Yantacciya
Shafin an samar dashine Domin Zakulo labaran Gaskiya daga sako da lungun Duniya
29/01/2026
🇮🇷 — Rundunar Sojin Ruwa ta Iran da Rundunar Sojojin kare Juyin Juya Halin Musulunci za su gudanar da atisayen sojojin ruwa nan ba da jimawa ba.
Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC za ta gudanar da atisayen jiragen ruwa na wasan Wuta kai tsaye a gabashin mashigin Hormuz, ciki har da yankunan da jiragen ruwa na kasa da kasa ke aiki. Ana sa ran samun cikas, kuma wannan atisayen zai nuna karfin Iran na dakile jigilar jiragen ruwa idan Amurka ta kai hari.
Rundunar Sojin Ruwa ta Iran, tare da hadin gwiwar Rundunar Sojin Ruwa ta Rasha da Rundunar Sojojin China za su gudanar da atisayen jiragen ruwa a Tekun Oman. Abin lura shi ne, an ga jirgin ruwan USS Abraham Lincoln a can 'yan kwanaki da s**a gabata, a cewar bayanan sa ido kan jiragen sama na jama'a da ke nuna tashin jiragen saman Amurka a yankin.
Prof Ibrahim Maqari Ya Maida Martani Ga Maganar Trump.
07/08/2025
K**a Sowore Zalunci ne, A Sakeshi Haka Nan.
26/07/2025
Bayahude ba ya bukatar ka amince da shi, a'a ya na buƙatar shugabanka ya mallake ka ko ta hanyar kishin ƙasa ko ta hanyar addini. Sannan shi kawai zai mallaki shugaban ka. Kaga kenan ko ka ƙi ko ka so ya riga ya mallake ka.
Misalin aƙidar a bi shugaba mai mulki sau da ƙafa ko da fasiƙi ne kamar kulle kai ne a cikin keji ko akurki sannan ka miƙa wa mai son tsare ka makullin.
Wannan dalilin ne ya sa musulmi Sama da biliyan ɗaya a duniya su ka gagara ƙwatar ƴan uwansu a GAZA daga hannun ƴan tsiraru da basu wuce dubu dari bakwai ba tsawon shekaru saba'in.
ALLAH YA CE: SHIN BA ZA KU HANKALTA BANE????
© Hakim Raajii
24/07/2025
📸Yadda Huda Abu Al-Naja ke kallon hoton ta kafin yunwa ta canza mata halitta 🥲
K**ar yadda kuke gani cikin hotuna wannan yarinya mai suna Huda Abu Al Naja mai kimanin shekaru 12 a duniya ke riƙe da hoton ta da aka ɗauka kafin Isra'ila ta jefa su cikin ƙangin azababbiyar yunwa.
Huda Æ´ar yankin Al-Mawasi ce dake Kudancin zirin Gaza, tana fama da matsananciyar yunwa wadda a yanzu ake tsammanin har ta kamu da cutar "Celiac disease".
Huda É—aya ce daga cikin dubbunnan Palasdinawa da yunwa ta illata sakamakon toshe hanyoyin shiga da abinci zirin Gaza da Isra'ila ta yi.
ABS Radio - Daga Gaza
Kaso 70 na ƙarfin Amrk na sama da ruwa ya tunkari Yammacin Asiya inda za a yi Jana'izar Tinƙahon Duniya.
Za su iya yin amfani da MOAB (Mother of all Bombs) a kan Ira*n.
Deep state ta anshe ragamar jagorancin Amrk. Mahaukacin Kare ya rusunawa masu gidansa, sun shafi kansa sun ce good boy.
To daga nan ne Jahimu za ta buÉ—e, ba akan Iran kaÉ—ai ba, a kan Duniya.
Kusan shekara guda guda kenan munata rubutu a kan abun nan. Har Alƙalami ya fara gajiya.
Ba tsorata Mutane muke son yi ba.
Amma kowa ya sani, ba taɓa sauya Order ta Duniya ba tare da an yi uwar watsi ba.
Gumurzu ne zai fara tsakanin great reset da great awakening. Tsakanin globalist north, da global south. Yanzu muna a baƙin gate a tsugunne, muna jiran a buɗe kofa. Idan an buɗe ba za ta rufe ba sai kowa ya shiga.
الملØÙ…Ø©
Yawan ƙarafa na faɗa an fi Iran. Ba yawan ƙarfi ba. Ƙarfi na Allah ne kuma ya bawa muminai.
Tabbas Iran za ta jigata. Amma za ta buwaya.
Al'amari ne zananne, tun ranar gini.
Shamsudeen Hassan
WANI KARATU!
ba kowa bane ya lura da cewa wasan kokawan turai wanda ake yin sa daga kai sai dan kamfai, wrestling, ko kuma wasan dambe boxing da ake yi da gajerun wanduna idan ka zama na daya a duniya wai belt za'a baka! Duka wandunan da dan kamfan da gajeren wandon babu wanda yake amfani da belt! Ka taba lura da haka?
Wasan damben hausa wanda sai an nade maka hannu domin ka ji dadin kai naushi hannun a daure yake tamau amma bayan ka zama zakara a qasar hausa sai a baka takobi, takobin da ka ciwo da, daurarren hanu ta ina zaka iya sarrafa shi?
ABIN LURA!
shi wawantar da al'umma tare da hana musu yin nagartaccen tunani na ajiye komai a muhallin sa bai taqaita iya yan' Nigeria ba! Duniya ne baki daya,
Amma mafi munin ciki shine na malam bahaushe wanda shi an daure maka hannu tamau sannan an baka takobi,
WATO AN DAURE MAKA TUNANIN KA TAMAU SANNAN AN BAKA YAN'CI,
Yadda alqalan wasannin can dana yi misali dasu suke jan ragamar duk wani motsinka haka anan ma malamai suke jagorantar daure maka tunanin naka ka tamau! Su hana ka yancin tunani,
Idan ka kwance tunanin ka daga wancan mugun daurin tare da kwace shi daga hannun miyagun malamai zaka gane cewa banajin cikin nasarar da hulk hogan ko warriors da su hit man s**a samu a kokawar wrestling, ko kuma Muhammad Ali da mike tyson irin su deontey da Anthony joshua a fagen boxing a wannan zamanin s**a samu akwai wata gudunmawar malamin addini ko guda daya cikin ta!
Idan kana son zama me nasara kuma me yan'ci ka wai ka yaqi zalinci.
© Shehu Abumajid Abu Bakara.
09/04/2024
DAN AREWA DA WAWAN TUNANI 2
Zanga Zanga wani aikine da ya kunshi bayyana mastayar wani mutum ko gungun mutane akan wani abu a bayyane ta hanayar Furtawa ko nunawa domin jama'a su shaida.
Irin wannan ta faru a ranar da aka bayyana Addinin Musulunci a sarai, inda Sahabbai s**ayi Jerin Gwano Daga gidan Arqam bin Abul Arqam (R.A)
inda musulmai suke Yin taron Addini a asirce, zuwa jika dakin Ka'aba mai Girma .
suna Shelanta wadannan Kalmomi
"Allah ÆŠayane Kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Alihi Manzonsa ne"
Ana jifansu ana Dukansu , haka s**aci gaba da wannan Jerin Gwano Har Jikin Dakin Ka'aba mai Daraja.
Halasci Ko Haramcin Zanga Zanga a Musulunci ya dogara ne da sakon da Zanga Zangar take isarwa.
Sakon Halas ne ko Haram, shine zai Fassara Zanga Zangar a Shari'ance.
Domin A addinin Musulunci komai Asalinsa Halas ne , har sai an sami Haramcin aikatawa.
Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?
Eh tabbas Zanga Zanga tana da Amfani kwarai da gaske, domin itace kadai hanaya ta kwanciyar hankali wacce Al'umma suke iya bayyana matsayarsu akan wani abu ba tare da sun cutar da kowa ba.
Wannan Tsarin na Bayyana matsayar Al'umma itace ta Bambance Bawa da 'Yantacce, itace ta banabance wayayye da Kidahumi, itace ta Bambance Wanda yasan ciwon kansa da wanda bai sani ba.
Zanga Zanga ta samar da Mafita ga Al'ummomi masu yawa, akan wasu tsare-tsaren da aka dankara masu wanda yake tauye masu hakki.
Misali shine Zanga Zangar da kungiyoyin gwagwarmayar Africa ta Kudu s**ayi ta Allah wadai da nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu.
Wanda aka fara tun 1912 har 1992 Ya zama jigo ga gwagwarmayar neman 'Yancin Africa ta Kudu, kuma sila A samun 'Yancin kansu.
Zanga Zangar da Akayi a Nigeria ma Lokacin mulkin Jonathan akan kara kudin man fetur tayi tasiri, domin kuwa tasa dole ya janye kudirin karin kuÉ—in man a wancan lokacin.
Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?
Eh tabbas duk daga inda kayi Zanga Zaga a Duniya domin nuna goyon baya ga wasu al'ummar da ake zalunta to yana taimakawa waÉ—an da aka zalunta ta ta hanyoyi masu yawa, daga ciki akwai karfafa Gwiwa cewa Ba'a manta dasu b akwai waÉ—an da s**a tare dasu a neman 'Yancin da suke , basu kaÉ—ai bane.
Waɗan da suke zaluncin suna na muradunsu a kowacce kasa a duniya, dan haka duk ƙasar da al'ummar ta duk fito s**ayi Allah wadai da Zaluncin da akewa raunana a wani waje to Ita kasar da take aikata wancan Zaluncin tana da wakili a kasar da kake Kuma sakon ka yaje gareshi , kuma sun tabbatar baka tare dasu a Zaluncin da suke, kuma zaka taimakawa waɗan da ake zalunta Daduk abinda kake iyawa, Hakan Barazana ce Babba Ga Azzalumi.
Domin Munga yadda Zanga Zangar da akayi a Libiya Yankin Bengazi ta shafi Amurka kai tsaye, har ta ki ga rufe Ofishin Jakadanci na Amurka a Libya É—in.
Kuma mmunga yadda zanga Zanga tasa Amurka da Isara'ila sake Mugayen manufofin su masu yawa a Iraq, Jordan da sauran ƙasashen da s**a yadda da yin wani yunkuri domin kawo sauyi.
Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?
Idan Al'umma Ta yadda aka kwace mata 'Yancin yin Zanga Zanga to an maida wannan Al'ummar K**ar bayi, domin za'ayi ta korasu kamar dabbobi babu Mai kiwo, kuma basu da wata hanya ta nuna rashin amincewarsu akan wani tsarin da aka dankara masu.
Shiyasa Azzaluman masu mulki s**a dukufa wajen ganin sun Raba Al'umma da wannan 'Yancin da Addini ya basu kuma Tsarin Mulkin Demokradiyya ya basu.
domin ta Hakane kadai cikakkiyar bautarwa zai yiwu akan wannan Al'umma.
Rushin Gwagwarmaya da kwatar 'Yanci daga Azzaluman masu mulki shine kadai zai bawa duk wani mai son ya rayu cikin 'Yancin Addini da zamantakewa, Mafita da yake nema domin rayuwa cikin Aminci.
~Ibn Abubakar Alhausawy
06/04/2024
DAN AREWA DA WAWAN TUNANI (1)
Ya ishi mutum Jarrabawa Allah yayi shi a Nigeria kuma Arewacin Nigeria, domin kuwa In Allah ya Azurta mutum da Fahimtar abubuwan da suke faruwa a kewaye dashi gwargwadon hali, to kullum zai dinga kwana yana tashi cikin damuwa da halin da al'umma take ciki.
To saide ita kuma Al'ummar mafi yawanta basa lura , kuma basa gane hakikar halin da suke ciki, kuma suna gaba da duk mai kokarin Nuna musu wannan halin da suke ciki domin a fara kokarin samo hanyoyin maganin matsalar.
To ya zakayi da wanda Baima yadda yana cikin matsala ba b***e ya fara tunanin hanyar Da zaibi domin Maganin ta ?
Idan ka duba a kewaye dakai sai kaga wani mutum wanda Malaman sa s**a hana masa 'Yancin yin tambaya, sannan s**a hana masa 'Yancin yin bincike, Saide abin da s**a fada masa kadai shin ma'auninsa, idan kace dashi, Ya kamata ya dinga Tambaya sannan ya dinga bincike domin nemawa kansa amsosin wasu daga matsalolin da s**a dameshi , sai yace dakai , ai tunda akace dashi karya yayi tambaya kuma kar yayi bincike, to Ya Yarda, kuma matsayar da kenan , To irin wannan mutum Ya zakayi dashi ?
A wanan Al'ummar tamu ce zaka waiga kusa dakai sai kaga wanda wanda Aka baiwa wani hakkinsa ta hannun wani , shi wanda Aka baiwa hakkin nasa ya bashi ya cinye masa hakkin nasa, Saika bashi shawara kace, kaga tunda an baiwa wane Hakkin ka kuma ya cinye kana iya bin kadin hakkin ka dalilin da yasa ma akayi kotu da jami'an tsaro kenan , Sai Shi kuma yace dakai , ai Ba rabo bane domin Allah ne bai nufi kudin su iso gareni ba, idan kuma kace dashi Ai Allah ya riga ya bashi wanine ya cinye masa, Sai yace dakai Baka da Tauhidi, saboda kaki yadda da kaddara.
to ya zakayi da irin wanan mutum wanda bisan Dalilin da Yasa Allah zai yi Hisabi shine saboda wasu bayi suna cinye hakkin wasu bayin. ?
A wannan yanayin na kunci da damuwa da wasu mutane s**a jefa al'umma a ciki da gangan idan kayiwa mutane da dama bayanin haka basa ganewa sai s**e ai Allah yaso ya gansu cikin wannan Kangin Bauta kunci da damuwa.
Idan kace dasu ai Tunda Allah ya ajiye Arziki na Zinariya, Azurfa, kasar noma , man Fetur, Iskar gas, Kogonni, Hasken rana da sauransu, Ai ya baku arziki, sai yace dakai ai A'a ai hakkin amfani da wannan Azikin masu mulki ne kadai suke dashi , idan ka tambaye shi to Meyasa masu Mulkin basa amfani da arzikin wajen inganta rayuwar al'ummar kasar?
sai yace dakai wai Allah ne bi nufiasu mulkin da suyi Adalci ba, Ya yadda ya jingina Mummuna ga Mahalicci akan ya jingina ga Mai Mulkin da yake zaluntar sa, shin ya zakayi da irin wadannan mutanen ?
A wannan Kasa tamune Azzaluman masu mulki s**a gano Amfani da malamai wajen Kamfen na siyasa shi yafi komai sauki, Ga Araha ga Biyan buƙata, Sannan Ga kariya ta musamman a duniya, su tafka sata da gangan mai gurgunta tattalin arziki, Daga sun ɗan sanya Malamai na Fada kadan , shikenan, sai a jinginawa Allah kuncin da Satar Azzalumin mai mulki ta Kawa talakawa, shinen Sai ace da talaka ai Tauhidene jure wannan kuncin rayuwa kuma akwai lada mai girma.
haka nan talaka zai yarda kuma yayi biyayya da nufin samun lada, bayan Malam ya dade da karbar nasa ladan daga cikin hakkin talakawa da aka sace.
shin ya zakayi ka Fahimtar da irin wadannan mutanen cewa Ba Allah ya dora masu Kunci da wahalar rayuwa ba, hakan ya faru ne saboda wasu sun sace Arzikin da ya kamata ayi amfani dashi wajen saukaka wa rayuwarsu?
Jarrabawace ta Kasancewa a cikin wannan Al'umma wacce aka haÉ—u masu mulki da Malaman Fada aka daure mata Kwakwalwar ta , aka hana ta tunani mai kyau akan mokomarta , aka hanata duk wani yunkuri ko motsin da zai kai ga 'Yantar da kanta.
Ana cutar da ita ta hanayar amfani da imanin ta addininta da riko da Malaman ta shugabanninta.
Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?
Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?
Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?
Mu hadu a Rubutu na Gaba.
~Ibn Abubakar Alhausawy
27/02/2024
KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (2)
A Rubutunmu na Farko Munyi bayanin yadda masu Bautar da Al'umma suke karantar ta ciki da bai, kafin su bautar da ita, ta yadda Bazasu sami Turjiya ba daga waÉ—an da suke Bautarwar, inda wasu da ake bautarwar ma su kansu Basusan ana bautar dasu ba.
Matakin Da Masu mulkin mallaka suke bi domin tabbatuwar mulkinsu.
To bayan Masu mulkin mallaka sun karanci Al'ummar da suke yiwa mulkin mallaka to akwai hanyoyin da suke bi domin Tabbatar da wannan mulkin nasu, daga karantar Al'ummar da Sukayi, tunda sunsan Karfin Al'ummar da kuma Raunin ta.
Hanyoyin da 'Yan Mulkin Mallaka suke bi wajen Sarrafa Al'ummar Nigeria, Africa dama duk inda suke mulkin mallaka a duniya.
Tsarin Mulki: Soja Ko Farar Hulla ko Sarauta.
Wajen Tsarin Mulki suna samar da tsarin mulki ne da bazai taɓa cin karo da Muradunsu na mulkin mallaka ba, koda kuwa su waɗan da ake mulka suna tsammanin suna da 'yanci , to duk abinda zasuyi bazai wuce iyakar da 'Yan Mulkin Mallaka s**a shata musu ba, inde kuwa basu tsallaka wannan iyaka ba, to tsarin mulkin bazai amfani al'ummar ba.
Zabar Shugaba:
Wajen Zabar Shugaba da zai jagoranci wannan tsarin da 'Yan Mulkin Mallaka s**a yiwa sitamfi wanda bazai amfani Al'ummar kasar ba, suna tabbatarwa Shugaban Zaiyi biyayya ne ga Tsarin da aka bashi (Na mulkin mallaka) Kuma bazai ketare iyakar da aka shimfida ba.
domin tabbatar da biyayyar Dan takarar wannan kujera ta mulki to dole yaje can kasashen 'Yan Mulkin Mallaka domin amsa tambayoyin da Zasuyi masa, wanda daga nan zasu gane Zaiyi biyayya ko A'a.
Shiyasa Lokacin Zabe ko nadin sarauta zakuga ana rige rigen zuwa kasashen waje tarukan tattaunawa, To
idan Mai Neman Mulkin Zaiyi biyayya to sai a bashi damar takara, idan yaci mulki su saka shi cikin rabon arzikin da zasu deba daga kasarsa, Sannan su bashi kariya shi da iyalansa daga tuhumar cin hanci da rashawa, Sai yayi Komai ba komai, Anan duniya, idan bazai yi biyayya ba kuma to wajen zaben fidda gwanima dakyar ya wuce inka ya wuce to bazai wuce Babban Zabe ba, Inko duka 'Yan takarar sun yarda da sharadinsu to sai su zabi wanda Zaifi yin biyayya su bashi mulki.
inko bayan yahau kan mulki ya nemi bijirewa, to sun shirya yadda zasu kau da wanna mai mulkin, ta hanayar amfani da turakun tsarin mulkinsu da yake jagoranta.
Irin wadannan turakun Mulkin sun hada da Soja, Majalisa, da sauransu.
Tsaron Kasa:
Kasashe'Yan Mulkin Mallaka basa taba bari tsaron kasashen da suke mulka yabar hannunsu.
sune suke Bada training ga Askarawa na kasa, suke sayar mata da makamai, suke kula da cibiyoyin tsaron kasar da sunan masu bada shawara, suke Bada umarni wajen ayyukan tsaro na wanan kasa, dan haka duk yadda za'ayi Kasar tsaronta yana tafin hannunsu.
Idan sunso sai su samar da rashin tsaro domin biyan wasu bukatunsu kuma babu wanda ya isa ya samar da tsaron.
Duk sirrin Kasa yana hannunsu. dan haka dolen masu rike da mulkin kasar suyi musu biyayya sau da kafa.
Abin takaicin ma Duk training din da zasu bawa sojan wannan kasa to marar amfani zasu bashi, haka duk makamin da zasu bashi to shima marar amfani zasu bashi domin karma yayi tunanin kalubalantar su wata rana.
Tattalin Arziki:
Kasashe 'Yan mukin mallaka, Sune suke Tasarrufi da tattalin arziki na ƙasashen da suke mulka, sune suke da Bankin Bada Lamuni na Duniya Wato (IMF) sune suke da Bankin Duniya da yake tsarawa dukkan sauran Bankunan ƙasashe yadda Zasuyi aikinsu wato (World Bank), sune suke da cibiyar hada-hadar kudade ta duniya wato (World Trade Center) sune suke da Hanyar musayar kudi a tsakanin Bankunan duniya wato (SWIFT) sune suke da Kudin da dole idan zakayi cinikayya ta kasuwanci sai dashi wato(Dollar) Koda kasuwanci Kasa zatayi to Saide ta siyar ko ta sayo kaya ta amfani da kuɗin kasashe'Yan Mulkin Mallaka.
dade sauransu.
Shiyasa sai talaka ya rasa Meye Dalilin da yasa kudin kasarsa kullum yake rage daraja.
duk wadannan cibiyoyin kayan aikine na tabbatar da Mulkin Mallaka ga kasashen da ake yiwa mulkin mallaka.
Dolen kasa tayi biyayya ga dokoki da Muradun 'Yan Mulkin Mallaka, inkuma taki su saka mata takunkumi (su hanata cinikayya a duniya)
Sanna Har yau dinnan Kasashen da Ba'ayi masu mulkin mallaka to basu da yawa ko Goma dakyar su kai.
Nan Munyi takaitaccen Bayani ne akan abubuwa da s**a shafi kasa kai tsaye , wanda su masu mulki sun san dasu, kuma sunayin biyayya ga Iyayen Gidansu 'yan Mulkin Mallaka, to amma Meyasa Koda talakawa sun gane anayin mukin kasar sune ba domin su talakawa su sami saukin Rayuwa ba, kuma basu da wata dama tacewa ayi ko a'a a al'amuran Tafiyar da kasarsu , Amma duk da hakan talakawa basa iyayin komai ?
Ko Meyasa kaso mafi yawa na al'ummu sunsan mulkin mallaka ake musu amma basa iya yunkurin kawo Gyara ?
Insha Allahu zamu amsa wadannan tambayoyi a cikin Rubutun mu na gaba , da Zaiyi magana akan yadda 'Yan Mulkin Mallaka suke sarrafa Al'ummar Gari Domin su hanasu kokarin kawo sauyi.
~Ibn Abubakar Alhausawy
26/02/2024
Sojan Sama na Amurka Aaron Bushnell Kirista ÆŠan Shekaru 24 Ya cillawa kansa wuta a gaban ofishin Jakadanci na Isra'ila a birnin Washington DC na Amurka.
Sojan yayi Hakane a yunkurin sa na farkar da Duniya irin girman Zalunci da Amurka da Isra'ila suke aikatawa akan Al'ummar FalsÉ—inawa a Gaza da yamma da kogin Jodan.
Kafin Ya kunna wutar a Jikinsa Saida yayi bayani inda yake cewa
"Ni Bazan kasance mai taimakawa Kisan Kiyashin da Akewa FalsÉ—inawa ba, dan haka zanyi Wani abu mai tsananin hatsari domin Farkar da duniya dan haka dole Falastinwa su sami 'yanci. "
Bayan ya cillawa kansa wuta a Gaban Ofishin Jakadanci na Isra'ila, yaci Gaba Da maimaita kalmar Free Palestine har Saida wutar taci karfinsa 😠yazama muryarsa bata fita anajin me yake faɗa, amma yana tsaye yana daga hannu yana kara tabbatar da matsayarsa har Saida ya fadi kasa.
Duk Wannan abun yayi shine yayin da wayarsada ya ajiye ta akan ma'ajiyin waya take daukar video na abinda yake faruwa.
Hoton da yake Kasa Hoton Aaron Bushnell ne.
Menene ra'ayin ku akan irin wannan yunkuri na Aaron domin Farkar da Duniya Halin da Al'ummar FalasÉ—inawa suke ciki ?
26/02/2024
WASU MALAMAN DA KARYA KADAI SUKE GA ZASU RIKE MABIYANSU.
To idan ba da karya kadai sukega zasu iya rike mabiyansu ba Ya abinda ya faru kowa ya shaida , harma kukayi walima da farin ciki da faruwar sa, kukayi nade-naden sunaye ga waÉ—an da s**a aikata shi, kukayi ta isgili da yaÉ—a hotunan faruwarsa sannan ku dawo kuce wai bai faru ba ?
Kune fa kuka ce Buhari da Elrufa'i da Buratai da Sukayi wannan kisan kiyashin Aikin Allah suke , harma kuka raÉ—awa Burtai suna (Ayatullahi Burtai) sannan kuke Tsokala da sunan sa kuna cewa waÉ—an da kuka tabbatar ya aikatawa ta'addanci Ga Buratai nan , domin ku muzanta musu Har kun manta ?
Kune fa kukace Lefin Zagin Sahabbai yasa akayi kisan kiyashin Zariya, kuma wadan da s**a aikata ta'addancin sunyi dai-dai, kuma har kukayi walima da bukukuwa, harda waÉ—an da s**ayi sallar Godewa Allah da kisan da Gwamnatin Buhari tayi, sannan kukace ko Buhari baiyi maku komai ba , tunda ya (K*ashe 'Yan Shi'a) To ya gama yi maku komai , Har kun manta Kenan?
Kune fa Kuke yawo da hotunan Malam Zakzaky An dauko shi a Wilbaro jikinsa duk jini, idonsa yana zubar jini, kuna yaÉ—a hoton kuna Cewa (Wali mai Baro) har kun manta ne ?
Kune fa kuka dauko hoton sa da likitoci s**a dauka bayan Sunje duba Lafiyarsa , wanda a cikin hoton kowa yana iya kallon Idon Malam Zakzaky guda daya a mace baya aiki, kuka dinga yaÉ—a hoton kuna cewa Yazama mai Ido daya kuna kiransa da (Dujal mai ido É—aya) saboda isgili da shakiyanci irin naku , Yanzu duk wannan abinda kukayi kun manta kenan ?
Kune fa Kuke cewa Kunyi ajalin Shia'a ba ita ba kayanta, domin duk Gomnonin Shia'a na Kaduna , Kano , Da Yobe Buhari ya K*ashe su , kuna murna kuna fada , dan haka Shia'a tazo karshe Yanzu kuma kuzo kuce ba'ayi kisan ba ? Anya har kuna da saurin mantuwa haka?
Kune fa kukace kar abar Zakzaky ya fita neman lafiya, idan aka barshi ya fita Guduwa Zaiyi bazai dawo ba, saboda tsoro, shin har kun manta?
To abin mamakin duk da tabbatarwa da kukayi , harda murna da kukayi , da isgilanci da kukayi da goyon baya da kuka nuna ta duk hanayar da kuke iyawa , Saboda kunga Allah ya kunyata ku Allah ya bashi Lafiya ba domin kunso ba, Yanzu saiku dawo kuna ƙaryata kanku da sabbin karyayyaki saboda ku katange miskinan almajiranku daga fahimtar Ikon Allah da yake kunshe a cikin tseratar da bawansa Malam Zakzaky dakuma Warkar dashi.
A cikin wannan rubutun Na makala hotuna , domin bawa ÆŠan Rijiyar lemo amsa, dakuma miskinan almajiransa. Cewa Duniyafa Bazata manta ba Ta'addancin Buhari a Zaria, da rawar da kuka taka, yanzu ba Zamanin Shekaru 1400 da s**a wuce bane, da zaku aikata ta'addanci ko sauya tarihi domin boye Ta'addancin.
~Ibn Abubakar Alhausawy
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Abuja