ya kai mata 23.

A cewarsa, bai wuce shekara guda ba tun da ya auri amaryarsa ta ƙarshe, wadda ita ce ta 23 a jerin matansa. A halin yanzu, ƙaramin ɗansa ko ’yarsa na da watanni uku, yayin da babban ɗansa ya kai shekaru 53.

Isaac Adamo ya shahara wajen kiwon dabbobi, inda a wani lokaci ya mallaki dabbobi sama da 800. Ya bayyana cewa yalwar dukiya ce ta sa yake yawan aure.

> “Nakan yi aure duk lokacin da nake so, saboda ina da shanu da yawa, ina da dukiya da kadarori,” in ji shi.
“Dogarona a rayuwa shi ne kiwon dabbobi; ina da raƙuma, shanu da awaki masu yawa.”

Ya kuma ce yana yin aure ne a duk lokacin da ya rabu da ɗaya daga cikin matansa.

> “Idan na ga mace mai kyau, sai na saki ɗaya daga cikin waɗanda nake tare da su, na auro wata,” in ji Isaac.

Matarsa ta farko ta rasu, yayin da a yanzu yake tare da mata uku kacal, bayan ya rabu da mata 19. Ya ce wasu rabuwar ta faru ne sakamakon saɓani, wasu kuma ba tare da wani dalili na musamman ba.

Daga cikin ’ya’yansa 70, akwai maza 36 da mata 34. Isaac ya bayyana cewa a yanzu ba shi da niyyar ƙara aure.

A cewarsa, idan aka haɗa ’ya’yansa da jikokinsa, iyalinsa sun kai mutum 279. Sai dai ya amince cewa dukiyarsa ta ragu a yanzu idan aka kwatanta da baya.

Babban ɗansa na da suna Ibrahim, yayin da ƙarama kuma ake kiranta Dahab. Isaac ya ce mutane da dama kan tambaye shi yadda yake kula da tarbiyyar wannan adadi na ’ya’ya, amma a ganinsa hakan bai da wahala matuƙa, musamman idan akwai dukiya.

Yanzu haka, labarin rayuwar Isaac Adamo na ci gaba da janyo muhawara da mamaki a tsakanin jama’a.

18/02/2026

DA DUMI-DUMI | Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufa'i, ya gaza cika sharaɗin beli da humumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa tu'annati EFCC ta ba shi a yau.

Sharaɗin belin dai shine; sai el-Rufa'i ya kawo wani Sakataren din-din-din (Permanent Secretary) da kuma wani darakta Janar a ma'aikatar gwamnatin tarayya.

Majiyar mu ta tabbatar ma na cewa; wani Sakataren din-din-din a ma'aikatar gwamnatin tarayya da ya fara zuwa ofishin hukumar EFCC domin tsayawa el-Rufa'i ya ji tsoron tsaya ma sa, inda ya janye daga tsayawa el-Rufai a hukumar ta EFCC.

Yanzu haka dai el-Rufai zai cigaba da zama tsare a hukumar ta EFCC — a daidai lokacin da itama hukumar nan ta ICPC ta aiko masa da takardar gayyata domin ta bincike shi.

31/01/2026

Halastaccen Sarkin Kano Sanusi!

30/01/2026

Munafurci ne wannan!

Majalisa ta ba da umarni a yi amfani da jiragen yaki da sojojin kasa don kai manyan hare-hare a wasu sassan jihar Gombe - Duba yankunan da za a farmaka a sashen sharhi.

Hoto: , (X)

30/01/2026

DA DUMI-DUMI | Sarkin Zazzau ya ɗauko yąƙi da ƙungiyar Izala a jihar Kaduna.

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa rikįci ya ɓarke tsakanin ƙungiyar Izala da mai martaba sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Bamalli, sakamakon bada umurni da yayi a rufe wasu manyan masallatan Juma'a na ƙungiyar Izala dake cikin garin Zaria.

Wannan umurni ya na ƙunshe ne cikin wasu takardu guda biyu, ma su ɗauke da sa-hannun sakataren majalisar masarautar Zazzau, Mal. Yusuf Abubakar Hayat da kuma Hakimin gundumar Zaria da Kewaye, Barr. Muhammad Sambo Shehu Idris.

Umurnin ya ce mai martaba sarkin Zazzau, ya hana sallahr Juma'a a masallatan Juma'a na malam Kabiru dake unguwar Bisa da kuma masallacin Juma'a na unguwar Fatika.

Sai dai kuma sarkin ya ce za'a iya gudanar da salloli 5 na kowacce rana da sauran karatukan addinin musulunci da aka yarda da su.

28/01/2026

I accepted 1 fan badge from King Indara.

28/01/2026

Er Jarida Mai Capacity!🥱

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Gombe