Iambello143
By the grace of God we must become the change we wish to see in the world. I love you all my people's
14/02/2026
Mahaifi zai iya dawowa gida da gajiya mai nauyi.
Amma yana shigowa, zai ajiye gajiyar gefe guda, ya dauki yaransa yana wasa da su kamar ba shi ne ya sha wahalar rana ba.
Alhali takalminsa ya tsage.
Rigarsa daya ce take yawo a jikinsa.
Zuciyarsa tana cike da lissafin yadda zai biya kudin makaranta, kudin abinci, da maganin mahaifiyarsu.
Amma duk da haka, zaka ga yana fada musu cewa:
"Kada ku damu, komai akwai shi, kuma komai zai yi kyau inshaAllah."
Zai iya jure yunwa domin su koshi.
Zai iya jure sanyi domin su ji dumi.
Zai iya jure wulakancin kowa a waje, amma idan ya dawo gida, zai tsaya a matsayin "Sarki" kuma garkuwar da kowa yake alfahari da ita.
Wannan sam ba wasa ba ne...
Wannan shi ake kira mahaifi.
Shi ne mutumin da yake gina rayuwar wasu, alhali tasa tana rugujewa. Shi ne jarumin da ba ya bukatar lambar yabo, sai dai ganin yaransa sun zama mutane.
Allah Ya albarkaci mahaifanmu, wadanda suke raye Allah Ya kara musu lafiya da nisan kwana, wadanda s**a rigamu gidan gaskiya Allah Ya kyautata makwancinsu. 🤲
Wace kalma daya zaka iya cewa game da Mahaifinka? 👇
Iambello143
12/02/2026
Abu biyar (5) da zaka bincika alokacin zaɓar matar aure:
1. Gwajin aminci alokacin talauci:
Kafin ka aure ta, ka gwada amincinta a lokacin da kake da arziƙi da kuma lokacin da arziƙinka yayi ƙasa
Wasu matan zasu zauna dakai idan kanada arziƙi, dagabaya idan ka haɗu da jarrabawar karayar arziƙi sai su kasa jurewa
Shin tana iya jure matsin rayuwa ko ƙalubale?
Idan bata iya jure sauyin yanayi, ƙalubale ko jarrabawa, to kar ka aure ta.
Hanyar da zaka jarraba budurwarka:
Ka ɗauki tsawon lokaci batare da bata kyauta ba, idan tayi magana sai kace bakada zarafi. Ka nuna cewa kana cikin yanayin karayar tattalin arziƙi domin ganin yadda halayenta zasu sauya agareka.
2. Gwajin fushi:
Dole kasan yadda take sarrafa fushi
Idan mai saurin fushi ce, to karka aureta.
Ka motsa motsin zuciyarta. Ka ƙirƙiri ƙaramin rikici.
Ba don cutarwa ba, sai don lura.
Shin tana zagin ka?
Shin tana raina ka?
Shin tana ƙoƙarin rushe ka?
Ko kuwa tana nutsuwa acikin fushi?
3. Gwajin son kai:
Kana buƙatar sanin tana kula da kai da gaske, ko kuma abin da take samu daga gare ka kawai take baiwa muhimmanci
Ka dogara da ita na wani lokaci
Ka riƙa neman taimakonta akai akai
Mace mai tausayi zatayi ƙoƙarin nema maka mafuta idan kana acikin halin neman taimako ko ƙunci
Mace mai son kai zata janye maka idan kana neman taimakonta
Tausayi ba daga kalamai bane, tausayi yana cikin kyautatawa da hidimtawa miji.
4. Gwajin biyayya:
Biyayya ba rauni ba ce, amincewa ce
Shin tana yimaka biyayya idan ka yanke hukunci?
Shin tana jayayya da hukuncinka?
5. Ladabi da tsari:
Shin tana taimakonka wurin kula da dukiyarka, da hanaka almubazzaranci?
Wasu mata suna almubazzaranci da dukiyar miji, abinci da sutura
Mace mai almubazzaranci ba zata iya taimakawa miji ba, sai dai ta rosa mijin
Kuma mafiyawansu basa godewa miji bisa ɗawainiyar da yakeyi dasu. Kullum cikin kuka da yawan ƙorafi.
⚠️ Wallahi ku san matan da kuke aura, mafiyawan matasa su ke ɗebowa kansu wahala.
Iambello143
27/10/2025
ALAMOMI 5 DA KE NUNA MACE BA ZA TA DADE A GIDANKA BA:
1. Mai Girman Kai: Tana jin ita ta fi ƙarfin kowa, har da kai. Ba za ta ɗauki shawara ba.
2. Mai Son Gasa da Kai: Tana son ta nuna cewa ita ta fi ka, ko a kuÉ—i, ko a ilimi. Ba za ta bari ka zama "shugaba" ba.
3. Mai Yawan Kula Maza: Koda tana tare da kai, idonta yana kan wasu. Ba za ta kiyaye mutuncinka ba.
4. Mai Bijirewa Iyayenta: Idan tana iya yi wa iyayenta rashin kunya, taka ma ba za ta ji ba.
5. Mai Son Yanci Fiye da Kima: Tana son ta riƙa fita yadda take so, ba tare da izininka ba. Ba ta son "tsari" na gidan aure.
Ka auri mace mai tawali'u (humble). Wanda za ta girmama ka a matsayin mijinta, kuma ta gina gidanku tare.
Allah Ya tsare mu daga mace mai girman kai.
Amin🤲 ✍️
Asslam
Free your mind with any rubish focus your dream
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Delta State