HaskeeMsk

HaskeeMsk

Share

Barka da zuwa shafin HaskeeMsk.Muna baku tabbacin insha Allah bazakuyi nadamar kasance wa tare damu ba a cikin wannan Shafi Mai albarka.

05/06/2026

In bayaga Muhammad Manzon Allah (saw),Fadi kara duk halittan Allah kacifkaf babu Wanda yakai Ali (as

wani yankin na jawabin jagora Sayyid Ibraheem Yaquob Zakzaky (h).

Photos from Sayyid Ibraheem Zakzaky Office's post 04/06/2026
04/06/2026

"Ranar Ghadir ita ce ranar da Manzon Allah (SAW) ya bayyana matsayin Amirul Muminina Imam Ali (AS) a gaban dubban Musulmi a Ghadir Khumm. Rana ce ta cikar addini, cikar ni'ima da tabbatar da jagorancin da Allah Ya zaɓa domin al'umma bayan ManzonSa. A wannan rana muna sabunta alkawarinmu ga Wilayar Imam Ali (AS) da Ahlul Baiti (AS), muna kuma roƙon Allah Ya tabbatar da mu a kan tafarkin gaskiya har zuwa ƙarshen rayuwarmu. Eidul Ghadir abin farin ciki ne ga masu son Aliyu, ranar godiya ga Allah bisa ni'imar shiriya da jagoranci."

02/06/2026

Wani bangare na jawabin jagora Sayyid Ibraheem Yaquob Zakzaky (h) a shekarun da s**a gabata.

20/05/2026

UWARMU GUDA UBANMU GUDA BAMAISO YA GANMU A WARE SAI MAKIYI NA JAGORAN MU ����

17/05/2026

ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA (1).....

Akwai mutane da dama da suke tasowa cikin rayuwa, wasu su rayu su mutu ba tare da duniya ta san dalilin zuwansu ba. Amma akwai wasu bayin Allah da tun kafin mutane su fahimce su, Allah Ya riga Ya tanade su domin wata babbar manufa. Irin waɗannan bayin ne idan ka duba rayuwarsu, zaka ga gwagwarmaya ce, juriya ce, haquri ne, da sadaukarwa domin addini.

Daga cikin irin waɗannan bayin Allah akwai Jagora, Sayyid Ibraheem Yaquob Zakzaky (H). Mutumin da rayuwarsa gaba ɗaya ta zama littafin gwagwarmaya, juriya da tsayin daka wajen tabbatar da Musulunci da soyayyar Ahlulbaiti (AS).

Tun farkon fara da'awarsa, Jagora(h) bai samu rayuwa cikin sauƙi ba. Ya fuskanci ƙunci, tsangwama, kulle-kulle, cin zarafi, da barazanar mutuwa daga masu mulki da makiyan addini. Amma duk da haka bai taɓa ja da baya ba.

Lokacin da yake ɗalibi a makaranta, ya fahimci cewa Musulmi suna rayuwa cikin duhu na jahilci da zalunci, sannan Turawan yamma da tsarin mulkinsu sun mamaye tunanin al'umma. Sai ya tashi tsaye domin wayar da kan mutane zuwa ga Musulunci na gaskiya. Wannan ne ya jawo masa ƙiyayya daga masu anfani da jahilcin al'umma(masu mulkin zalumci.

An tsare shi sau da yawa. An hana shi walwala. An gallaza masa. Amma duk lokacin da aka fito da shi daga kurkuku, sai a ga ya ƙara ƙarfin guiwa fiye da da. Domin mutum ne wanda ya fahimci cewa hanyar gaskiya ba hanya ce ta jin daɗi ba, hanya ce ta jarabawa.

Makiyan cikin gida sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun tarwatsa wannan harka. Wasu sun yi amfani da ƙarya da jita-jita. Wasu s**a shiga zuba wa mutane guba a zukata da sunan nasiha. Wasu s**a yi ƙoƙarin rarraba kan mabiya. Amma duk da haka, Allah Ya cigaba da kare wannan tafiya.

A waje kuwa, manyan azzalumai da masu tsoron tashin Musulunci sun haɗu domin ganin an dushe wannan haske. Sun san cewa idan mutane s**a farka daga barcin jahilci, to mulkinsu da tsarin danniyarsu zai shiga hatsari. Saboda haka s**a cigaba da shirya makirce-makirce iri-iri akan Jagora da wannan harka.

Kololuwar wannan zalunci ita ce kisan kiyashin Zariya na shekarar 2015. Inda aka kashe dubban almajirai da masoya Ahlulbaiti (AS), aka rusa Husainiyya Baqiyyatullah, aka rusa gidan Jagora, sannan aka kashe masa ‘ya’ya da iyalai cikin rashin tausayi.

Duk da wannan mummunan zalunci, Jagora bai ce a ɗauki makami ba. Bai kira mutane zuwa ramuwar gayya ba. Sai dai ya cigaba da kira zuwa haquri, juriya da cigaba da gwagwarmaya cikin hikima. Wannan abu kaɗai ya isa ya nuna cewa lallai wannan mutum akwai wata kariya ta Ubangiji tare da shi.

Domin da ba taimakon Allah ba, da tuni makiya sun gama da shi. Amma duk tarkon da s**a kafa masa, Allah Ya maida shi silar ƙara yaɗuwar wannan harka. Duk lokacin da s**a so dushe hasken, sai hasken ya ƙara bazuwa.

Yau wannan harka ta kai wuraren da makiya ba su taɓa tsammani ba. Akwai matasa da dama da s**a dawo zuwa ga addini saboda wa'azuzzukan Jagora. Akwai dubban mutane da s**a fahimci matsayin Ahlulbaiti (AS) ta sanadiyyarsa. Duk wannan kuwa bai zo cikin sauƙi ba, sai da jini, hawaye, wahala da sadaukarwa.

Lallai Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) zakara ne da Allah Ya nufa da cara. Domin ba kowa bane yake tsallake irin waɗannan jarabawa ya cigaba da tsayuwa akan manufarsa. Wannan hanya hanya ce ta annabawa da waliyyai, hanya ce ta haquri, juriya da sadaukarwa domin gaskiya.

Allah Ka ƙara kare Jagora (H), Ka ƙarfafa masa guiwa, Ka tabbatar da mu akan tafarkin gaskiya, Ka sanya jinin shahidanmu ya zama haske ga al'umma baki ɗaya.

Zamu ci gaba Insha Allah.
17/5/2025.
Hassan Kabeer Haskee ✍️

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Funtua?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Funtua Maska Of Nigeria
Funtua