Gombe Reporters

Gombe Reporters

Share

Sahihan Labaru Da Dumi Duminsu

04/08/2026

Hon Usman Santuraki dake Takara a Jam'iyar ADC ya bawa jama'a Jari ne a Wani Yunkuri na tallafawa Jama'ar Yamaltu Deba.

Kimanin mutum 1650 ne Daga gundumomi 11 na Karamar Hukumar.

Wannan shine karo na uku da Santurakin Ke yin irin Wannan tallafi.

04/08/2026

SANARWAR FADAR SHUGABAN ƘASA

Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami’an rundunar sojin Najeriya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙara albashin jami’an rundunar sojin Najeriya da kaso tsakanin kashi 30 zuwa kashi 80 cikin 100.

Kimanin jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da wannan sabon tsarin albashi.

A ƙarƙashin sabon tsarin, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba, 2026, jami’an da ke sama da mukamin Kanal (Colonel) za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100. Wannan ya haɗa da Brigadier General, Major General, Lieutenant General da General.

Jami’an daga mukamin Kanal (Colonel) zuwa Warrant Officer kuma za su samu ƙarin albashi na kashi 50 cikin 100, yayin da sojoji daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin albashi na kashi 80 cikin 100.

Sabon tsarin zai ƙara kuɗin albashin rundunar sojin Najeriya na shekara daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.

Shugaba Tinubu ya sha yabawa jarumtaka da sadaukarwar jami’an rundunar sojin Najeriya wajen yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma 'yan ta'adda a wasu sassan ƙasar nan.

A cewarsa:

> “Dole ne mu ci gaba da tallafa wa maza da mata da ke tabbatar da tsaron rayukanmu da dukiyoyinmu yayin da suke gudanar da ayyukansu na kare ƙasa.

> “Gwamnatinmu za ta ci gaba da bai wa jin daɗin sojoji muhimmanci, tare da inganta rundunar sojin Najeriya ta hanyar samar musu da mak**ai na zamani da fasahohin da suke buƙata domin gudanar da aikinsu yadda ya k**ata.

> “Mun yi imanin cewa babu wata ƙasa da za ta kai ga ci gaba ba tare da tsaro ba. Saboda haka, za mu ci gaba da tattara dukkan ƙarfin rundunar soji da sauran hukumomin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin dukkan 'yan Najeriya.

> “Ina kira ga jami’anmu da sojojinmu da su ɗauki wannan mataki a matsayin wata alama ta girmamawa da godiyarmu bisa irin hidimar da suke yi wa ƙasarmu. Tare, za mu yi nasara a kan duk masu son tarwatsa haɗin kan ƙasarmu.”

Bayo Onanuga
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Na Musamman Kan Yaɗa Labarai da Dabaru
4 ga Agusta, 2026

04/08/2026

Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Damfara da Ya Yi Karya Cewa Lauya Ne Hukunci Kan Sanya Kansa a Matsayin Lauya da Kuma Mallakar Hatimin NBA na Jabu a Legas

Mai shari'a A.M. Lawal na Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, a ranar Talata, 4 ga Agusta, 2026, ya samu wani mutum mai suna John Nwawuto Anoruo da laifin sanya kansa a matsayin lauya da kuma mallakar hatimin ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na jabu, tare da yanke masa hukunci.

Anoruo, wanda ke gudanar da wata cibiyar ba da shawarwari kan harkokin shari'a da ilimi a yankin Ikorodu na Legas, jami'an EFCC sun k**a shi ne a ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026.

Lamarin ya fara ne bayan ya gabatar wa EFCC ƙorafi mai kwanan wata 22 ga Satumba, 2025, a madadin wasu kwastomominsa kan kamfanin Global West Vessel Specialist Nigeria Limited.

Sai dai bincike ya nuna cewa ƙorafin da kuma takardar janye ƙarar mai kwanan wata 5 ga Maris, 2026, dukkansu suna ɗauke da hatimin NBA na jabu, wanda Anoruo ya amsa cewa ya saya daga wani cibiyar kasuwanci da bai bayyana sunanta ba a Legas.

Yayin bincike, mutumin mai shekaru 55 ya bayyana cewa ya samu digirin lauya daga Jami'ar Najeriya da ke Nsukka a shekarar 2018 ta hanyar karatun yamma, amma bai taɓa halartar Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law School) ba.

Bayan kammala bincike, Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a ranar Talata, 4 ga Agusta, 2026, a gaban Babbar Kotun Jihar Legas ta hannun ofishinta na shiyya ta biyu, bisa tuhume-tuhume biyu da s**a shafi amfani da hatimin NBA na jabu da kuma yin ƙarya cewa shi lauya ne.

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya zarge shi da amfani da hatimin ƙarya mai taken "Nigerian Bar Association" mai lambar SCN037400, da nufin a ɗauke shi a matsayin na gaskiya, wanda ya saɓa wa Sashe na 366(1) kuma hukuncinsa yana ƙarƙashin Sashe na 365(1)(x) na Dokokin Laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2015.

Tuhuma ta biyu ta bayyana cewa a ranar 4 ga Satumba, 2025, Anoruo ya gabatar da kansa ga EFCC a matsayin cikakken lauya mai lasisin yin aiki a Najeriya, tare da amfani da hatimin NBA mai lambar SCN037400, alhali lambar ta mallakin wani lauya daban ce.

Da aka karanta masa tuhume-tuhumen, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Bayan amincewarsa da laifin, lauyar masu gabatar da ƙara, Saadatu Mahmud Yabo, ta gabatar da jami'in bincike na EFCC, Umar Faruk Ahmad, domin bayyana yadda lamarin ya faru.

Shaidan ya bayyana wa kotu cewa EFCC ta karɓi wata ƙorafi daga lauya Adeyinka Olumide-Fusika mai kwanan wata 14 ga Afrilu, 2026.

A cewarsa, mai ƙorafin ya yi zargin cewa Anoruo ya shigar da ƙorafi a kansa da kamfanin lauyoyinsa, yana ƙaryar cewa shi ma lauya ne.

Ahmad ya ce bincike ya tabbatar da cewa lambar rajistar Kotun Koli da ke kan hatimin NBA da wanda ake tuhuma ya yi amfani da ita ta wani lauya daban ce.

Ya kuma shaida wa kotu cewa Anoruo ya amsa cewa ya samo hatimin NBA na jabu daga wani cibiyar kasuwanci a Legas, kuma ya tabbatar da cewa ba a taɓa karɓarsa cikin ƙungiyar lauyoyin Najeriya ba.

Shaidan ya kuma bayyana cewa wanda ake tuhuma ya samu Naira miliyan 7.5 daga shari'ar da ya karɓa, inda ya biya Naira miliyan 1.5 ga wani cikakken lauya domin ya gudanar da shari'ar a madadinsa.

Har ila yau, Ahmad ya ce lokacin da Anoruo ya amsa gayyatar EFCC, ya zo sanye da rigar lauya, sannan binciken da aka gudanar a gidansa ya kai ga gano hatimin NBA na jabu mai ɗauke da lambar rajistar wani lauya daban.

Ta hannun jami'in binciken, masu gabatar da ƙara sun gabatar da takardun shaida da s**a haɗa da ƙorafin Olumide-Fusika, bayanan wanda ake tuhuma, wasiƙun binciken da EFCC ta aika wa Body of Benchers da Kotun Koli ta Najeriya tare da amsoshinsu, rigar lauya da aka ƙwato daga hannunsa, hatimin NBA na jabu da kuma shaidar biyan Naira 300,000 cikin asusun dawo da kuɗaɗen EFCC.

Lauyan wanda ake tuhuma, G.E. Demkemefa, bai yi adawa da karɓar waɗannan hujjoji ba, inda kotu ta karɓe su tare da sanya musu lambobin shaida daga Exhibit 1 zuwa Exhibit 9.

Yayin neman sassauci, wanda ake tuhuma ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 2.5 ga mutumin da ya kawo masa shari'ar, sannan ya biya Naira miliyan 1.5 ga lauya wanda ya ɗauka ya gudanar da ita.

Daga nan, lauyar masu gabatar da ƙara ta roƙi kotu ta yanke masa hukunci bisa amincewarsa da laifin, tare da umartar a kwace dukkan kayayyakin da aka gabatar a matsayin hujja domin su koma hannun Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

A yayin yanke hukunci, Mai Shari'a Lawal ya ce:

> "Dangane da yadda wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa, kotu ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume biyu."

Sai dai lauyan wanda ake tuhuma ya roƙi kotu da ta tausaya masa, yana mai cewa wannan ne karo na farko da ya aikata laifi, kuma bai ɓata lokacin EFCC ko na kotu ba.

Ya kuma ce shi ne ke ɗaukar nauyin iyalansa da s**a haɗa da matarsa da 'ya'yansa biyar, yana roƙon kotu ta ci shi tara maimakon daurin kurkuku.

Daga bisani, Mai Shari'a Lawal ya ci tarar wanda ake tuhuma Naira 120,000 a kan tuhuma ta farko da kuma Naira 150,000 a kan tuhuma ta biyu, wanda ya kai jimillar Naira 270,000, kuɗin da za a biya ga Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Legas.

Kotun ta kuma ba da umarnin a kwace rigar lauyar da hatimin NBA na jabu da aka samu a hannunsa, a miƙa su ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun EFCC.

Dele Oyewale
Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a
4 ga Agusta, 2026

04/08/2026

Yan Bindiga Sun Kuma Karbi Lemuna daban daban kafin su ka saki Babban alkaline na na Jihar Kebbi.

03/08/2026

Ƙungiyar Ƴan Achaba ta Bawa Hukumar NEDC lambar yabo kan samar da Ayyukan Cigaba.

Rahoto- Hassan Lawan Koli

03/08/2026

Yadda Gwamna Inuwa Ya Ɗaga wa Ƴan Achaba Hannu lokacin da yake shigowa garin Gombe ranar Litinin.

🎥 - Hassan Lawan Koli

03/08/2026

Rashin Bawa Kananan 'Yan Kwangila Aiki Shine Musabbin Karuwar Talauci a Gombe.

🎥Hassan Lawan Koli/Muhammad Gombe
GABATARWA: Adamu Ali Tongo

Photos from Gombe Reporters's post 03/08/2026

LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Al'ummar Amada LCDA S**a Tarbi Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya Jim kadan bayan isowar sa Gombe bayan Ziyarar aiki a birnin tarayya Abuja.

📸 Abdul Noshaking

Photos from Gombe Reporters's post 03/08/2026

Tirela ɗauke da shanu ta faɗi a Tashan Dukku da ke Gombe

Wata babbar motar ɗaukar kaya (tirela) da ke ɗauke da shanu ta faɗi a shataletalen Tashan Dukku da ke cikin birnin Gombe.

Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya jawo cunkoso a yankin, yayin da jama'a s**a taru domin ganin abin da ya faru tare da ƙoƙarin taimakawa wajen ceto shanun da abin ya shafa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a kammala tantance yawan asarar da hatsarin ya haifar ba, kuma ba a tabbatar da ko akwai waɗanda s**a jikkata ko s**a rasa rayukansu sak**akon lamarin ba.

Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su fitar da ƙarin bayani da zarar an kammala bincike kan musabbabin hatsarin da kuma girman asarar da aka yi.

📸 BMC

03/08/2026

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi tsokaci kan muhawarar da ake ci gaba da yi kan ko ya dace malamai su shiga siyasa kai tsaye ko kuma su takaita ga wa'azi da koyar da addini kawai.

Muhawarar ta kara daukar hankali ne bayan yadda wasu malaman addini s**a shiga harkokin siyasa, lamarin da ya raba kan al'ummar Musulmi, musamman a Arewacin Najeriya.

Daga cikin fitattun malaman da s**a shiga siyasa tare da bayyana aniyarsu ta tsayawa takara akwai tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, da kuma malamin Musulunci mazaunin Sakkwato, Sheikh Bashir Ahmad Sani, wanda a watan Fabrairun 2026 ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jiharsa a babban zaben shekarar 2027.

Haka kuma akwai wasu malamai masu daraja da s**a taba rike muk**an siyasa, yayin da wasu ke ci gaba da rike muk**ai a gwamnatocin jihohi daban-daban.

Sai dai, daga cikin dukkansu, batun shiga siyasar Pantami shi ne ya fi daukar hankalin jama'a.

Masu adawa da shigar malamai cikin siyasa na cewa fagen siyasa ya cika da rikici, zage-zage da rarrabuwar kawuna, wanda bai dace da matsayin malaman addini ba.

Sun ce shiga siyasar jam'iyya na iya jefa malamai cikin cin mutunci, s**a, hare-haren siyasa da bata suna, lamarin da zai iya rage daraja da karfin tasirinsu a idon al'umma.

A cewarsu, ya fi dacewa malamai su ci gaba da bayar da shiriya ta addini, ba da shawara idan bukatar hakan ta taso, tare da rika jan kunnen shugabanni daga wajen gwamnati.

Sai dai masu goyon bayan shigar malamai siyasa suna ganin ba za a iya kawo sauyi mai ma'ana ta hanyar zama a gefe kawai ba. Sun ce mutanen kirki da nagarta su ma ya k**ata su shiga siyasa domin ba da gudummawarsu wajen gyara al'amuran kasa.

A cewarsu, idan malamai suna da ilimi, gaskiya da kwarewar shugabanci, bai k**ata a hana su neman muk**an zabe ba, maimakon su takaita ga wa'azi da addu'a kawai.

Muhawarar ta sake daukar sabon salo bayan fitowar tsohon Minista, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam'iyyar PDP.

Da yake tsokaci kan batun a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa babu wani laifi idan malaman addini s**a shiga siyasa tare da taka rawa kai tsaye.

A cewarsa, ma shiga siyasa da malamai za su yi ya fi zama suna tsayawa a waje suna yi wa 'yan siyasa addu'a kawai.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Beside Bima Lodge Gombe, Gombe Stat
Gombe