Yakubun Bauchi Digital Vanguard

Yakubun Bauchi Digital Vanguard

Share

Welcome to Yakubu Adamu Digital Awareness Page

Photos from Yakubun Bauchi Digital Vanguard's post 28/07/2026

MASHA ALLAH: Kungiyar Kiristoci Ta Jihar Bauchi Ta Kai Ziyarar Girmamawa Ga Dr. Yakubu Adamu Tare da Bayyana Goyon Bayanta Ga Dukkan Yan Takarar Jam'iyyar APM

Kungiyar Kiristoci ta Jihar Bauchi ta kai ziyarar girmamawa ga Dr. Yakubu Adamu dan takarar gwamnan Jihar Bauchi a karkashin tutar Jam'iyyar APM domin nuna goyon baya ga takararsa da kuma manufofin jam'iyyar na samar da ingantaccen shugabanci

A yayin ziyarar shugabannin kungiyar sun bayyana cewa sun zo ne domin nuna hadin kai zaman lafiya da kuma tabbatar da goyon bayansu ga Dr. Yakubu Adamu tare da dukkan yan takarar Jam'iyyar APM da ke neman mukaman siyasa a fadin Jihar Bauchi

Kungiyar ta jaddada cewa ci gaban Bauchi na bukatar shugabanci na gaskiya adalci rikon amana da kuma shugabanci mai hada kan al'umma ba tare da la'akari da bambancin addini ko kabila ba Sun kuma bayyana cewa suna da yakinin cewa yan takarar APM za su kawo sauyi mai amfani ga al'ummar jihar

A nasa jawabin Dr. Yakubu Adamu ya nuna matukar godiya ga Kungiyar Kiristocin Jihar Bauchi bisa wannan ziyara da goyon bayan da s**a nuna Ya tabbatar da cewa idan al'ummar Bauchi s**a ba shi dama zai jagoranci jihar cikin adalci gaskiya da kuma tabbatar da cewa kowane dan kasa yana da damar cin moriyar dimokuradiyya ba tare da nuna bambanci ba

Ziyarar ta kara nuna muhimmancin hadin kan addinai zaman lafiya da kuma hadin gwiwar al'ummar Bauchi wajen gina jiha mai cike da ci gaba hadin kai da walwala ga kowa

Photos from Yakubun Bauchi Digital Vanguard's post 28/07/2026

Hon. Yakubu Adamu PhD Ikon Allah Sai Kallo.

A Tarihin Bauchi Babu Wani Dan Siyasa da Al'umma suke rige rigen Taimakawa ma Talakawa ta Hanyar Kungiyoyi Daban Daban don Nema mishi Soyayya a agurin Talakawa kamar Dr. Yakubu Adamu (Wazirin Giade).

Ba'a Taba Samun Dan Siyasan da Tun kafin Yaci zabe Alkhairan shi sun shiga Lungu da Sako kamar Wazirin Giade ba.

Kuma Hakan Yasamo Asali ne da Irin Kyawawan Halaiya da shi Mai Masallaci da Masallatan ke dashi a Wajen Ganin ya Taimaki Al'umma.

A kullum baida Wata magana kamar Yaya za'ayi a samu a Taimaki Marasa Karfi ?

Yaya za'ayi Taimakon ya Isa inda ya kamata ?

Su Waye na Gaba ya kamata a Taimake su ?

Wannan Halaiyan nashi shine yayi wa Mutanen Jahar Bauchi jagora wajen Rige rigen Ganin Kowa ya Bada Gudumawar shi don Ganin Nasaran Dr. Yakubu Adamu Dan Takaran Gwabnan Jahar Bauchi a Jam'iyar APM Mai Alamar Rogo .

Yah Allah Ka fimu Sanin shi , yah Allah Muna rokon ka da Budedden zuciya da ka bashi Gwabnan Jahar Bauchi a zabe Mai Zuwa 2027.

Photos from Yakubun Bauchi Digital Vanguard's post 26/07/2026

YANZU-YANZU: Daga Garin Jos, Jihar Plateau, inda mai girma ɗan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam'iyyar APM mai alamar rogo, Dr. Yakubu Adamu (PhD), tare da ɗan takarar Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdulrazak Nuhu zaki, da Engr. Shamsudeen Bala Mohammed, tare da sauran manyan jiga-jigan jam'iyyar, s**a kai ziyarar girmamawa ga babban malamin addinin Musulunci kuma jagoran Izala na ƙasa, Sheikh Dr. Yahaya Jingir, domin neman addu'a da albarkarsa.

Sheikh Dr. Yahaya Jingir ya nuna matuƙar farin cikinsa da wannan ziyara tare da yabawa Dr. Yakubu Adamu bisa kyawawan ayyukan alheri da yake gudanarwa a faɗin Najeriya.

A cikin jawabinsa, Sheikh Dr. Yahaya Jingir ya bayyana cewa Dr. Yakubu Adamu ya cancanci tsayawa takarar kowace irin kujera ta shugabanci a Najeriya, ba wai ta Gwamnan Jihar Bauchi kaɗai ba. Ya ce ayyukan alherin da Dr. Yakubu Adamu yake yi sun bazu a sassa daban-daban na ƙasar nan, kuma babu jihar da ba a ji labarin gudummawarsa ba.

Haka kuma, Sheikh ya yi addu'a tare da fatan Allah Ya ba Dr. Yakubu Adamu nasara, sannan ya ƙara da kira ga al'umma da su zaɓi nagarta da mutumin da zai yi musu adalci da ci gaba.

Muna miƙa godiya ta musamman ga Sheikh Dr. Yahaya Jingir bisa tarba, addu'o'i da fatan alherin da ya yi. Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.

Allah Ya dawo da tawagar gida lafiya, Ya kuma ba su nasara a dukkan al'amuransu. Amin.

25/07/2026

Indai chanchanta neh Gwamnan Jahar Bauchi Senator Bala Mohammed Abdulkadir yafi kowa sanin waya chanchanci ya gajeshi.

Zaban Yakubu Adamu Phd a matsayin tsayayyen dan takaran Gwamnan Jahar Bauchi karkashin jamiyyar APM adalcine ma talakawan jahan.

Dubi da yanda ya riqe mukaminsa na kwamishinan kudi bil haqqi da gaskiya, da kuma samo wa jahar hanyoyin cigaba na investment daga sassa na duniya.

Matashi shi ya kamancemu a wannan zamani na digital age, shine yasan meke gudana kuma yasan yanda zai kawar da duk wata damuwa ko annoba da zai tinkaro al'umma.

Yakubun Bauchi Digital Vanguard

24/07/2026

Alhamdulillah! Dr. Yakubu Adamu ya zama halastaccen ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da sunansa tare da sanya shi cikin jerin sunayen 'yan takarar da aka karɓa a hukumance domin zaɓen gwamna mai zuwa.

Wannan mataki na nuna cewa ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanada, kuma yanzu ya shiga sahun 'yan takarar da za su fafata a zaɓen.

Allah Ya ba shi alheri, Ya kuma ba Jihar Bauchi abin da ya fi zama alheri ga al'umma.

24/07/2026

Fatan Alheri Ga Dr. Yakubu Adamu

Dr. Yakubu Adamu na daga cikin mutanen da s**a fito da burin yi wa al'umma hidima ta gaskiya.

Mutane da dama suna kallonsa a matsayin jagora mai natsuwa, hangen nesa da kuma kishin ci gaban Jihar Bauchi.

Burinsa na ganin an samu ci gaba a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, tattalin arziki da samar wa matasa damar yin aiki ya sa mutane da yawa ke masa fatan alheri.

A wannan tafiya, abin da ya fi muhimmanci shi ne addu'a.

Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi ikon yin abin da ya dace, Ya shiryar da shi zuwa ga alheri, kuma idan mulki alheri ne gare shi da al'ummar Bauchi, Allah Ya ba shi nasara cikin zaman lafiya da adalci.

Allah Ya sa duk wanda zai jagoranci Jihar Bauchi ya kasance mai tsoron Allah, mai gaskiya, mai riƙon amana da kuma mai fifita buƙatun talakawa a kowane lokaci.

Allah Ya albarkaci Jihar Bauchi, Ya ba ta shugabanci nagari, Ya haɗa kan al'umma, Ya sa zaman lafiya, ci gaba da wadata su tabbata.

Amin.

12/05/2026

Big shout out to my newest top fans! Abdllah Ahmad

04/01/2026

ANNOUNCEMENT

The Yakubun Bauchi Ambassador’s Forum, Kaura Independent Communication, and Yakubu Adamu Influencers hereby invite members of the press, civil society organisations, party stakeholders, and the general public to a Press Conference in defence of:

His Excellency, Senator Bala Abdulkadir Mohammed The Executive
Governor of Bauchi State and Hon. Yakubu Adamu, PhD Commissioner of Finance and Economic Development, Bauchi State.

The press conference is convened to address recent developments, clarify facts, and reaffirm our collective commitment to constitutional democracy, due process, and good governance in Bauchi State and Nigeria at large.

Details are as follows:

Date: Monday, 05 January 2026

Time: 11:00 AM prompt

Venue: E4 Resort

All media houses, opinion leaders, party loyalists, and concerned citizens are encouraged to attend.

Signed:
Yakubun Bauchi Ambassador’s Forum,
Kaura Independent Communication and
Yakubu Adamu Influencers

NB: This strictly on Invitation.

Thank you.

03/09/2025

Big shout out to my newest top fans! Adamu Musa Yakda, Abdllah Ahmad

16/06/2025

Big shout-out to my newest top fans! Adamu Musa Yakda

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Bauchi