Bintaeco 19
𝟭.𝟱𝗠 followers • 𝟭𝟯 following
21/11/2025
20/11/2025
Gaskiya ta fara fitowa akan batun kisan kare dangi a Najeriya. Sabbin takardu daga Ma’aikatar Shari’ar Amurka sun fallasa wani abu mai matuƙar hatsari:
Wasu kungiyoyin neman Biyafara a ƙasashen waje ne s**a kaddamar da yaƙin zargin cewa ana “kisan gilla ga Kiristoci a Najeriya.” Kamar yadda jaridar Guardian ta buga.
Wannan ya sa Donald Trump da Sanata Ted Cruz s**a bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai “takatsantsan kan ‘yancin addini.”
Sanata Cruz ya ce, “Babu ƙasa a duniya da ake zaluntar Kiristoci kamar Najeriya.”
Ya kawo Boko Haram da ‘yan ta’adda, eh, mun san su da laifinsu, amma ga hakikanin magana:
Wannan zargi na kisan kare-dangi ana shiryawa, ana ɗaurawa, ana turawa kasashen waje ne daga hannun waɗannan ‘yan Biyafara na dake zaune a kaşar waje.
Takardun DOJ suna da danganta da kamfen ɗin ƙungiyar United States of Biafra, ciki har da gwamnatin Biyafara da suke cewa tana “cikin hijira.”Sun ɗauki masu lobin siyasa a Washington, sun rattaba hannu a kan wasu takardu a Finland, suna ƙoƙarin nuna Najeriya a matsayin ƙasa mai kisan kiyashi, ba don magance matsalolin gida ba, sai don neman karɓuwa a Amurka.
Ɗaya daga cikin manyansu, Simon Ekpa, yanzu haka yana gidan yari a Finland saboda laifukan ta’addanci, zambar haraji, da tada fitina. Amma kuma shi ake sanyawa hannu a takardun da ke zargin Najeriya da kisan kare-dangi.
Takardun sun nuna wani abu mafi muni:
Saƙonninsu ana yi ne musamman domin jan hankalin wasu ‘yan siyasar Amurka, musamman magoya bayan Trump, da zancen cewa goyon bayan Biyafara zai “ceto Kiristoci” kuma zai takaita tasirin China. Ku saurara da kyau. Wannan ba wayar da kai ba ce. Wannan inji ne na siyasa da ake sarrafa shi daga ƙasashen waje. An tsara shi. Ana ɗaukar nauyinsa. An tura shi ne don canza yadda Turawan waje ke kallon Najeriya.
Waɗannan kamfen-kamfen da ake haɗawa da kalmomin “kisan kare-dangi” da “zaluncin addini” na iya kunna fitinar kabilanci a cikin gida, su kuma ɓata sunanmu a idon duniya.
20/11/2025
Allahu akbar
19/11/2025
Idan kanason kasan abunda yake faruwa a Maiduguri, to kaje ka kalli wannan film (Operation Red Sea 2018).
Duk abunda ka gani acikin wannan film, shi ke faruwa a Maiduguri, Jejin Sambisa, da Tafkin Chadi
-----------------------
Idan ka shiga makarantar koyon aikin soja, zaka fara a matsayin (recruit-trainee)
- Private Recruit
- Lance Corporal
- Corporal
- Sergeant
- Staff Sergeant
- Warrant Officer
- Master Warrant Officer
- Second Lieutenant
- Lieutenant
- Captain
- Major
- Lieutenant Colonel
- Colonel
- Brigadier General
- Major General
- Lieutenant General
- General (Chief Of Army Staff)
------------------------
(Brigadier General Musa Uba) wanda yan ta'addan ISWAP s**a kashe babban mutum ne a gidan soja
Matsayi biyu ne tsakaninsa da "Chief Of Army Staff"
"Brigadier General Musa Uba" yana jagorantar rukunin sojoji biyar (5 battalions) a fagen daga
Kowane rukuni akwai sojoji har guda dubu acikinsa:
1 battalion = 1000 soldiers
5 battalions = 5000 soldiers
Sojoji dubu biyar (5000 soldiers) ke ƙarƙashin kulawar "Brigadier General Musa Uba" 😭🥹
Allah yajiƙansa yayi masa rahama ameen
------------------------
⚠️ Kisan Brigadier General babban abun kunya ne ga ƙasa irin Nigeria
Yakamata gwamnati ta ƙara inganta kasafin kuɗin tsaro tare da nemo na'urorin fasahar yaƙi irin na zamani domin kawo ƙarshen wannan mummunan ta'addancin.
Haryanzu a nigeria muna amfani da tsohuwar fahar yaƙi ta hanyar kai samame a ƙasa, yayin da cigaba yazo a duniya ta hanyar amfani da fasahar zamani
- Amfani da jirage marar matuƙi (combat drones da surveillance drones)
- Artificial Intelligence (gano abokan gaba, sarrafa makamai ta hanyar satellites da radar)
- Amfani da makaman zamani domin kai hari daga nesa (cruise missiles da ballistic missiles)
- Electronic Warfare: ta hanyar lalata makaman abokan gaba, katse GPS, da lalata sadarwarsu
⚠️ Matuƙar Nigeria tacigaba da amfani da tsohuwar fasahar yaƙi, bazamu taɓa nasara akan Boko Haram ko ISWAP ba
Idan mun tura jirgin sama zasu kakkaɓo shi, idan sojoji sun kai samame a ƙasa zasu harbesu saboda sunfi sojojinmu ƙarfin makamai 📌
Alhassan Mai Lafia
19/11/2025
Shahararriyar mawakiyar Rap ta Amurka Nicki Minaj ta bi sawun shugaba Donald Trump, inda ta jaddada zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya duk da ci gaba da muso da fadar mulki ta Abuja ke yi.
A yayin wata zantawa da aka shirya a jiya Talata a birnin New York bisa jagorancin jakadan Amurka a MDD Mike Waltz, fitacciyar mawakiyar mai shekaru 42 a duniya ta gode wa Shugaba Trump kan yadda ya dauki wannan batu da matukar muhimmanci.
19/11/2025
19/11/2025
Click here to claim your Sponsored Listing.