Musa Idris JB

Musa Idris JB

Share

Musa Idris JB Office Insight And Opinionon National And International News, Politics, Business, Entertainment, Spot, Financial

13/04/2026

Gaskiya Ne Sheikh Bello Yabo

Photos from Musa Idris JB's post 12/04/2026

ADC Za Ta Yi ‘Zanga-Zangan Yanke Kauna’ (Civil Disobedience) Kan Amupitan Kan Neman Ya Yi Murabus Daga Shugabancin INEC

Jam'iyyar ADC na neman shugaban INEC ya yi murabus bisa zargin goon bayan APC
Jam’iyyar ADC, ta buƙaci Farfesa Joash Amupitan, ya sauka daga muƙaminsa na shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasar wato INEC.

Jam’iyyar ta yi wannan kira ne bayan wasu sabbin zarge-zarge da s**a bayyana a kan shugaban na INEC.

An ruwaito cewar wasu tsofaffin rubuce-rubucen da Amupitan ya yi a kafafen sada zumunta, sun nuna yana goyon bayan jam’iyyar APC.

Sai dai fitaccen malamin jami’ar nan ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka, Farooq Kperogi, ya ce wasu tsofaffin rubuce-rubuce da ake alaƙanta Amupitan sun yana goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan na iya rage amincewar jama’a dangane da sahihancin INEC.

Batun ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta, inda ra’ayoyin mutane s**a bambanta kan gaskiyar waɗannan rubuce-rubuce.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce lamarin yana da matuƙar muhimmanci kuma zai iya shafar amincewar jama’a da tsarin zaɓe, inda ya buƙaci Amupitan ya yi murabus nan take.

Jam’iyyar ta kuma ce za ta ci gaba da zanga-zangan Yanke Kauna wato Civil Disobedience da ɗaukar wasu matakai har sai shugaban INEC ya sauka daga muƙaminsa.

01/03/2026

Na san da yawa daga cikin ku baku san me a rubuta a Zoben Sayyid Ali khamene'i ba, An rubuta cewa “Lallai Ubangiji na yana tare da ni”

HOTO📸 Iran Times

01/03/2026

Wannan ita ce Amurka, ana tsaka da tattaunawa, sun kàshe Jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Khamenei. Kar ku manta sun sacé Nicolas Maduro, shugaban kasar Venezuela fa.

Yanzu, don Allah, ku da ake tattaunawa da ku kan matsala, ku ne kuma kuke ta’àddànci. Allah Ya yi gaskiya, wallahi.

“Suna faɗi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu.” Suratu Ali-Imran 3:167.

Mu ’yan Nigeria, musamman ’yan Arewa, babu abin da wannan zai tuna mana sai mu dage da addu’a. Wallahi babu wani abu da zai dakatar da Amurka a wannan duniyar sai Allah. Kuna ganin Iran da Venezuela kawayen Russia da China ne, amma me s**a tsinana musu?

Maganar cewa ana kàshe Kiristoci a Nigeria, kuma Amurka ta dage a kai, tabbas akwai manufa a ƙarƙashinta, sunce ana take hakkin Dan adam a Iran da Venezuela ma, a jiya kawai yara kanana yan makaranta sama da 80 s**a kàshe a Iran.

Addu’a ce kawai za ta kare mu daga sharrinsu. Ya Allah ka kare mu daga sharrin zalunci.

28/02/2026

Yana Raye Shiya Jasu Sallar Isha'i Ma..

Photos from Musa Idris JB's post 10/02/2026

TINUBU BA ABOKINA BA NE:- El-Rufai

‎Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya ce bai taɓa samun wata alaƙar abota ta musamman da shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

‎Yayin wata hira da ya yi da Trust TV, El-Rufa'i ya bayyana cewa goyon bayan da ya bai wa Tinubu a zaɓen 2023 ya samo asali ne daga biyayya ga jam’iyya da yarjejeniyar siyasa, ba wai don zumunci ba.

‎Ya ce bayan wa’adin mulkin Buhari na shekaru takwas, akwai fahimtar cewa mulki zai koma Kudu, Tinubu ya zama ɗan takarar jam’iyya ne a wannan tsari.

02/02/2026

Kidnapped Nigerians left to Die as Poverty cuts off means of means to pay Ransoms

And People still call this type of Government Democracy?

Govt that Care for Elites and their Families is what we have in Nigeria

-Says Shariah Council President Dr Bashir Aliyu

19/01/2026

Farkon Tafiyar Ga Abunda Ya Fara Bullowa Dasu Fatawar Son Rai Da Malamai Sukamar Cha Saiya Ajiye Ya Koma Wai Mangaran-Malaman-Sunna Masu Sukar Sanarwar Yan Tatsine-Almajiran Buba-Marwa.
Allah Ya Shiryar

14/01/2026

@2026 AFCON Final

MAROCCO Vs SENEGAL
Insha Allah

Photos from Musa Idris JB's post 17/12/2025

Shugaban Karamar Hukumar Funtua Katsina, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya, Ya Sayawa Wani Maraya Sabon Takalmin Soso Tare Da Bashi Jarin Ruwan Leda 5, A Ranan Talata.

📷: FB/Amb Funtua

01/11/2025

AMURKA KE DAUKAR NAUYIM BOKO H$RAM ....

Dan majalisar Amurka Maisuna Scott Perry ya bayyana cewa Amurka ce ke daukar nauyin kungiyoyin dake ayyukan halaka al'umma a Nigeria...

Dan majalisar yana wannan jawabin ne a ranar 13 ga watan Fabrairu na wannan shekarar lokacin da ake tattaunawa a zauren majalisar akan ayyukan hukumar USAID wacce gwamnatin Amurka ke daukar nauyin ayyukanta...

Scott Perry yayi jawabi akan tarin hujjojin da s**a tattara wadanda suke nuna yadda hukumar USAID take bawa kungiyoyin tada zaune tsaye kudade da mak$mai duk saboda su hal@ka mutane a Nigeria ...

Idan mun dawo kan jawabin da shugaba Trump yayi a wannan rana, inda yake bayyana Nigeria a matsayin kasar dake halaka kiristoci, hakan na nufin kenan ita amurkan ce ke aikata ayyukan halaka kiristoci a Nigeria tunda sune suke da alhakin duk ayyukan kungiyoyi masu kash3 kash3 a Nigeria...

Akwai shaidar bidiyo dake nuna lokacin da Dan majalisa Scott Perry yake bayyana cewa Amurka ke daukar nauyin mun@nan ayyuka a Nigeria....

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Jekada Fari Gombe Street
Gombe
760214