Muhammad Shehu
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muhammad Shehu, Digital creator, Abuja.
18/03/2026
Saudiyya Tace Bata Ga watan Sallah ba
Dan haka Sallah sai ranar juma'ah...🤗
03/03/2026
Bayan share watanni bakwai hannun yan bindiga, yau wannan bawan Allah yasamu futowa 🥹.
23/02/2026
Addu'ar buɗe baki🥤🥘🥙
`ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ`
Zahabaz-zama’u wabtallatil-‘urūqu wa thabatal-ajru in shā’ Allāh.
Ma’ana: `Ƙishirwa ta tafi, jijiyoyi sun ji ruwa, kuma lada ya tabbata in sha Allah.`
Mu yi addu'a, mu faɗawa Allah damuwar mu kafin mu sha ruwa sannan mu yawaita istigfari.
Allah ta'aala ya karɓi Azumin mu.
——Ahky Ameer
18/02/2026
BARKA DA SHAN RUWA
Ramadan dama ce... Ba ka da tabbacin sake riskar sa, ka yi iya bakin ƙoƙarinka wajen ganin ka rabauta a cikin wannan watan.
Ku ciyar daga abin da Allah ya h**e muku, ku karanta Alqur'ani, ku yi nafiloli
Allah ya karɓi ibadunmu. Amin.
17/02/2026
Assalamu alaikum yan uwa, alhamdulillah, mun ga jinjirin watan Ramadan.
Yanzu lokaci ne na ibada, rahama, gafara, da yawaita ayyukan alheri.
Abubuwan da ya kamata mu yi yanzu:
Yi niyyar azumi kowace rana saboda Allah
Yawaita zikiri da istigfari
Karanta Al-Qur’ani
Yin addu’a da neman gafara
🤲 Allah Ya sa mu cika wannan Ramadan da ibada mai albarka, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya karɓi azuminmu da ayyukanmu.
17/02/2026
Alhamdulillah Masha Allah anga wata azumi Ramadan Mai albarka a Nigeria
Daga fadar Mai girma shehun Borno
ℹ SIFFOFIN NAMIJI MAYAUDARI GUDA 10 DA YA KAMATA KI SANI DON KARE MUTUNCINKI.
👇
17/02/2026
BARI NA GAYA MA GASKIYA.
Duk Duniya Babu Wani Da Mutane S**a Rasashi s**a Daina Rayuwa da Nishaɗi(kaco kam), Karma ka Ruɗi kanka da yawan Ya'n Uwanka ko Abokai ko mutanen dake kewaye dakai✋Hm! Inde Mutane ne ina tabbatar ma Da Yawa cknsu Suna Tare dakai Ne Dan Wata Maslaharsu, dan haka Karkai mamaki dan sun Barka a ranar da s**a samu wanda ya Fika.
Wauta ce babba, ka riƙa ji a ranka cewar "Mutanen Da s**a fita sha'aninka ko S**a mantaka ckn Rayuwarsu, wataran a Ransu Suna tunaka kmr yadda kai kullum kk tunaninsu" 💔😅
Inhar zakaji shawarata ka Manta su Kawai kmr yadda s**a manta ka Ɗin nan.
Wani abu da baka sani ba...
Su Mutane Duk Yadda kakai a Iya Mu'amala wataran Zaka ga sun Tafi Sun Barka (kuma badan ka musu laifin komai ba💔😢)
Dan haka kar kaita Baƙin Cikin hakan, Wanda Ya Futa a Rayuwarka, Shima Wataran Wani Zai Fita a Rayuwarsa.
كما تدين تدان
(A Ƙarshe)
Karka Taɓa Tambayar Maƙaryaci me yasa yake ma Ƙarya, Dan tabbas Da wata Karyar zai baka Amsa.
Duk Wanda ka yarda dashi tun Karon Farko yaci Amanarka, karka sake yadda Dashi karo na Biyu, Ba Buƙatar Shanye Ruwan Teku duka Dan a Gane yana da Gishiri.
Ina Fatan ka Gane?
Toh ka Huta Lafiya...
Muyi sharing domin al'umma su amfana
Duk wanda yayi nuni akan aikin alkhairi kamar ya aikata ne.
Allah yabamu iko ameen 🤲🏼
12/02/2026
Ya sha kaye a zaɓe, sai ya katse wutar lantarki ga dukkan ƙauyen yana cewa shi ne ya haɗa wutar da kuɗinsa. Saboda haka su je su roƙi wanda s**a zaɓa ya yi musu.
Haka kuma ya dakatar da tallafin karatu ga ɗalibai 60 a mazaɓarsa wanda shi ne yake ɗaukar nauyi da kuɗinsa, yana zargin iyayensu da rashin mara masa baya a zaɓe har ya rasa kujerar majalisa.
Sun ce idan s**a zaɓe shi zai ƙara arziki ne a kan kujera, sai s**a zaɓi wani da bai ƙara musu komai a rayuwarsu ba.
Haka abin yake a yanzu a Plateau North da Plateau Central..
Sai naji ana tacewa free Abdul jabbar kabara wai dagaske ne
🥺
Click here to claim your Sponsored Listing.