Da'irar Azare
An Bude Wannan Shafi Ne Domin Isar Da Sakonnin Harka Islamiyyah Na Musamman Na Da'irar Azare Dama Kasa Baki Daya.
_Har ila yau akwai wani aiki da ake so, wanda yake da muhimmanci, shi ne ku ɗauki alƙawari kai da ɗan uwanka; ka riƙe hannunka na dama da hannunsa na dama (masafaha), sannan sai kace; ‘Na yi ‘yan uwantaka da kai saboda Allah, na kuma yi musafaha da kai saboda Allah, na kebance ka da wannan saboda Allah, kuma na wa Allah alƙawari da Mala’ikunsa da litttatafansa da Manzonninsa da Annabawansa da A’imma Ma’asumai (A.S) cewa; in na zama cikin ‘yan Aljanna, kuma aka min izini na shiga Aljannar, ba zan shiga ba sai tare da kai.’_
_Babban magana! Wani ya taɓa bani hannu wai ko wuta ko Aljanna tare za mu shiga, nace ni ban yarda ba. Nace Aljanna dai na yarda, amma wuta ban yarda ba. Nace Allah ya sauwaƙe, kai meye naka na kawo batun wuta? Aljanna dai kawai. Allah ya sauwaƙe min shiga wuta. Wai in da zafi mu je tare, nace Allah dai ya sauwaƙe, alƙawari dai a kan Aljanna ne. Mutum ya yi alƙawari ko wuta ne a je tare? Aljanna dai Malam. In aka ce min in shiga Aljanna, zan ce ina wane? Sai mu shiga tare._
_To, yana da kyau rannan ka samu ɗan uwanka, masoyinka kai masa wannan alƙawari. Sai ya zama insha Allahu in ɗayanku ɗan Aljanna ne, ba zai shiga ba sai tare da ɗayan. Sai ya tsaya yace ina wane? Ai na riga na yi alƙawarin ba zan shiga ba sai da shi. To shikenan, ka ga in baka samu tsira ba, sanadiyyar ɗan uwanka sai ka samu, in sMu a wajenmu ziyara da rai ko ba rai duk ɗaya ne._
06/06/2022
“A Sakonnin Imam Khomeini (QS) ya yi ta amfani da Kalmar ‘Mustad’afin’ (raunanan da ake zalunta), raunanan mutane na ko ina, ba a ce maka wadanda ake zalunta din Musulmi kawai ba, Musulmi ne ko Kirista, zalunci bashi da kyau a kan kowa. Ba a goyon bayan zalunci a kan kowa.
“Wato mu bamu yarda da zalunci ba ko a kan wane ne, hatta ko da azzalumi aka zalunta, za mu ce wannan kam an zalunce shi, domin muna so a yi masa adalci. Misali, da za a k**a shi, sai a ce a yi masa wani hukunci wanda ya wuce laifin da ya yi, za mu ce an masa zalunci. Allah Ta'ala yana cewa: “Ku yaki masu yakarku a tafarkin Allah, amma kar ku yi shisshigi, Allah baya son masu shisshigi.” (Baqara: 190).
“Ko mutum yana yakarka ne, ko abokin gabanka ne, ba a ce ka masa shisshigi ba, ba a ce ka zalunce shi ba. Wannan nizamin addini kenan. To sai ya zama Imam ya ta jaddada cewa “A tallafawa wadanda ake zalunta ko su wane ne.”
— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabinsa na Tunawa da Imam Khomeini (QS) karo na 33 a shekarar 2022.
29/05/2022
Update:
Students from the various Fudiyya Islamic schools, who are about to graduate from the Quranic memorization classes, visit leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) today at his Abuja residence.
Hausa:
Dalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin saukar Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), yau Asabar a gidansa dake Abuja.
28/05/2022
13/05/2022
"Wannan yakarmu ake yi amma kuma duk ana ta baganniya. Yanzu mutane sun zama babu wanda zai yi magana a saurare shi, sai an ce shi wane ne, sai a duba kai wane ne, kai dan mene ne kai. Ta haka suke kallo. Wannan abu da ban al’ajabi. Dama yana cikin yakin da s**a kawo mana, sai da s**a kawo yakin rarraba kawukan mutane sannan s**a shigo da wani nau’in yakin, sai ya zama kowa yanzu ya yi magana sai ka ga shi daban-daban ne kawai.
"Idanun mutane ya rufe. Su ba su karbar gaskiya idan sun ji ta sai daga wurin wane s**a ji. Kuma ba gaskiya kadai, idan Malam wane Malaminsu ne komai ya fada ya yi daidai. Gaskiya ya yi, ko ba daidai bane, daidai ne. Idan ko wancan Malam ba Malaminsu bane, to komai ya fada ba daidai bane. Haka ake yi? Ita gaskiya sunanta gaskiya, inda ka ganta sai ka ce haka take. Amma inaa. Yanzu an shamakancin mutane an sa musu irin wannan tunanin kai kawai kowa da kungiyarsa. Kowa da kungiyarsa, wannan kungiyanci ya shigi mutane, ya zama shi ne ya zama ginshiki ya hana su gane komai".
*-Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin ganawarsa da wakilan bangarorin Harka Islamiyya a ranar Juma'a 6 ga watan Shawwal 1443 daidai da 6 ga watan Mayun 2022 a gidansa dake Abuja.*
09/05/2022
"Wato muna wata irin kasa ce da komai ya faru, in musiba ta samu wani mutum, sai ka ga k**ar ma har murna suke yi. Sai su yi ta murna. Ka san da ban mamaki ko? Idan musiba ta samu wani sai ka ga wani yana murna. Shima sai tasa ta zo, sai ya yi bakin ciki, sai wani kuma shima ya masa murna. Sai ta je ga wancan, ka ga ba wanda ya san yaushe za ta kare kenan.
"Yanzu wa ya san ya al'amari zai kasance nan da baɗi, ko kuma bayan shekara biyu zuwa uku? Tunda abubuwan suna gudu ne ba kadan ba, gudu suke ba kadan ba. Da ana bin jirgin kasa, an fi aminci, to yanzu jirgin kasan ka ga abin da s**a yi masa. To daga nan kuma ka ga yanzu ba aminci kenan a jirgin ma ko da an gyara shi....
"Su abin da kowanne (daga Mahukuntan Kasar nan) yake da bukata shine a bashi mukami, ala bashi a yi duk abin da aka ga dama. Ko me aka ga dama a yi, shi dai a bashi mukami. To. Idan ka ce ga mafita, mutane s**a ce ba haka nan bane. Ya za ka yi da su? Ba sai ka kyale su ba? Muce to shikenan ku nemi mafita inda za ku samu. Amma an ce musu ga mafitar, sun ce ba haka bane.
"Wasu su kan ce eh gaskiyarka ne, musulunci din ne mafita, amma fa kai kana nufin Shi'a ne, mu kuma ba za mu yi Shi'a ba. Ta wani dan Tawayiyya yace, wai yanzu in ma aka yi 'revolution' a kasar nan za a kafa Gwamnatin Shi'a ne, shi kuma da a yi shiaa gara ma a cigaba da Dimukuradiyyar. Yace gara 'Statuesque' da ISLAM wanda shi a wajensa sunansa Shi'a. To sai mu ce ai ba wata matsala, kai ka yi Sunnah Islam din mana. Shi kuma ba zai yi ba. Sunnah Islam din nasa shine ya bi azzalumai. Ya samu nasa kason.
Wani yanki daga Jawabin Jagora yayin Ganawa da wakilan yan uwa a gidan shi dake Abuja.
06-May-2022
08/05/2022
TSOKACIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KAN HALIN DA KASA KE CIKI
"Wannan irin ƙasa, mutane suna ta ɓaganniya, ana yaƙarku amma ba ku gane ba. (Ana kaɗa ku) k**ar shanu. Ka san saniya ina ruwanta in ma ƙwata za a kai ta (a yanka)? Ana tafiya tana cin ciyawarta.... Amma mutum wanda yake da hankali, kuna gani ana neman a ƙarisa ku, a gurgunta ku da ƙarfin tsiya.
"Har ma an riga an gama gurguntawar, ana ta ta yi ne, kudinku baya sayan komai. A 1980 Dala 1 ne Naira 2, Yanzu Naira 570+ ne Dala 1, amma da kuwa Naira 2 ne Dala 1. To kuma amma wai mu ke da 'Golden Zone', amma kudinmu bai da daraja.
"Mu nan irin diban 'Gold' din da suke a kewayen Zamfara din nan, Helicopters suke zuwa da shi su yi ta diba, har mutane sai su ce sun ji karar jirgin sama, wasu Helicoptoci ne, kuma 'Gold' ake diba a yi waje da su, ba tare da biyan ko kwabo ba. Kuma su wadanda ake cewa shugabannin sun sani. Su abin da ya dame su kawai a basu nasu kason.
"Kuma ni na lura magana ma in ka yi ma (k**ar) ba amfani, saboda su mutanen kasar nan ma in ka yi maganar ma suna cewa kai mahaukaci ne. Wata rana da nake magana din nan, su wadanda nake maganar don su lura amma ba su damu ba, amma sai aka ce har wani General ya daki tebur, yace wannan mutumin 'is dangerous!' ka ga yana magana da talakawa ne. Lokacin da nake cewa ku gane ba wata Boko Haram, mai suke diba, yanzu haka akwai rijiyar mai 25 a Borno, mai ake diba. Shine ya bugi Tebur yana cewa akwai hadari don ana fadawa talakawa ne. To su kuma talakawar ba su damu ba ma....
"Wato muna wata irin kasa ce da komai ya faru, in musiba ta samu wani mutum, sai ka ga k**ar ma har murna suke yi. Sai su yi ta murna. Ka san da ban mamaki ko? Idan musiba ta samu wani sai ka ga wani yana murna. Shima sai tasa ta zo, sai ya yi bakin ciki, sai wani kuma shima ya masa murna. Sai ta je ga wancan, ka ga ba wanda ya san yaushe za ta kare kenan.
"Yanzu wa ya san ya al'amari zai kasance nan da baɗi, ko kuma bayan shekara biyu zuwa uku? Tunda abubuwan suna gudu
02/05/2022
An Nuna Goyon Bayan Palastine A Da'irar Azare A Masallacin Idi.
Ayau Litinin 1 ga watan Shawwal dai-dai da 02-May-2022 Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky (H) sun gudanar da Muzahara zuwa Masallacin Idi, Muzaharar da aka fara gudanarwa ta fara daga kofar gidan Wakilin Yan uwa na Garin Malam Aliyu Abubukar Dawod k**ar yadda aka saba duk shekara.
Tawagar Yan Uwan sun rike banners masu dauke da Foton Jagora Sheikh Zakzaky tare da Tutocin kasar Palastine domin nuna goyon baya ga raunanan Palastine din, Gefe guda masu jerin gwanon sun yi kira ga Gwamnatin Nigeria akan ta gaggauta sakarwa Malamin Passport din sa domin ya samu damar Fita neman magani.
*MediaForumAzare
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Azare
07046431819