HR Reporters
HR Reporters is an independent Hausa News media dedicated to rigorous journalism.
We provide objective local news, political analysis, business insights, and entertainment updates, with a core focus on crime reporting and investigative human-angle stories
09/08/2026
RUNDUNAR TSARO TA K**A WATA MATASHIYA KAN YUNKURIN SATAR JARIRI A KADUNA
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar cafke wata matashiya budurwa cikin tsakiyar dare, bayan an gano ta da shirin garkuwa da sace wani sabon jinjiri daga wani babban asibiti da ke jihar.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, wasu maza da ake zargi suna tare da matashiyar sun tsere da gudu nan take bayan da jami'an tsaro s**a gano lamarin.
Haka kuma, ana gudanar da bincike mai zurfi kan zargin cewa akwai yiwuwar hadin baki da daya daga cikin ma'aikatan asibitin domin gudanar da wannan danyen aiki cikin sauki.
A yayin binciken, jami'ai sun yi kokarin kiran lambobin wayoyin mutanen da s**a tsere, sai dai sun ki daga kiran kuma daga baya s**a kashe wayoyin baki daya don boye sawunsu.
Yayin da ake gudanar da binciken farko, wadda ake zargin ta ce ba ta san da nufin satar jaririn ba. Ta bayyana cewa mutanen da s**a tsere ne s**a umarce ta da ta dauko jaririn, da nufin za a kai shi wani wuri na musamman don ba shi taimako da sadaka.
Sai dai, sauran bayanan sun nuna cewa tana da cikakkiyar masaniya kan dukkan tsarin. Ita kuma ta ci gaba da jaddada cewa wadanda s**a gudu din sune ainihin jagororin tafiyar kuma su kadai s**a san gaskiyar lamarin.
Rundunar tsaro ta bayyana cewa an tsananta bincike domin gano inda sauran mutanen da s**a tsere suke, da kuma bankado babban dalilin da ya sa suke son sace jaririn.
Haka zalika, asibitin ya dauki matakan tsaro na ninka jami'ai domin tabbatar da lafiyar jarirai da iyayensu.
📷 HR Reporters
✓Follow, Share, And Subscribe =>
09/08/2026
DA DUMI-DUMINSU: Ya ƙera wayar sadarwa,tana iya yin kira ba tare da kati airtime ba.
A ƙasar Namibia, wani ɗalibin makarantar sakandare mai suna Simon Petrus ya ƙera samfurin wayar sadarwa ta amfani da tsofaffin wayoyi, talabijin, da sauran kayan lantarki da aka zubar.
Na’urar da ya ƙera tana iya yin kira ta hanyar tsarin rediyo ba tare da amfani da airtime ba. Haka kuma tana ɗauke da fitila, fanka, da wuraren cajar na’urori.
Simon ya ƙera wannan na’ura ne domin ta taimaka wa mutanen da ke yankunan karkara, inda siginar waya kan yi rauni ko kuma hanyoyin sadarwa kan kasance masu tsada.
Ƙirƙirarsa ta lashe matsayi na farko a wata gasar fasahar makarantu, sannan ta ja hankalin mutane a sassa daban-daban na duniya.
📷 HR Reporters
✓Follow, Share, And Subscribe =>
09/08/2026
Ina Kira Ga Masu Mata Ɗaya Su Ƙara Aure Domin Rage Yawan Zawarawa Da Ƴan Mata, Inji Sarki Sanusi II
Me Zaku Ce?
📷 HR Reporters
✓Follow, Share, And Subscribe =>
09/08/2026
DA DUMI-DUMI: Sojojin Operation FANSAN YAMMA Sun Ceto Fasinjoji 33 da ’Yan Ta’adda S**a Yi Garkuwa da Su a Zamfara
Sojojin Rundunar Sector 2, Joint Task Force North West, Operation FANSAN YAMMA sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda s**a yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026, bayan sojojin sun samu sahihin bayani cewa ’yan ta’adda sun tare tare da sace fasinjojin da ke tafiya a yankin Magazu na Tsafe.
09/08/2026
Daga ƙarshe dai ga yadda ta kasance da su a Libya
Allah ya ba ku ikon cin wannan jarabawar, gaskiya abun da wuya
09/08/2026
TOFA: "Ƙarya ne zargi ba ya kashe aure. In ji shaik Lawan Triumph.
Wannan magana babu ita a addini.
Babu abin da ke kashe aure sai saki.
Akwai sahabin da ya zo ya sami Manzon Allah S.A.W ya ce masa matata tana bin maza kuma ba shakka na tabbatar da hakan, sai Manzon Allah S.A.W Ya ce masa sake ta sai ya ce ina son ta, sai Manzon Allah S.A.W ya ce riƙe abar ka.
Shi ba ma zargi yake ba ya tabbatar.
Dan haka maganar zargi yana kashe aure ba nassi ba ne magana ce ta molanka da ake faɗa a ƙasar Hausa". In ji shaik Lawan Triumph.
Me Zaku Ce?
📷 HR Reporters
✓Follow, Share, And Subscribe =>
09/08/2026
Da dama a shafukan sada zumunta na tofa albarkacin bakinsu game da auren gata da gwamnatin Kano ta gudanar tun bayan bayyana shirinta na aurar da mutum 1,500 a jihar.
Mene ne ra’ayinku a kai?
📷 Reporter:
✓Follow, Share, And Subscribe =>
09/08/2026
HOTUNA: Yadda wasu daga cikin gwamnonin Arewa da wasu manyan baƙi da s**a haɗa da malamai da sarakuna, s**a halarci taron bikin auren gata na Jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar.
📷 Reporter: Usman Kano
✓Follow, Share, And Subscribe =>
Cikekken Bayani kan Yadda aka k**a su da zargin sce Jariri Asibitin Babura ta Jihar Jigawa
📷 Reporter:
✓Follow, Share, And Subscribe =>
08/08/2026
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta k**a wani Peter Sinamai, mai shekaru 30, mazaunin Sangere, ƙaramar hukumar Gombi, bisa zargin ka*she mahaifinsa na jini tare da jefa gaw@arsa cikin wata rijiya.
An k**a wanda ake zargin ne bayan jami’an rundunar sun samu rahoton faruwar lamarin. Binciken farko da ’yan sanda s**a gudanar ya nuna cewa ana zargin matashin da ka@she mahaifinsa sannan ya jefa ga@war cikin wata rijiya da ke yankin su
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, CP Kabiru Umar Hassan, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
An gano ga@war mamacin kuma an fitar da ita daga rijiyar, sannan aka kai ta dakin ajiye ga@warwaki domin gudanar da binciken ga@war (autopsy).
Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar wa manema labarai da k**a wanda ake zargin, inda ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
📷 Reporter: Aisha Usman
✓Follow, Share, And Subscribe =>
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Abuja